DEASH na yunkurin farfadowa a lokacin Corona

A cikin ‘yan makonnin da suga gabata an ga yadda kungiyar ta’addar DEASH ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a kasashen Iraki da Siriya

1413425
DEASH na yunkurin farfadowa a lokacin Corona

A cikin ‘yan makonnin da suga gabata an ga yadda kungiyar ta’addar DEASH ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a kasashen Iraki da Siriya.

A wannan maudu’in mun kasance tare da Dr. Murat Yeşiltaşmanazarcin harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA…

Baya ga Karin yawan hare-haren da kungiyar DEASH suka kara yi, za’a iya bayyana cewa kuma sun dauki sabbin tsaruka. Kungiyar ta na amfani da barkewar cutar coronavirus don tsara sabbin hare-hare, da kuma zuga mabiyanta tare da karfafa tunanin cewa ita ce mai fada aji da babu kamanta a yankunan da ake fama da rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya, Afirka da Asiya. Za’a iya bayyana wannan dabarun a matsayin dabarun yaƙin hamada. Shirin DEASH na farko shi ne ta sake karbe ikon yankunan gabashi da yammacin rafin Euphrates da haka take ganin zata sake dawo da tasirinta a yankin baki daya.

Sha'awar ƙungiyar 'yan ta'adda DEASH na aiwatar da dabarun da take ƙoƙarin aiwatarwa a lokacin cutar coronavirus na nuni da son yin amfani da damar annobar domin kara haifar da masifu a doron kasa. Tun bayan barkewar annobar Covid-19 da ta haifar da raguwar tsaron kasa, kungiyar DEASH ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a kasashen Afghanistan, yammacin Afirka, Afirka ta Tsakiya, Yankin Sahel, Misira da Yaman. An kuma ga yadda take mafani da gibin da annobar ta haifar wajen kai hare-hare a Iraki, Maldives da Philippines. Baya ga wadannan kasashen ta yi kuma kira da akai munanan hare-hare a yammacin duniya.

Zamu iya fahimtar cewa kungiyar ta’addar DEASH na mafani da damar bulluwar annobar corona domin sabonta tsarukanta da kuma kara kai hare-hare a doron kasa. A bisa haka an ga yadda masu alaka da kungiyar a kasashen Iraki da Siriya ke ci gaba da taka rawarsu har ma da kara yawan wadanda suke horarwa a cikin wadannan yankunan. Kungiyar ta’adar ta yi amfani da wannan damar cikin gaggawa kuma ta kara daukar sabbin tsarukan da zasu ci gaba da bata damar karfafa ikonta a wadannan yankunan. Bugu da kari, a yayinda dakatar da yarjejeniyar dake tsakanin Iraki da Faransa; janye jami’an Amurka daga yankin da kuma dakatar da horarwa a yankin ya ragonta yakar kungiyar DEASH da ake yi, kungiyar ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a Irakin. A dayan barayin kuma, kungiyar ta DEASH na sake kai hare-hare a yankunan rafin Europhates da mayakan YPG/SGD ke da iko dama a yankunan da basu da cikkeken tsaro a Iraki. DEASH dai na ci gaba da kara kaiminta ta kai hare-hare a yankunan masu yawa a Iraki mai mazauna Larabawa ‘yan sunni. Ire-iren hare-haren da DEASH ke kaiwa yankin cikin gaggawa na nuni da cewa tana samun gudunmowa daga bangarori, kuma hakan na tabbatar da cewa tana amfani da yankin da ta taba yiwa mulkin mallaka a kwanakin baya.

A watan Afirilun shekarar 2020 anga yada wasu tsarukan hare-haren kungiyar ta’addar DEASH har biyu masu taken (Girbin Mayaka). Daga ranar 2 zuwa 8 ga watan Afirilu shekarar 2020 an tabbatar da cewa sun kai hare-hare har sau 60. Kodayake mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren suna  yammancin Afirka ne kusan rabin hare-haren sun kaisu ne a kasar Iraki. A ranar 16 ga watan Afirilun shekarar 2020 da kuma a tsakanin ranakun 9-15 ga watan Afirilun shekarar 2020 an tabbatar da cewa DEASH ta kai hare-hare har sau 33 a Iraki a jumlace ta kaddamar da hare-hare 49 a doron kasa.

Mafi yawan wadannan hare-haren da ta kai a Iraki ta kai su ne a lokuttan da aka saka dokar hana fita waje domin dakile kwayar cutar corona. Hakan ya sanya Iraki rage yawan sojojinta dake sintiri domin dakile cutar da kuma sauya tsaruka da Amurka ta yi a yankin sun kasance damar da DEASH suka yi amfani dashi. Wadannan hare-haren na tabbatar da bayanan da hukumomin leken asirin kasar suka fitar dake bayyana cewa DEASH nada mayaka har gudu dubu 3000 a yankin. Matsalolin tsaro dake Siriya na kara baiwa kungiyar DEASH dama. An dai tabbatar da cewa mambobin ‘yan ta’adda su kusan 500 da sa ka tsare daga gidan yârin Siriya sun koma Iraki su ka ci gaba da ayyukan ta’addanci. Kafin ma bulluwar annobar corona kasancewar yadda hare-haren da DEASH ke kaiwa sun kai 20 a wata, lamarin da aka bayyana a matsyin baban kalubale.

Sai kuma gashi DEASH na ci gaba da kara yawan hare-haren da take kaiwa. Gabanin corona sun kasance suna kai hare-hare ta kashe jami’ai da kuma a ofisoshin jami’an tsaro, bayan kuma bulluwar corona, DEASH da kuma EYP sun kara yawan harin da su ke kaiwa ofisoshin ‘yan sanda, sansanin sojoji da makamantansu. Dangane ga bayanan da rundunar sojin Irakin ta fitar wadannan hare-haren na karawa sabon shugaban DEASH Abu Ibrahim al-Hashimi al-Quraishi karfi wanda aka nada bayan Amurka ta kashe magabacinsa a shekarar 2019.

A Siriya ma ana ganin yadda DEASH ke ci gaba da kai kwatankwacin hare-haren da take kaiwa a Iraki. Kungiyar DEASH wacce ta fi kai hari a Siriya, a yankin garin Sukhna sun kai wa sojojin farmaki a ranar 9 ga watan Afirilu. Duk da gudunmowar da Rasha ke baiwa sojojin Siriya ta sama Hukumar Kare Hakkokin Bil Adama ta bayyana cewa a ranar a yayinda aka kashe sojoji 32 ‘ya’yan kungiyar DEASH 26 ne aka hallaka. Sai dai kawo yanzu hadi da DEASH babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin. Kimanin shekara guda kenan dai kungiyar DEASH na kalubalantar sojoji, mayakan Shi’a da kungiyar SDG a kasar. DEASH dai na amfani da ababen hawa makare da bama-bamai, abubuwan fashewa da miyagun makamai wajen kai hare-harensu.

 

A karshe dai, kungiyar ta’addar DEASH ta na amfani da barkewar cutar coronavirus a matsayar damar kara kai hare-hare a doron kasa. A Iraki ne dai suka fi kai hare-hare sai kuma a kasar Siriya. Duk da da haka akwai bukatar a kara sanya ido a harkokinta a Iraki.

 

Wannan sharhin Dr. Murat Yeşiltaş ne manazarcin harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar dan Adam watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya…

 Labarai masu alaka