Rana Irin ta Yau 11.11.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a rana irin ta yau.

Rana Irin ta Yau 11.11.2019

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1821 aka haifi Fyodor Dostoyeski a kasar Rasha wanda ya shahara da littattafansa kamar su “Crime and Punishmet, “Buda” da kuma “Karamazov Brothers”.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1914 ta shelanta wa Kasashen Kawance yaki a Yakin Duniya Na Farko.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1918 aka yi yarjejeniya tsakanin Jamus da Kasasen Kawance inda da yin haka aka kawo karshen Yakin Duniya Na Farko.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1947 Turkiyya ta zama mamba a Asusun Lamuni Na Duniya.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1973 aka yi yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Masar inda da yin haka aka kawo karshen Yakin Yom Kippur.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2004 Shugaban Kasar Falasdinu na farko Yaser Arafat ya rasu a wani asibiti dake kasar Faransa. An yi sallar gawarsa a birnin Al-kahira inda aka bunne shi a birnin Ramallah. Mahmud Abbas ne ya maye gurbinsa a matsayin Shugaban Kasa.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2005 Marubucin Wasan Kwaikwayo Mustafa Akkad ya rasu a shekararsa ta 75 a birnin Amman. Akad ya shahara da fim din da ya rabuta game da Umar Mukhtar da kuma shahararren fim mai suna “the message”.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2016 Ciyaman din garin Derik dake birnin Mardin a Turkiyya Fatih Safiturk ya rasu sakamakon harin bam da ‘yan ta’addan PKK suka shirya.


Tag: Tarihi

Labarai masu alaka