Libiya bayan taron kolin Berlin

Taron kolin da aka gudanar a makon da ya gabata a Berlin babban birnin Jamus ya dan dakatar da rikice-rikicen da Libiyan ke fama da shi a halin yanzu

Libiya bayan taron kolin Berlin

Taron kolin da aka gudanar a makon da ya gabata a Berlin babban birnin Jamus ya dan dakatar da rikice-rikicen da Libiyan ke fama da shi a halin yanzu. Sai dai taron bai haifar da mafitar siyasar da zata kawo karshen matsalar  ba baki daya. Domin samar da lumana mai dorewa a kasar ta Libiya akwai bukatar hukumomin kasa da kasa, kungiyoyin kasa da kasa da masu fada aji a yankunan; dama na kasa da kasa su kulla hadaka mai karfi akan lamarin. Taron kolin Berlin dai ya yi nasarar shawo kan wasu masu fada aji a doron kasa akan lamarin na Lbiya amma bai haifar da wata matsaya mai gwabi ba. Daga watan Afirilun shekarar 2019 dakarun da Janar Halifa Haftar ke goyawa baya sun ka fara daukar matakan soja domin kwace mülki a kasar daga hannu hukumar haddin gwiwar da Majalisar Dinkin Duniya ta samar a kasar. Janar Haftar dai ya kasance yana samun gudunmowa da goyon baya daga kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Misira, Saudiyya da Faransa. Kasancewar yadda Faransa ke goyawa mai yunkurin yin juyin mulki baya ya zama abin dubawa da idon basira. Saboda Faransa wacce daya daga cikin kasashen dindin din na Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ce kuma sai gashi tana goyon bayan laifukan yakin da dakarun Haftar ke ci gaba da aikatawa a Libiya; tana kuma goyon bayan habbakar da gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniyar ta jagoranci kafawa da kuma bayar da goyon baya domin habbakar da ita ta haramtacciyar hanya.

Akan wanan maudu’in mun kasance tare manazarci a fannonin tsaro Dr. Murat Yeşiltaş a Gidauniyyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA.

 

              Hadaddiyar Daular Larabawa da Misira sun kasance kasashen dake kan gaba wajen baiwa Janar Haftar gudunmowa da karfin gwiwa. Sanadiyar gudunmowar da Haddadiyar Daular Larabawa ta baiwa Haftar ne ta sama da kasa ya bashi damar iya karbe ikon wasu muhimman yankuna a kasar ta Libiya. Haka ita ma Misira ta bashi tallafi mai kwari inda ma har ta taimaka ta tura da wasu sojojinta. Hakan na nuni da Haddadiyar Daular Larabawa, Misira da Saudiyya suna goyon bayan mülkin kama karya na soja a kasar Libiya. Wannan dai ya kasance siyasar wasu kasashen Larabawa bayan juyin juhanin kasashen ta Larabawa.

Idan muka dubi bayanan da aka fitar masu sakin layi 55 bayan taron Berlin, zamu iya sharhin cewa za’a iya samun sulhu da lumana cikin sauki idan aka kalubalanci kasancewar sojojin Haftar a kasar da ma kasashen dake goya masa baya. Sai dai bayanan da aka fitar basu bayyana janar Haftar a matsayin wanda ke sabawa kasar ba; sai ma bayyana shi aka yi a matsayin wani mai fafutuka ko daya daga cikin masu fada aji a kasar. Haka kuma kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Misira masu goyawa Haftar baya na kokarin bayyana cewa dakarun Haftar su kasance sojojin dindin din kuma siyasarsa ta samu gurin zama a hukumar Tripoli. Bisa ga hakan ne suke neman cewa Haftar ya kasance wanda zai nada ministan albarkatun man fetur da shugaban babban bankin kasar ta Libiya. Haka kuma duk da bayananan da aka fitar bayan taron na kunshe da matakai akan hana shiga da miyagun makamai a kasar ta Libiya; wannan ba abu ne da Hadaddiyar Daular Larabawa zata mutunta ba. A cikin irin wannan yanayin samar da lumana ta hanyar siyasa a kasar zai yi wuya kwaran gaske.

Turkiyya wacce ke goyon bayan gwamnatin hadin gwiwa da MDD ta samar a Libiya, a taron na Berlin ta maida hankali akan yadda za’a samar da lumana a Libiya ta hanyar siyasa da diflomasiyya. Duk da dai Turkiyya ba ko wane bayanan da aka fitar bayan taron ya mata dadi ba; taron ya yi nuni da cewa bata kasance ita daya ba a wajen goyawa gwamnatin haddin gwiwa a kasar baya. Turkiyya ta kasance wacce ke duban yadda dakarun Haftar zasu karbe ikon kasar da basu bi haramtacciyar hanyar juyin mulki ba. Zamu iya tabbatar da hakan idan muka kalli yarjejeniya da Turkiyya da Libiya suka ratabawa hannu a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar 2019. Turkiyya dai ta kasance kasa mai muhinmanci ta fanni siyasa da ma a fannin soja da kasar Libiya. Ta kuma fahimci cewa hanyar soja ba zai taba kawo karshen matsalar kasar ba, shi ne dalilin da ya sanya ta yi kira da karfin murya domin abi hanyar diflomasiyya a taron na Berlin.

 

Taron kolin Berlin akan Libiya dai ya samar da lumana na dan wani lokaci da kuma tabbatar da irin tsarin matakin da za’a dauka anan gaba. Idan dai har Haftar da kasashen dake goya masa baya sun ka dage da cewa hanyar soja ce zata iya kawo karshen matsalar kasar , ko shakka babu rikicin kasr zai iya kara kamari. Hakan kuwa ka iya mayar da kasar kamar Siriya da kuma kara rikita matsalolin da suka yiwa yankin katutu. A sabili da haka ya kamata zaman Berlin ya kasance wani dama da za’a mutunta.

 

 

Wannan sharhin  Dr. Murat Yeşiltaş manazarcin harkokin tsaro a Gidauniyar Nazari akan Siyasa Tattalin Arziki da Hakayyar dan Adam watau SETA.         Labarai masu alaka