Faransa na shirin nemo hanyar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Faransa na shirin nemo hanyar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

475831
Faransa na shirin nemo hanyar samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Ministan Harkokin Waje na Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Mayis za a fara zaman tattaunawa tsakanin Falasdin da Isra'ila a Paris babban birnin Faransa.

A tattaunawar da Ayrault ya yi da jaridar Liberation ya bayana cewa, kasashen Amirka, rasha, Tarayyar Turai da Majalisar Dinki,n Duniya da wakilan karin wasu kasashe sama da 20 za su halarci tattaunawar.

Ya ce, kawo zaman lafiya tsakanin dauloli 2 da suke zaune a Kudus shi ne mafita kawai.

Ministan harkokin Waje na Falasdin Riyadh Al-Maliki ya bayyana cewa, suna maraba da wannan mataki da Faransa ta dauka.Labarai masu alaka