Iyaye Mata na Diyarbakir: Hawayenmu Ya Kare

Iyaye mata sun kwashe watanni biyu suna zama a gaban ofishin HDP dake yankin Diyarbakir domin gudanar da zanga-zanga akan ‘ya’yansu da aka sace.

Iyaye Mata na Diyarbakir: Hawayenmu Ya Kare

Iyaye mata sun kwashe watanni biyu suna zama a gaban ofishin HDP dake yankin Diyarbakir domin gudanar da zanga-zanga akan ‘ya’yansu da aka sace.

Mahaifiya mai suna Hacire Akar wacce take ikirarin wadanda suka kama danta mai suna  Mehmet Akar zuwa saman wani tsauni dake garin Diyarbakır sun tahone da motar jam’iyyar HDP, ta fara zaman zanga-zanga a gaban ofishin jam’iyyar dake yankin tun a ranar 22 ga watan Agusta.

Mahaifiyar Akar wacce ta yanke hukuncin wannan zaman zanga-zangar domin kalubalantar matakin ‘yan ta’dda akan danta, ta yanke wanan hukuncin ne tun ranar da aka kama dan watau 22 ga watan Agusta. Mahaifiya Hacire wacce ta bayyana wannan bajintar ta ta, ta kasance abin koyi ga wasu uwayen da suka kasance cikin bakin ciki kamarta.

Adadin iyalan ya karu zuwa 55

Baya ga Fevziye Çetinkaya, Remziye Akkoyun da Ayşegül Biçer uwayen da suka yi koyi da matakan da uwayen Akar suka dauka a ranar 3 ga watan Satumba sun karu; a halin yanzu zaman zanga-zangar ya samu halrtar iyalai dake matsala irin tasu har 55.

Ana dai samun al’umma na kai wa uwayen dake zaune a gaban ofishin jam’iyyar HDP dake yankin domin nuna goyan baya ga zaman zanga-zangar kalubalantar kame ‘ya’yansu da mambobin jam’iyyar ke yi.

Baya ga ministan harkokin cikin gidan Turkiyya Süleyman Soylu, ministan iyali da kwadago Zehra Zümrüt Selçuk; wadanda ‘yan uwansu suka yi shahada, ‘yan siyasa, jaruman wasanni, yan jarida, sha’irai, wakilolin kungiyoyi masu zaman kansu da ‘yan kasar da dama sun bayyana kaiwa wadan nan uwaye ziyara domin nuna goyon baya akan matakin da suka dauka da kuma yi musu jaje.

Wayen da suke zaune a gaban ofishin jam’iyyar ta HDP bna dauke da hotunan yaransu da aka dauke, inda suka bayyana cewa suna masu matukar jin zafin batar ‘ya’yan nasu kuma suna masu matukar fatar sake kasancewa da ‘ya’yansu cikin kankanen lokaci.

"Sun cutar da rayuwarmu "

Wata mata mai suna Imamihan Nilifirka wacce aka dauke yaronta Mehmet shekaru hudu da suka gabata ta iso Diyarbakir daga Istanbul domin halartar wacan nan zanga-zangar zaman inda ta bayyana cewa yaronta take so sake haduwa dashi.

Nilifirka wacce ta zargi HDP da laifin kame mata yaro, ta kara da cewa “HDP ne suka dauke mini yarona, nasan da haka. Su kawo mini yaro na. Bamu samu labari daga gareshi ba, bai kuma ko kira ta wayar tarho ba. Danginmu na cikinbakin ciki, sun dauke muna yaronmu, sun cutar da rayuwarmu.  Hawayenmu ya kare. Me suke bida a gurin yaronmu?  Yaro ne ba zai iya ko cutar da tururuwa ba, yaro da ya kasance mai hazaka ne a makaranta.

Nilifırka, wacce ta yi zaman durumi har na watanni biyu domin nuna zanga-zangarta ta bayyana cewa ita da danginta suna jiran bayannan da HDP zasu fitar.

