Trump ya kori Ministan Harkokin Wajen Amurka Tillerson

Shugaban Amurka Donald Trump ya kor, Ministan Harkokin Wajen Kasar Rex Tillerson inda ya maye gurbinsa da Daraktan Hukumar leken Asiri ta CIA Mike Pompeo.

A wata sanarwa da Fadar White House ta fitar ta ce, tun ranar Juma'ar da ta gabata tump ya bukaci Tillerson da ya sauka daga kan kujerarsa wanda hakan ya sanya shi katse ziyarar da ya ke kai wa a kasashen Afirka.

Pompeo zai maye gurbin Tillerson inda a CIA kuma Gina Hapsel mace ta farko za ta zama Shugabar Hukumar don maye gurbin Pompeo.

A makon da ya gabata ne dai Tillerson ya fara wata ziyarar aiki a kasashen Afirka.

Trump ya kori Ministan a lokacin da Amurka ke tsaka da tattaunawar sulhu da Koriya ta Arewa.Labarai masu alaka