Abin mamaki Trump ya halarci taron addini

A safiyar da ya fara mulkin Amurka, Trump da mataimakinsa, Mike Pence sun halarci wani taro a babban cocin kasar ke Washigton.

Abin mamaki Trump ya halarci taron addini

A safiyar da ya fara mulkin Amurka Trump da mataimakinsa Mike Pence sun halarci wani taro a babban coci a birnin Washigton.

Wakilan addini 26 ne suka halarci taron, yayin Imam Macid ya wakilci musulunci daga cibiyar musulunci ta Adams Centre.

Daga nan kuma sai Trump da mataimakinsa suka tsallaka zuwa reshen Virgina na ofishin dillancin tsaron kasar wato CIA.

Anyi mamakin ziyarar tasa saboda maganar da ta yadu lokacin zabe kan cewa, akwai kiyayya tsakaninsa da CIA.

A maganar da yayi a ofishin, Trump ya yabi ma’aikatan wurin tare da cewa zai kasance mai maramusu baya a kowanne lokaci.

A wurin ne dai ya kara da cewa, ‘yan jarida mutane ne marasa mutunci, kuma bazai sassautawa kafofin watsa labarai ba.

Sannan a ranar farkon dai Trump ya gana da shuwagabannin kasashen waje ta wayar tarsho, inda ya gana da shugaban kasar Mexico, wanda Trump ya sha cewa zai gina katanga tsakanin kasarsa da Amurka.

Shuwagabanin sun bayyana cewa za su hadu dan tattaunawa akan al’amuran da za su taimakawa kasashen guda biyu.

Bayannan Trump ya gana da shugaban kasar Kanada, Justin Trudeau ta wayar tarho.

Shuwagabannin biyu sunce alakar kashen biyu na da matukar anfani, musamman ta fannin kasuwanci.Labarai masu alaka