Shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka CIA zai ziyarci Turkiyya

Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Amurka Mike Pompeo zai ziyarci kasar Turkiyya a ranar Alhamis din nan.

Shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka CIA zai ziyarci Turkiyya

Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Amurka Mike Pompeo zai ziyarci kasar Turkiyya a ranar Alhamis din nan. 

An bayyana cewa, shugaban na CIA zai ziyarci Turkiyya awanni bayan tattaunawar shugaban Kasar Turkiyyan Recep Tayyip Erdoğan da shugaban kasar Amurka Dolad Trump ta wayar tarho.

Wannan ce ziyara ta farko da Pompeo zai kai kasar waje tun bayan nada shi a kan mukamin nasa.

A yayin ziyarar tasa za a tattauna batutuwan 'yan ta'addar PKK da reshen kungiyar da ke Siriya da ake kira YPG/PYD.

A yayin ganawar Trump da Erdoğan an tabo batutuwan hadin kai don yaki da ta'addanci.

Nan da wani dan lokaci Erdoğan da Trump za su gana da juna.Labarai masu alaka