Jam’iyyar Muqtada al-Sadr ta lashe zaben kasar Iraqi

Kungiyar dake karkashin shugaban Shiar kasar Iraqi Muqtada al-Sadr da suka jima suna sa-in-sa da Amurka da kuma kalubalantar manufofin Iran a Iraqin sun yi nasarar lashe zaben ‘yan majalisun da aka gudanar a kasar.

Duk da reshen Sadr ne suka lashe zaben ba zai iya zama firaministan kasar ba saboda rashin tsayawa takara da bai yi ba. Kungiyar hadakarsa ta Sairoon ta samu kujeru 54.

A yayinda Victory Alliance ta firaminista dake kan gado Haider al-Abadi ta zo ta uku da kujeru 42 bayan reshen Al-Fatih da tazo ta biyu da kujeru 47.

Reshen Al-Fatih na karkashin jagorancin Hadi al-Amiri wanda ya jagoranci haffsosin da suka kauda kungiyar ta’addar DEASH da haddin gwiwar Iran a kasar Iraqi.Labarai masu alaka