Yadda ake hada naman "Rokali Uludag Kebab" mai dadi da ya samo asali daga Turkiyya

A shirinmu na abinciccikan Daular Usmaniyya da muke kawo muku duk mako, a wannan satin za mu bayyana muku yadda ake hada balangu ko hadin nama mai suna Rokalı Uludağ Kebabını

Yadda ake hada naman "Rokali Uludag Kebab" mai dadi da ya samo asali daga Turkiyya

A shirinmu na abinciccikan Daular Usmaniyya da muke kawo muku duk mako, a wannan satin za mu bayyana muku yadda ake hada balangu ko hadin nama mai suna Rokalı Uludağ Kebabını wanda ya samo asali daga garin Bursa na Turkiyya, za kuma mu yi bayanin yadda ake hada shi a kauyen Cumalikizik da Hukumar UNESCO ta sanya a jerin sunaye wuraren tarihi.

Domin hada wannan abinci mai dadi ga kayayyakin da ake bukata:

 

Rabin kilo na nikakken nama

ganyen Roka dauri daya

Tumatur kwaya 3

Tafarnuwa hakora 3

Yogot kofi 1

Buredi mai kama da surar farce guda 1

Man shanu gram 400

Gishiri

Bakin barkono

Jan barkono

 

Mai dafa abinci kuma mai binciken al’adu Yunus Emre Akkor ne yake mana bayanin yadda ake sarrafa wannan abinci mai dadi. A sha kallo lafiya.


 


Tag: Nama , Balangu

Labarai masu alaka