Ko ya kamata a kalli maslaha akan Daular Usmaniyya?

Akwai waɗansu maslaha da ƙa'ida da gaskiya basu isa domin warware su. Kayayyakin gadon da daular Usmaniyya ta bari na ɗaya daga cikin ire-iren wadannan maslahohi.

1267077
Ko ya kamata a kalli maslaha akan Daular Usmaniyya?

Akwai waɗansu maslaha da ƙa'ida da gaskiya basu isa domin warware su. Kayayyakin gadon da daular Usmaniyya ta bari na ɗaya daga cikin ire-iren wadannan maslahohi. A halin yanzu yadda ma ya kamata mu yi sharhi akan daular Usmaniyya ya zama abin muhawara. A ƴan kwanakin nan, a bukin cikar Lebanon shekaru ɗari da samun ƴanci shugaban kasar Michel Aoun ya zargi daular Usmaniyya da kafa ta'addanci inda kuma ya bayyana cewar ƙasarsa ta samu ƴanci ne da goyon bayan ƙasar Faransa. Ana dai samu da ganin irin wannan zargin a cikin littafan ƙasashen yamma dana ƙasashen Laraba lokaci-lokaci.

 

Daga sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Turkiyya ce muke gabatar muku da sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar ilmul siyasa dake jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt…

 

Ko shakka babu hukumar data kwashe shekaru 600 tana gudanarwa za'a iya samun wasu lamurrukanta da za'a iya yin suka akansu. Amman zargin daular Usmaniyya da ayyanar da ayyukan jari hujja tare da taushe al'adun wasu tamkar yadda wasu ƙasashen ke aiyanarwa, wannan lamari ne da za'a ƙalubalanta da kakkausar murya. A Turkiyya a yau, akwai masu sukar daular Usmaniyya da rashin ƙaddamar da tsarin mamayar ƙasa, inda suke iƙirarin cewa a lokacin da Daular Usmaniyya ta samu dama da ta zartar da irin wannan tsarin da yanzu an samu ɗinbin Turkawa da Musulmai a ƙasashen da suka kasance ƙarƙashinta. Da kuma Faransa da lngila basu samu damar ikirarin  da suke yi ba akan mafi yawancin ƙasashen da suka mulka. Amma daular Usmaniyya bata aiyanar da irin mulkin kama karya da jari hujja ba, tsarinta ya banbanta dana ƙasashe masu ra'ayin hakan.

 

Pax Ottomana

A yau dai ƙasashen da suka kasance ƙarƙashin daular Usmaniyya sun kasance tamkar kogunan jini. Ƙasashen Balkan, gabas ta tsakiya da Afirka da suke cikin mawuyacin hali yanzu, a lokacin daular Usmaniyya sun kasance cikin lumana inda suke zaune lamun lafiya tare da amfani da harsunansu, addinansu da al'adunsu. Haka kuma suka barsu bayan ficewar daular Usmaniyya daga ƙasashen. Za'a iya ganin haka a littafin tsarin daular Usmaniyya mai suna Pax Ottomana (Lumanar Daular Usmaniyya) dake tattare da jin ƙai da zaman takewa. Za'a iya yabon irin matakan jin kan da daular Usmaniyya ta dauka a lokacin da ta gano Amurka, yadda bata dauki ko wani irin matakin kauda addini ko harshen al'umman yankin ba; da kuma yadda duk da ta kwashe shekaru 150 yankin lndiyawar lngila ta bar al'umman yankin na ci gaba da magana da harshen lngilishi.

Da ire-iren waɗannan ikirarin da ake yi da zargi marasa kan gadon da ake yiwa daular Usmaniyya wai ta aiyanar da mulkin jari hujja gaskiya ne; da a halin yanzu shugaban ƙasar Lebanon Michel Aoun bai kasance Kirista ba. Zamu iya baiwa shugaban ƙasar Lebanon amsa da wasu kalaman da wani ɗan uwansa dan ƙasarsa Kirista mai suna Amin Maalouf ya rubuta inda ya kamanta tare da banbance zunzurutun tsarin mulkin daular Usmaniyya dana ƙasashen jari hujja masu mulkin mallaka: Acewarsa

 

“Babu wani addinin da babu taƙawa da hakuri a cikinsa. Amma idan har za'a yi sharhi akan kishiyoyin nan biyu. Musulunci babu abin asha tare dashi. Yadda sojojin Musulmi suka gano ƙasashen kakaninmu suka kuma barsu da addininmu na kiristanci bani tunanin da sojojin Kirista ne suka gano ƙasashen musulmi suka kuma zauna dasu har na tsawon karni huɗu da basu bar al'umman da musulunci ba. Mu dubi abinda ya faru ga Musulmi a Spain ko ma Musulmin Silciya an kau dasu daga doron ƙasa baki daya, basu bar ko mutum daya ba, ko dai an hallakardasu ko kuma an tilasta su canja addinisu zuwa kirista."

