Shugaban Mayakan Mahadi ‘yan Shi’ar Iraki na ziyara a Saudiyya

Shugaban Mayakan Mahadi ‘yan Shi’a a kasar Iraki Muktada Al-Sadr na ziyara a Saudiyya sakamakon gayyatar da Yariman Kasar Mai Jiran Gado Muhammad Bin Salman ya yi masa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya SPA ya bayar da labarin cewa, Muhammad Bin Salman da Al-Sadr sun gana a birnin Jeddah inda suka tattauna kan batun alakar Saudiyya da Iraki.

Ba a bayar da wasu bayanai da yawa ba a labaran.

Wannan ne karo na farko bayan shekaru 11 da Al-Sadr ya ziyarci Saudiyya.

A ranar 25 ga watan Yuli Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya ziyarci ya tafi garin Tanja na Morokko don huta wa. A karkashin dokokin Saudiyya idan Sarki ya yi tafiya to Yarima Mai Jiran Gado ne zai rike kasar har sai ya dawo.

AALabarai masu alaka