Yaki da Iran zai iya janyo rikici a kasashen Afirka

Kisan da Amurka ta yi wa kwamandan Dakarun Kudus na Iran Janar Kassim Sulaimani da Mataimakin Shugaban Hashdi Sha’abi Abu Mahdi Al-Muhandis a ranar 3 ga watan Janairui ya haifar da mayar da martani da suka daga 'yan Shi'a a fadin duniya.

Yaki da Iran zai iya janyo rikici a kasashen Afirka

Kisan da Amurka ta yi wa kwamandan Dakarun Kudus na Iran Janar Kassim Sulaimani da Mataimakin Shugaban Hashdi Sha’abi Abu Mahdi Al-Muhandis a ranar 3 ga watan Janairu a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Bagdad Babban Birnin Kasar Iraki ya haifar da mayar da martani da hayaniya a duniyar Shi’a da Iran ke da karfi a cikinta. Wannan yanayi ya janyo daga muryar adawa da Amurka a kasashen da Iran ta ke da jama’ar Shi’a dake goyon bayanta kamar su Iraki, Labanan, Yaman, Siriya da Najeriya. Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya (IMN) ta mabiya Shi’a sun mayar da martani ga Amurka bayan kisan Sulaimani. Jama’ar Shi’a na Najeriya sun gudanar da zanga-zangar adawa da Amurka a Abuja Babban Birnin Najeriya da kuma garin Zaria. Afirka ta Kudu kuma dake da kyakkayawar alakar diplomasiyya da Iran ta bayyana kisan Sulaimani a matsayin ta’addancin kasa da kasa inda ta ce tana goyon bayan Iran.

Mutuwar Kasim Sulaimani, na da ikon gwada kwanjin Iran a nahiyar Afirka. A wani kaulin za a iya cewar batun Kasim Sulaimani zai iya ba wa Iran damar dabbaka ikonta a kasashen Afirka. Baya ga Afirka ta Kudu ba wata kasa a Afirka da ta fito ta nuna goyon baya ga Iran. A lokacinda da Iran ta ce za ta yi ramuwar gayya, an dinga fadin akwai yiwuwar ganin wani motsi daga magoya bayan Iran dake kasashen da ba na Gabas ta Tsakiya ba. Hakan ya sanya rundunar tsaron Najeriya suka tsaurara matakai a ofisoshin jakadancin kasashen waje dake kasar. Iran na kokarin karfafa ikonta a Afirka ta hanyar amfani da ‘yan Shi’a da kuma ‘yan kasar Labanan dake biyayya ga Hizbullah. Hakan ya sa ake ganin Iran za iya amfani da su wajen kai hari kan cibiyoyin dake da alaka da Amurka a nahiyar ta Afirka.

Tasirin Iran a Afirka

A kokarin Iran na ganin ta kara karfi da samun iko a Afirka, ta dinga taimakawa ‘yan shi’a da kuma kulla alakar diplomasiyya ta bangaren ilimi, tattalin arziki da yada al’adu. Amma sakamakon rikicin Siriya, Yaman da kuma takunkuman Trump ya sanya Afirka ta zama mataki na 2 a manufofin Iran. Amma a makon da ya gabata bayan Amurka ta kashe Sulaimani ana ganin manufofin Iran a kasashen waje za su iya sauya akala. Ana tunanin Iran za ta iya tsayar da manufofinta a Gabas ta Tsakiya da Afirka. Idan Iran ta yanke hukuncin yin yaki da Amurka to ana ganin magoya bayan Iran dake wasu kasashe za su yi kokarin harar matsugunan Amurka a kasashensu. Baya ga Gabas ta Tsakiya, Afirka ce wajen da Iran za ta iya cin karenta babu babbaka.

Tun daga juyin juya halin Iran zuwa yau, Iran ta zuba jari da yawa a kan mabiya Shi’a dake Afirka. Duk da matsalolin da ta fuskanta a ‘yan shekarun nan amma ta ci gaba da bayar da taimako ga ‘yan shi’ar Afirka. Haka kuma da nufin samun tasiri a kan jama’ar Afirka, Iran ta ci gaba da gudanar da aiyukan ilimi da kula da lafiya. Idan har kamar yadda Iran ta fada za ta yi ramuwar gayya, to akwai yiwuwar magoya bayanta dake Afirka su ma su motsa. An san Iran da hada kai da wasu kungiyoyin da ba na Shi’a a Afirka. Amma kuma yana da muhimmanci a bayyana cewar ‘yan Shi’a na Afirka suna da alaka ta kai tsaye da Iran. Duk wani abu da ya shafi Iran yana shafar Afirka. A kafafan yada labaran da ake yada manufofin Iran ake rainon irin wadannan mutanen. Saboda yadda jama’ar Shi’a a Afirka suke marasa rinjaye ya sanya Iran ke amfani da Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya ta shi’a wajen yada manufofinta a kasashen Afirkan.

