Yadda ake sarrafa "mercimekli köfte" watau danbun lantil a Turkiyya

Barkanmu da sake saduwa damu a cikin shirinmu mai suna Abincin Turkiyya

Yadda ake sarrafa "mercimekli köfte" watau danbun lantil a Turkiyya

Barkanmu da sake saduwa damu a cikin shirinmu mai suna Abincin Turkiyya.  A yau zamu bayyana muku yadda ake sarrafa wani nau'in abincin da ake yi da jan lentil. Wannnan nau'in abincin da ake kira da suna "mercimekli köfte" watau danbun lantil ya kasance abinci mai amfani da daɗi sosai ga waɗanda basa cin nama.  Lantil dai ya kasance hatsin da ake yawan amfani dashi wajen sarrafa nau'ukan abinci da dama a ƙasar Turkiyya. Ana amfani dashi domin yin miya, dambu dama wasu sauran nau'o'in abinci.  A yau abincin lantil ɗin da zamu bayyana muku ya kasance nau'in abincin da ake ci a matsayin ainihin abinci ko kuma na gyara baki a lokutan da ake shan shayi.

 

Domin sarrafa Mercimekli köfte barı mu zayyana ire-iren kayayyakin da ake buƙata;

 • Kofi ɗaya na jan lentil
 • Kofi biyu na ruguzazzun alkama
 • Albasa ƙwara biyu da za'a yayyanke ƙanana
 • Rabin kofin man zaitun
 • Cokali uku na niƙekken tumatur
 • Rabin kofin ruwan zafi
 • Jinƙa ɗaya na faski
 • Zanganya uku na shuɗiyar Albasa
 • Lita ɗaya na ruwa
 • Cokali ɗaya na gishiri
 • Cokali ɗaya na cumin
 • Cokali daya na borkono
 • Ganyen letas goma

Yanzu kuma sai yadda ake sarrafa mercimekli köfte. Za'a fara dafa kofi ɗayan lentil ɗin da ruwa lita ɗaya bayan an wanke sosai. Za'a dai ci gaba da dafawa har sai yayi laushi. Bayan lentil ɗin ya dafu sai a zuba kofi biyu na ruguzazzun alkaman a rufe tukunyar a ci gaba da dafawa har na mintuna 35 zuwa 40

A lokacin da lentil da alkaman suke laushi sosai sa a kuma fara shirye sauran kayayyakin da za'a haɗa abincin dashi.

Da farko dai za'a zuba yankakkun albasan cikin tukunya a soya da man zaitun har sai ya yi laushi. Daga bisani kuma sai a zuba cokali uku na niƙekken tumatur, a kuma zuba  cokali borkono. Bayan an zuba rabin kofin ruwan zafi sai a bari ya tafasa har sau ɗaya ko biyu. A wannan lokaci za'a motse hadin lentil din sosai har sai ya yi kauri a kuma rufe tukunyar. A wannan lokaci kuma sai a yayyanke faski da shuɗiyar zanganyar albasan ƙanana-ƙanana. A halin haka za'a  zuba cokali ɗaya na cumin da cokali ɗaya na gishiri cikin haɗin a motse sosai har sai ya yi kauri. Sai kuma a zuba dukkanin sauran kayan haɗin a ciki a ci gaba da motsewa. A wannan lokacin sai a rinƙa ɗiban hadin daidai cikon tafin hannu ana matsewa a cikin tafin hannun a rinƙa jerawa akan farantin da aka shinfiɗa ganyen letas a samansa. A more lafiya.

A cikin wannan shirin namu mai suna Abincin Turkiyya a yau mun gabatar muku yadda ake sarrafa “mercimekli köfte” ku dakacemu a makon gobe domin gabatar muku da wani nau'in abincin Turkiyya mai daɗi. Ku huta lafiya.Labarai masu alaka