Yadda ake sarrafa 'menemen' masan kwai a Turkiyya

A al’adan abincin Turkiyya karin kumallo nada matukar tasiri kwaran gaske. Yana da wuyan gaske a yi karin kummalo ba tare da kek ko farantin kayan marmari a kusa ba

Yadda ake sarrafa 'menemen' masan kwai a Turkiyya

Barkanmu da wannan lokaci a cikin shirinmu mai suna Abincin Turkiyya da muke gabatar muku da yadda ake sarrafa wasu nau’ukan abincin Turkiyya daga nan shashen Hausa na gidan radiyon muryar Turkiyya.

A al’adan abincin Turkiyya karin kumallo nada matukar tasiri kwaran gaske. Yana da wuyan gaske a yi karin kummalo ba tare da kek ko farantin kayan marmari a kusa ba. A al’adan karin kummalo a Turkiyya a maimakon kofi ana amfani da shayi ne a cikin kananan kofunan tangaran. Shi kuwa kofi ana shan sa ne bayan an kammala karin kummalo. Kalmar Kahvaltı a Turkanci watau karin kumallo a Hausa na nufin “kalve altı” bi ma’ana kafin kofi. Watau abinda ake yi kafin asha kofi ko kafe. Shin ko wasu abubuwa ake hadawa da shayi yayin yin karin kumallo a Turkiyya? Daga cikinsu dai akwai cuku da zaitun. Hakika zaitun ya kasance abinda ke da tasiri kwaran gaske yayin gudanar da karin kumallo a kasar Turkiyya. Shi kuwa cuku watau cheese duk da akwai nau’o’insa da dama farin cuku shi ne wanda aka fi amfani dashi. Karin kumallo a Turkiyya dai abu ne da ake yi da kayayyaki da dama da suka hada da zaitun, cuku, man shanu, zuma, salami sausage, jam, kwai da ake sarrafawa ta hanyoyi da dama, kayan lambu, dolmade, tumatur, barkono da sauran wasu kayayyaki da dama.

A yau zamu bayyana muku yadda ake sarrafa wani nau’in abincin da ake karin kumallo dashi a kasar Turkiyya watau “menemen” wanda zamu iya kira masan kwai a harshen Hausa. Wannan nau’in omelette din dai ana yinsa ne da barkono, albasa da tumatur a wasu lokutta. Yanzu kuma sai kayayyakin da ake bukata domin sarrafa menemen.

Tumatur kwara 4

Albasa kwara daya

Danyen Barkono 4

Kwai kwara 3

Cokali biyu na man shanu

1/3 na cokalin gishiri

1/3 na cokalin garin barkono

Kafin mu fara bayyana yadda ake sarrafa Meneme yana da kyau mu sanar daku cewa menenen a kasar Turkiyya ya kasu kashi biyu, wanda ake yi da albasa da wanda ake yi ba albasa. A yayinda wasu ke bayyana cewar ya zama wajibi a yi manemen da albasa wasu kuma na ganin cewa hakan bai dace ba. Menemen da zamu bayyana muku a yau wanda ake yi da albasa ne; amma idan baku bukatar albasa kuna iya yin naku da barkono kawai.

A yanzu kuma sai yadda ake sarrafawa. Da farko dai za’a yayyanke albasa da tumatur kanana a kuma yayyanke danyen barkonon bayan an cire ‘ya’yan dake cikinsa.  Za’a soya albasan da mai na mintuna 4-5 daga bisani kuma sai a zuba barkono a ci gaba da soyawa a kuma zuba tumatur din da aka yayyanke a ciki a zuba sauran kayan hadin bayan tumatur din ya shanye ruwansa a kuma ci gaba da soyawa. A wannan lokacin za’a fasa kwayakwan a garwaye da gishiri da garin barkono a cikin wani kwano a zuba cikin hadin tumatur din dake cikin tukunya. A yayinda ake motsawa za’a soya na mintuna 3-4. Idan ana bukata za’a iya rabawa da zafi tare da biredi. A more lafiya.

A yau dai mun bayyana muku wani nau’in abincin da ake yi da kwai da ake ci a lokacin karin kumallo a kasar Turkiyya mai suna “menemen”. Ku dakace mu a makon gobe domin gabatar muku da wani nau’in abincin Turkiyya mai dadi. Ku huta lafiya.Labarai masu alaka