Tasirin Jama’ar Shi’a dake Najeriya

Ana hasashen cewar mambobin Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Najeriya sun kai kaso 5 na Musulmai kimanin miliyan 100 dake kasar wanda hakan ke nuna cewar sune mafi yawa a Afirka. Wannan jama’a da ta tasirantu da juyin juya halin Iran, na da manufar kafa kasa irin Iran a Najeriya. Wannan kungiya da ta kafa tsari makamancin na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanan, ba ta iya samun nasarar kafuwa sosai ba saboda matsin lamba da take fuskanta daga gwamnatin Najeriya. Saboda biyayya da suke wa Iran ya sanya suna gudanar da duk wasu bukukuwa da taruka da ake gudanarwa a Iran. Suna kuma bayar da goyon baya sosai ga siyasar Iran. Hakan ya sanya bayan kisan gilla ga Kasim Sulaimani magoya bayan Shi’a a Abuja Babban Birnin Najeriya da garin Zaria na jihar Kaduna suka yi wa Amurka zanga-zanga. Masu zanga-zangar da suka kona tutar Amurka, suka daga hotunan Sulaimani, sun dinga rera taken “Mutuwa ga Amurka”. Sun kuma sake jaddada neman a saki Shugabansu Ibrahim El-Zakzaky da aka kama tun shekarar 2015. haka zalika a shafukn sada zumunta na yanar gizo na kungiyar an aike da sakon ta’aziyya ga Iran tare da la’antar Amurka.

 

A wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan Najeriya ya fitar bayan da Iran ta sanar da za ta dauki fansar kisan Sulaimani, ya ce akwai yiwuwar a tayar da zaune tsaye a Najeriya. Sanarwar ta ce an gano akwai yunkurin za a kai hare-hare a Najeriya kuma sun dauki matakan kare afkuwar hakan. Kuma daga matakan da aka dauka har da na kare ofisoshin jakadancin kasashen waje. Wannan sanarwar da mahukuntan Najeriya suka fitar na nufin akwai yiwuwar magoya bayan Iran ‘yan Shi’a dake kasar za su iya kai hari kan hukumomin Amurka. Kungiyar Shi’a ta Najeriya ta sha gwabza fada da ake zubar da jini tare da jami’an tsaron kasar. A shekarar 2015 bayan da ‘yan Shi’a suka kai hari kan jerin gwanon motocin Shugaban Rundunar Sojin Kasa na Najeriya, an kashe mambobinsu 350 a wani martani da sojoji suka kai musu. Tun shekarar 2015 da ake gudanar da zanga-zangar neman a saki shugabansu El-Zakzaky ake samun zubar da jini a duk lokacinda suka yi zanga-zanga. Sakamakon yadda kungiyar ke barazana ga tsaron Najeriya ya sanya gwamnati haramta dukkan aiyukanta a kasar. Amma duk da haka kungiyar ta ci gaba da gudanar da aiyukanta. Majiyoyin BBC sun bayyana cewar kungiyar tana da wakilci a dukkan jihohin Najeriya 36. Ta bude makarantu sama da 360 ta hannun wata kungiyya mai suna Fudiyya. Sannan tana aiyukan asibiti da na kungiyoyin fararen hula. Haka zalika majiyoyin BBC sun ce kungiyar ta saka wasu mutanen da ta horar a rundunar ‘yan sanda da kuma hukumar leken asiri ta Najeriya.

 

Idan muka kalli batun ta wannan mahanga, za mu iya cewar za a iya amfani da wannan abu wajen tayar da zaune tsaye a Najeriya. Najeriya da take yaki da ‘yan ta’addar Boko Haram, zai mata wahala ta fuskanci ‘yan Shia da suka kai kimanin su miliyan 5 a kasar. Hakan ya sa ake ganin gara Najeriya ta dauki hanyar sulhuntawa da ‘yan Shi’a maimakon amfani da karfi wajen murkushe su. Sannan kuma ta shiga tattaunawa da Iran dake da iko a kan wannan kungiya ko kuma ta san hanyoyin da za ta raunata tare da rage karfin alakarsu da Iran wanda hakan zai sanya Iran din ta kasa amfani da su. Idan ba haka ba kuma to rikicin Iran da Amurka zai iya jefa Najeriya cikin matsala.

 

Rikici a Iran na iya janyo rikici a Najeriya. A saboda hakan duk wani abu da za a iya yi wa Iran da zai sanya magoya bayanta na Najeriya daukar mataki, zai fuskanci mayar da martani daga gwamnatin kasar. Sannan yana da muhimmanci a bayyana cewar mutumin da ya maye gurbin Kasim Sulaimani wato Isma’il Ghaani yana da alaka da ‘yan Shi’a na Najeriya. Jirgin ruwan da Amurka ta kama a Legas makare da makamai a shekarar 2010 mallakin abokin Ghaani ne. Hakan ya sanya a shekarar 2012 Amurka ta saka wa Ghaani takunkumi. Idan aka kalli wannan yanayi, za a iya cewa matukar Amurka ta yaki Iran to za a samu babban rikici a nahiyar Afirka.Labarai masu alaka