Koriya ta Arewa za ta ƙara kusantar China

Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya godewa takwaransa na China akan gudunmowar da ya bayar domin ganawarsa da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump da suka yi a ranar 12 ga watan Yuni a Singapore.

A yayinda Kim ya ziyarci China ya bayyana godiyar sa ƙarara ga shugaba Xi Jinping akan rawar da ya taka domin warware matsalolin nukiliyar kasar.

A sanadiyar haka ya bayyana ƙudurinsa na habbbakar da dangantakar kasarsa da China.

A ziyarar kwanaki biyu da ya kai ya bayyana cewar sun tattauna akan dangantakar kasashen biyu da kuma ganawar da ya yi da shugaba Trump a Singapore.

 Labarai masu alaka