Putin ya gana da Assad a birnin Sochi na Rasha

Shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Sochi da ke Rasha.

851557
Putin ya gana da Assad a birnin Sochi na Rasha

Shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Sochi da ke Rasha.

Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga fadar Kremlin ta ce, tattaunawar ta Putin da Assad ta mayar da hankali kan batun kyale amfani da karfin soji wajen kawo karshen rikicin Siriya inda ake da bukatar koma wa amfani da hanyoyi na siyasa da diplomasiyya.

Putin ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a fitar da dukkansassan siyasar Siriya da yadda za a tunkari lamarin.

Ya ce, sha'awar ya san matsayin Assad game da Taron Sulhun kasa. Sannan ya ce, Assad na da muhimmanci game da sulhu ta hanyar Siyasa da Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranta.

A nasa bangaren Assad ya ce, a shirye suke su bayar da goyon baya kan batun tattaunawa.

Assad ya ce, sun amince da Rasha kan ba za ta ba wa kasashen waje damar tsoma baki a lamarin tattaunawar ta Siriya ba.Labarai masu alaka