Yadda ake sarrafa abincin “islim kebabi” a Turkiyya

A duk lokacin da aka ambaci abincin Turkiyya abinda ke farkon zuwa ga zukatan mutane shi ne “kebab”

Yadda ake sarrafa abincin “islim kebabi” a Turkiyya

Barkanmu da wannan lokaci a cikin wani shirinmu mai suna Abincin Turkiyya da muke gabatar muku daga nan sashen Hausa na gidan radiyon muryar Turkiyya.

A duk lokacin da aka ambaci abincin Turkiyya abinda ke farkon zuwa ga zukatan mutane shi ne “kebab” Amma kamar yadda muka bayyana a baya abincin Turkiyya bawai kebab bane kawai ya kunsa yana tattare da nau’ukan abincin da suka hada da kayan lambu, kayan marmare da kuma kayan yaji. Har am a lokacin da ake hada Kebab din ana yawan sarrafa shi tare da kayan lambu. A yau nau’in abincin da zamu bayyana muku yadda ake yinshi shi ne “islim kebabi” Wannan dai nau’in abinci ne da ya kasasnce mashhuri a garin Gaziantep din kasar Turkiyya. Wannan dai nau’in abinci ne da ake sarrafawa tare da gauta da nama. Ku biyo mu sannu a hankali domin bayyana muku yadda ake sarrafa wanan abincin.

 

Bari mu zayyana kayayyakin da ake bukata domin sarrfa “İslim kebabı”;

Gauta hudu

Kofi daya na mai

Jan tomatur hudu

Borkono kwara biyu

Giram 500 na nama

Kwara na albasa yankakku

Cokali hudu na garin fulawa

Tafarnuwa hakura biyu

Kwai kwara daya

Rabin cokalin gishiri

Rabin cokalin borkono

Rabin cokalin garin Cumin

Rabin cokalin bakar borkono

Domin hada ruwan miya:

Cokali biyu na mai

Tumatur biyu yankakku

Tafarnuwa kwara daya

Rabin kofin ruwan zafi

Cokali ¼ na gishiri

Rabin cokalin borkono

Yanzu kuma sai yadda ake sarrafawa. Da farko dai bayan an kankare gautan za’a tsattsagasu gida hudu. Domin fitar da dandanonsu za’a dakatar da gautan cikin ruwan gishiri nar abin awa. A wannan lokacin za’a zuba naman cikin wani kwano a kuma garwaye tare da yankakkun albasa, kwai, garin fulawa, tafarnuwa, rabin cokalin gishiri, rabin cokali borkono, rabin cokalin cumin sai a ci gaba da motsewa har sai ya yi kauri na kimanin mintuna 10-15. Za a fara diban hadin a tafin hannu ana mulmulewa kamar kwallo, za’a iya yin kamar guda takwas. Sai a zuba cokali biyu na mai a cikin tukunya a a soya ana yi ana motsawa a hankali. A wannan lokaci sai a cire gautan daga cikin ruwan gishiri a kuma zuba su cikin ruwa mai yawa a dan dakata. Daga bisani sai a busar dasu ta hanyar dorasu a samman wani kyalle. A wanan lokaci sai a zuba kofin mai biyu ko uku cikin tukunya a kuma soya gautan sosai. Za’a ci gaba da soyawa har sai gautan sun fara ja, daga bisani sai a tsame a kuma dorasu akan kyallen domin kada mai ya yi yawa a cikinsu. A wanan lokaci za’a raba koriyar borkonon gida hudu, jan tumatur gida biyu. Sai kuma a sanya soyayyun gautan a cikin tukunya jeri-jeri. A tsakiya sai a sanya kwallon nama. A samansa sai a sanya tumatur da koriyar borkonon a hadesu da kwallon naman ta amfani da abin kwalkwalan hakura. Dukkanin kwallayen naman da aka hada haka za’a yi muşu sai a sanya tukunyar a cikin tanda. A wannan lokaci sai a soya mai a cikin wani tukunyar da za’a hada romon miya. Sai a zuba yankakkun tumatur, tafarnuwa, daya bisa hudun cokalin gishiri, rabin cokalin borkono. Sai a dora akan murhu a soya na mintuna 4-5. Wannan romon miyar da aka hada za’a rinka diba ana zubawa saman gautan. Bayan hadin abincin da aka sai ya cikin tanda mai zafin daraja 180 ya dauki mintuna 30 sai a sauke a raba.

A wannan makon mun gabatar muku nau’in abinci mai suna “islim kebabı” Ku dakacemu a makon gobe domin gabatr muku wani nau’in abincin Turkiyya mai dadi. Ku huta lafiya.Labarai masu alaka