Dolmade din hakarkarin rago daga dakin girkin Fadar Daular Usmaniyya

Dolmade din hakarkarin rago daga dakin girkin Fadar Daular Usmaniyya.

1417684
Dolmade din hakarkarin rago daga dakin girkin Fadar Daular Usmaniyya

Daga cikin dadadan abincin dakin abincin Daular Usmaniyya a wannan makon zamu gabatar muku da wani nau’in abincinda ake sarrafa a garin Mardin mai kara, hadin kai, kima da tarihi kwaran gaske. Bayan Miyar Lebeniye a wannan makon zamu gabatar muku da Kaburga Dolmade, zamu shirya wannan anu’in abincin tare da mata biyu ‘yan garin Mardin.

Domin sarrafa wannan abncin ga kayayyakin da ake bukata:

 • Giram 2.5 na hakarkarin rago

 • Giram 500 na naman tsokan naman rago

 • Cokali 3 na man shanu

 • Rabin kofin gyadar yin dolmade

 • Hakora 2 na tafarnuwa

 • Kofi uku na shinkafa

 • Cokali biyu na kayan yaji

 • Cokali 2 na barkono

 • Cokali 1 na gishiri

 • Hannu daya na yankakken ganyen dill

 • Hannu daya na yankakken ganyen faski

Mai dafa abinci kuma mai binciken al’adu Yunus Emre Akkor ne yake mana bayanin yadda ake sarrafa wannan abinci mai dadi. Kafin mu fara kallo barimu zaga garin Mardin mu kashe kwarkwatar idanuwanmu. A sha kallo lafiya.

 Labarai masu alaka