Sharhi akan rikicin dake tsakanin Iran da Amurka

Rigima da rikicin dake tsakanin Amurka da lran sun karu bayan kashe Kasim Sulaiman da Amurka ta yi a Baghdad babban birnin Iraki

Sharhi akan rikicin dake tsakanin Iran da Amurka

Rigima da rikicin dake tsakanin Amurka da lran sun karu bayan kashe Kasim Sulaiman da Amurka ta yi a Baghdad babban birnin Iraki. Janar Sulaiman wanda shi ne kwamandan sojojin kare juyin juhanin lran a Qudus ya kasance kashin gwiwar sallon siyasar kasar Iran a yankin a cikin ‘yan kwanakin  nan. Bugu da kari Janar Sulaiman daya ne daga cikin muhimman sunayen da suke jagarontar matakan sojan lran a yankunan tun daga lokacin da kasashen Larabawa suka kasance cikin halin juyin juhani. Bayan ga kasancewar Sulaiman wanda ya taka rawar gani a kassshen Lebanon, Siriya, lraki da Yaman, ya kuma kasance fitillar ayyukan dakarun kungiyoyin Shi’a a yankin. Haka kuma Sulaiman sabili da yadda ya karfafa dakarun Shi’a tun daga Lebanon har izuwa Yaman da kuma habbaka siyasar kasar lran a yankin ya sanya shi kasancewa mutum mai kima da daraja a idanun shugaban addinin kasar lran Hamaney dama a gurin shugaban kasar lran Ruhani. Idan muka dubi ire-iren rawar da Sulaiman ya taka da nasarorin da ya samu zamu iya sharhin cewa kashe shi zai kasance abinda zai haifar da yanayin da zai kada zuciyar lran kwaran gaske.

 

Muna gabatar muku sharhin Daraktan Bincike akan Tsaro Dkt. Murat Yeşiltaş daga Cibiyar Nazarin Siyasa da Tattalin Arziki watau SETA.

 

Hakika kashe Janar Sulaiman da kuma ramuwar gayya mai zafi da Iran ta yi nan take zai haifar da tashin hankula a Gabas at Tsakiya a shekarar 2020.  Duk dai manazarta basu da tabbacin ko hakan zai iya haifar da yaki tsakanin Amurka da lran, suna nazari akan cewa tabbas hakan zai kara zurfafa tsohuwar rufaffiyar yaki dake tsakaninsu da kuma kara  tsamin kallon hadarin kajin da kasashen biyu ke yiwa juna. Tahran dai ta sha alwashin yin ramuwa akan kashe Sulaiman, wanda a cikin dan kankanen lokaci ta tabbatar da hakan. A manyan titunan Tahran babban birnin lran al’umman kasar da suka kasance cikin mawuyacin hali na tsawon lokaci na ci gaba da rera taken ayi ramuwar gayya akan abinda aka yiwa kasar. A babban birnin Iraki ma watau Baghdad anga irin wannan cika tutuna tare da goyon bayan a dauki fansar kashe Sulaiman da Muhandis. Har ma sabbin kafaffun manya da kananan kungiyoyi dauke da makamai sun yada hotuna da bidiyon dake nuna shan alwashin da suka yi na daukar fansa. Majalisar kasar lraki ma ta yanke hukuncin korar sojojin Amurka daga kasarta; hukuncin da ta nemi gwamnatin kasar ta tabbatar. Iraki wacce ta kasance cikin fadace-fadace da rigingimu na tsawon lokaci ya zama wajibi akanta ta fara neman hanyar da zata magance wacan nan matsalar da ta taso a kasarta. Al’umar kasar Irak dai ta fahimci cewa rigima da tashin hankali tsakanin Iran-Amurka ba zasu kasance komai a gareta ba face kara nakasar da kasarta. Amma ba zata iya yin komai ba akan lamarin, domin kasar Iraki ba ta da gwabin da za ta iya kasancewa mai ‘yancin kanta da har za ta dauki matakin dakatar da Amurka dama Iran daga yi mata katsalandan a cikin kasa.

Domin yanke hukunci akan irin martanin da Iran zata mayarwa da Amurka ne ta gudanar da taron manyan jami’an tsaron kasar. A taron da shugaban addinin kasar Hamaney ya samu halarta; anka yanke hukuncin rataye jajayen tutoci a saman Masallatan kasar wadanda alamun yaki ne a akidar Shi’a. Hukumar Tahran dai ta jaddada cewa ba za ta cika alkawuran kasa da kasa ba game da shirin nukiliyar Iran sannan kuma za ta ci gaba da wadatar da sinadaran uranium, ta kuma kara da ikirarin mayar da babban martani ga Amurka. Daga karshe dai ta kaiwa Amurka hari a Iraki. Sai dai ba zamu iya bayyana cewa ko wannan martanin ya kasance martanin da ya yi dai-dai da kashe Janar Sulaiman ba. A wannan yanayin dai irin matakin da Amurkan kuma zata dauka shi ne abin dubawa mafi a’ala.

Kisan Janar Kasim Sulaiman dai ya tada zaune tsaye a Gabas ta Tsakiya. A halin yanzu dukkanin masu fada a ji a yankin suna nazarin yadda lamurka zasu kasance; kuma ko wannensu na shiri dangane da hasashensa.  Kawo yanzu dai Turkiyya ce kawai kasa tilo dake kira da a mayar da takubba kube. Isra’ila dai ta kasance cikin farin ciki kwaran gaske akan kashe Sulaiman. Ita kuwa Saudiyya tuni ta bayyana Sulaiman a matsayin mutum mai zubar da jini. Sabili da haka take ta farin ciki, sai dai kuma ta kasance cikin tsoro da fargaban cewa daga cikin martanonin da Iran zata mayar wasunsu zasu iya kasance akanta. Kananan kasashen yankin Gulf sun kasance cikin damuwa game da lamarin, hukumomin kasa da kasa kuwa sun zabi su yi shiru. Amsoshin da suke fitowa daga bakunan wasunsu kuwa ba su da kyau. Amurka kuwa duk da ta tsakano fadar tana kuma duba yadda zata kwantar da hunkula ta sake zaunawa da Iran. Ba a san dai ko yaki za ta barke ba, amma a shekarar 2020 Gabas Ta Tsakiya za ta kasance zafaffa.

Wannan sharhin Dkt. Murat Yeşiltaş ne Daraktan Bincike akan Tsaro a Cibiyar Nazarin Siyasa da Tattalin Arziki watau SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya.Labarai masu alaka