Yadda ake sarrafa abıncin da ake kira “su böreği” watau börek din ruwa a Turkiyya

Ire-iren abincin da ake sarrafawa da garin fulawa a gidajen biredi suna da muhinmanci a nau’ukan abincin Turkiyya kwaran gaske, musanman nau’in abincin da ake kira börek a kasar Turkiyya

Yadda ake sarrafa abıncin da ake kira  “su böreği” watau börek din ruwa a Turkiyya

Barkanmu da wannan lokaci a cikin wani shirinmu mai suna Abincin Turkiyya da muke gabatar muku daga nan sashen Hausa na gidan radiyon muryar Turkiyya.

Ire-iren abincin da ake sarrafawa da garin fulawa a gidajen biredi suna da muhinmanci a nau’ukan abincin Turkiyya kwaran gaske, musanman nau’in abincin da ake kira börek a kasar Turkiyya. Wannan dai nau’in abinci ne da ake amfani dashi a lokacin bude baki’ abincin rana koma na dare a yankunan Gabas ta Tsakiya, Balkan, Aewacin Afirka dama a kasashen Asiya ta Tsakiya. Börek, ya kasance nau’in abincin da ya samo asali tun a loakcin daular Usmaniyya wanda ya kasance mai suna iri daya a dukkanin yankunan da muka ambata a sama. Börek dai bai kasance ba face nau’in abincin da ake hadawa da tunkuraz fulawa tare da wasu kayayyaki da dama. Kayayyakin da ake hadashi dasu sun kunshi tun daga nama zuwa cuku; fular barawo zuwa naman kaza; dankalin turawa zuwa alleyahu da ma sauran wadansu abubuwa da dama. Ana kuma dafashi a cikin tanda, saman murhu ko a soya cikin mai. A dalilin haka akwai nau’ukan abincin börek da dama a kasar Turkiyya. A yau zamu bayyana muku yadda ake sarrafa daya daga cikin nau’o’in wannan abincin mai suna olan “su böreği” watau börek din ruwa. Wadanda keda bukatar koyon yadda ake sarrafa wannan nau’in abincin zasu iya biyo mu sannu a hankali domin wannan nau’in abinci ne mai wuyar hadawa.

Domin sarrafa “Su böreği” ana bukatar wadannan kayayyaki;

Kofi biyar na garin fulawa

Kwai kwara hudu

Kofi 2/3 na ruwa

1/2 cokali na gishiri

Kofi 2/3 na soyayyen man shanu

Lita biyu na ruwa (domin tafasa tunkuzan)

1/2 cokali na borkono

Cokali daya na man shanu

Giram 400 na cuku (Cheese)

Cikwon rabin hannu na yankakkun faski

Yanzu kuma sai yadda ake sarrafawa.  Da farko dai za’a hada tunkuza da kofi biyar na gasrin fuklawa, kwai hudu, kofi biyu bisa uku na ruwa da rabin cokalin gishiri. Bayan haka sai a yayyanke tunkuzar zuwa kananan kwallaye 10. Bayan an rufe kwallayen tunkuzar da kyallesai a dakata har na kusan awa daya. A wannan lokacin za’a garwaye faski din da cuku. A wannan lokacin za’a dora tukunya mai fadi a saman murhu a zuba ruwa lita biyu. A cikin ruwan da ya fara tafasa za’a zuba man shanu cokali daya da rabin cokalin gishiri. Bayan an dan bude kwallayen tunkurar domin su dahu sosai sai a sanyasu cikin ruwa mai tafasa a dafa na mintuna 30-35. Bayan sun dahu sai a sanya su cikin ruwan sanyi. Bayan sun yi sanya za’a tsame a bari su tsane. A wannan lokaci za’a shafe tukunya da man shanu a kuma jera kwallayen tunkuzar a cikin tukunyar. Za’a kuma yayyafa man shanu a samansu. Haka kuma za’a yi duakkanin sauran kwallayen tunkuzar. Bayan an jera dukkanin kwallayen tunkuzar sai a sanya hadin cukun a cikin ko wane. A wanan lokaci za’a kara yayyafa man shanu a samansu a kuma yayyanke kanana kamar girman senti mita 5-6. A wanan lokaci sai a sany su cikin tandar da aka kunne ya y izafin daraja 190 a soya har sai sun yi ja. A wannan lokaci sai a raba börek din da zafinsu.

A wannan makon mun gabatar muku da yadda ake sarrafa “su böreği”  ku dakacemu a makon gobe domin gabatar muku da wani nau’in bincin Turkiyya mai dadi.

 Labarai masu alaka