"Su fito su yi muna bayani. In dai su Kurdawa ne su fito su zauna tare damu. Bana bukatar Kurdawa irinsu. Nima Bakurda ce. Karsu yi siyasa da yarona. Sun kwace ‘yancin yarona da yaruwarsa. Kaman dai haka ne Nilifirka ta bayyana bakin halin da take ciki.

Nilifırka, ta bayyana cewa "Zata ci gaba da zaman zanga-zangar har zuwa karshe”

"Ba zamu bar nan ba har sai mun amshi ‘danmu "

Fatma Bingol mahaifiya mai yara biyar wacce aka sace danta mai suna Tuncay yana da shekaru 14 zuwa saman tsauni shekaru biyar da suka gabata ta bayyana cewar ta taho daga Istanbul ne domin halartar wacannan zanga-zangar da zummar sake haduwa da yaronta.

A yayinda Bingöl ke bayyana cewa shekaru biyar kenan rabonta da yaronta, ta kara da cewa “Su kawo mini yarona. Karsu tsaida uwayen yara anan,  Karsu sanya uwaye kuka irin haka, karsu wahalar da uwaye, karsu bakanta musu rai. Babu wanda keda hakkin cutar da wani. Dukkaninmu mun yi tsayin daka; babu inda zamu je sai an kawo muna ‘ya’yanmu . In suna iyawa su kashemu, bamu tsoron mutuwa”.

"Suga irin zaluncin da PKK ta yiwa Kurdawa "

Songül Altıntaş wanda ‘yan ta’adda suka dauke yaronsa mai suna Müslüm a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2015 a yayinda yake kan hanyarsa ta zuwa bautan kasa a garin Pülümür  dake karkashin gundumar Tunceli, ya bayyana cewa shekaru huhu kenann bai ji labarin yaronsa ba.

"Zamu kasance nan har kwanaki 60, zamu kuma kasance nan har na tsawon shekaru 60 ma. Ba zamu bar nan ba har sai yaranmu sun zo” Songül Altıntaş  ya bayyana haka tare da kira da uwaye mata da maza  da aka dauke yaransu zuwa tsaunuka da su fito kwansu da kwarkwatansu domin halartar wannan gagarumin zanga-zangar.

Altıntaş, ya kara jawabi kaman haka:

“Ya zama wajibi ga uwaye mata Kurdawa su farka daga barci. Su farka su ga irin zaluncin da PKK ke yiwa Kurdawa. Su lura da cewa basu da jin kai ga yara balantana ma ga uwaye mata da maza. Ya kamata uwaye mata Kurdawa su fahinci haka. Su kuma fahimci cewa bamu da wata makiya da ta wuce PKK.”

"Idan ba’a kawo min ‘ya ta ba: ba zamu fice daga nan ba”

Yasin Kaya wanda ya fito daga garin Ağri mutumin da aka dauke ‘yarsa mai suna Çiğdem tana da shekaru 17 shekaru hudu da suka gabata ya bayyana cewa ya halarci zanga-zangar ne domin jiran ‘yar tasa.

Kaya wanda ya yi kira ga uwaye mata da maza da su ci gaba da ayyanar da zanga-zangar jiran yaransu har lokacin da dusar kankara zata fara, ya kara da cewa,

"Muna jiran bayani daga garesu. Idan har ‘yata ba ta z oba, ba zan bar gurin nan ba. Su suna bayyana cewa su Kurdawa ne, amma ba Kurdawa bane. Mune asalin Kurdawa. ‘Yan HDP da suka dauke muna ‘ya’ya suwa tsaunuka, su fito; su z onan gaban mu. Su furta cewa “Allah ya tsinewa PKK, Ya waddansu, su kuma bayyana cewa “Bamu tare da PKK” Idan suka yi haka, mu kuma zamu bar nan gurin, domin idn basu hakan ba, toh suna tare dasu saboda haka alhakin dauke ‘ya’yanmu a wuyarsu zamu dora.Labarai masu alaka