Taron sulhu a Astana ya amince da kafa yankunan zaman lafiya a Siriya

Zaman sulhun warware rikicin kasar Siriya da aka gudanar a Astana babban birnin kasar Kazakistan karkashin jagorancin Turkiyya da Rasha ya amince da a kafa yankunan zaman lafiya da ba za a samu arangama a cikinsu ba.

726332

Kasashen Turkiyya, Rasha da Iran sun sanya hannu kan wannan batu.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar na cewa, za a kafa yankunan na zaman lafiya a daukacin jihohin Idlib da Lazkiye, sai kuma wasu yankuna daga jihohin Aleppo, Homs, Hama, Dera, Kuneytra da Gabashin Guta.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Siriya Steffan de Mistura ya bayyana cewa, ya ji dadin matakan da aka dauka a kasar Kazakistan.

Nan da wasu 'yan kwanaki kasashe 3 da suka jagoranci zaman za su fitar da taswirar yankunan na zaman lafiya da kuma bayyana lokacin da za su fara aiki.

An bayyana wadannan yankuna a matsayin wurare na wucin gadi don tabbatar da tsaro kuma karon farko za su fara aiki na watanni 6. Bayan kara amincewar kasashen da suka tsaya don tabbatar da kafa yankunan.Labarai masu alaka