"Zamu hana rabuwar ƙasar Siriya"

Shugabanin ƙasashen Turkiyya, Rasha da lran sun gudanar da taron ƙolin Siriya karo na uku a birnin Sochin Rasha inda suka amince akan tabbatar da zaman lafiya a Siriya.

853192

Sun kuma aminta akan bin hanyar siyasa domin hana wargazar ƙasar tare da ɗaukar matakan rage fitinun dake addabar Siriyan.

Haka kuma shugabanin ƙasashen uku sunyi yarjejeniyar ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da aka samu a wasu yankunan ƙasar da kuma baida taimako ga waɗanda ke cikin mawuyacin hali.

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya tabbatar da ɗaukar dukkan matakai akan kauda ƴan ta'adda PYD /PKK a yankunan, sabili da haka matakan siyasa ba zai shafi kungiyar ta'addancin ba. Haka kuma ya ƙara da cewa ƙasashen uku zasu yi aiki dangane da tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya domin aiyanar da zaman lafiya ta girmamawa da mutunta juna.Labarai masu alaka