A ƴan kwanakin nan ferfesan tarihi a lsra'ila Yuval Noah Harari ya yaɗa wata ƙasida a jaridar Hürriyet inda ya yi sharhi akan tsarin Pax Ottomana dake koyar da hakuri da jin ƙai:

“A zamanin tsakiya babu jin ƙai da hakuri a nahiyar Turai …..a ƙarni na 1600 a Parisa kowa darikar katolika yake bi, idan ma wani ɗan ɗarikar protestan ya shigo birnin kashe shi ake yi. A Landan kuwa kowa darikar Protestan yake yi, idan wani dan darikar katolika ya shigo birnin kashe shi ake yi, a wannan lokacin aka cimma Yahudawa zarafi, ba'a kuma ko son jin kalmar lslama. Amma a dai dai wannan lokacin ne Musulmi, Kirista, yahudawa, Armeniyawa, Bulgeriyawa, Ortodoxs da Romawa ke zaune a lstanbul lamun lafiya"

 

Amfani da tarihi ta hanyar ci gaba da tarwatsa yankin daular usmaniyya.

 

Zamu iya bayar da amsa akan yadda ake ci gaba da zargin osmaniyya. Amma ba zamu so mu tsaya akan haka ba. Zamu tsaya ne akan yadda wasu ƙasashe ke amfani da ra'ayin jari hujja da gudanar da mulkin kama karya. Da kuma ko za'a iya yarda da yadda ake ƙoƙarin kamanta musulunci wanda ya kasance mai yunkurin kare wadancan miyagun dabiu da samar da zaman lafiya da aikata ire iren abubuwan ƙin da muka ambata a baya. Bayan rushewar daular Usmaniyya munga yadda ƙasashen Balkan, gabas tsakiya da Afirka suka ci gaba da tarwatsewa . Har ila yau ana amfani da addini, kabilanci da makamantansu wajen ci gaba da tarwatsa waɗannan yankunan. Ana dai amfani da yadda a tarihance lamari jari hujja ya kasance wajen ci gaba da mulkin mallakar wadannan yankunan, ko wannan bakar dabiar abu ne da za'a iya tunanin bari?

 

Me yakama ayı acikin wannan halin?

A wannan halin dai bai kamata a tsaya akan abubuwan da daular Usmaniyya ta yi ko ta bari kawai ba. Ya kamatane ayi sharhi akan yadda aka kasance a ciki a halin yanzu da kuma yadda gobe zata kasance. Za'a iya daukar darasi akan illar da koyi daga ƙasashen yamma suka haifar a lokacin daular Usmaniyya da kuma lokacin kafa jamhoriyar Turkiyya. Haka kuma da yadda ƙasashen da suka kasance ƙarƙashin daular Usmaniyya suna ci gaba da fuskantar irin wannan kalubalen. 

Kawo yanzu dai ƙasashen Balkan, Afirka da gabas ta tsakiya na ci gaba da fuskantar kalubalen tarwatsewa . Da kuma yadda ake ci gaba da amfani da tarihinsu da al'adunsu. A sabili da haka sabani ra'ayin da bukatun masu mulkin jari hujja ya kamata mu fara sharhi akan yadda za'a samar da zaman lafiya da kuma ci gaban wadannan yankunan.

Ya dai kamata dukkanin masana, malamai da makamantansu su tashi tsaye tsayin daka domin ƙalubalantar ire iren wadannan yunkurin jari hujja da mulkin kama karya.

Ire- iren wadannan matakan ya kamata a dauke su ta hanyar duban lamurkan da ake aiyanarwa a cikin kasashen dama daga waje. A hakikanin gaskiya ya kamata a sabawa wadannan ƙasashe da yankunan mafita ne ta hanyar nazarin tarihinsu da al'adunsu da tunanin yadda ya kamata gobensu ta kasance, sabanin haka zasu kasance cikin matsaloli da dama da zai kara ƙerasu cikin halin ƙaƙanikayi daga karshe kuma su ci gaba da tarwatsewa.

 

Wannan sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban tsangayar ilimin siyasa a jami'ar  Ankara Yıldırım Beyazıt.Labarai masu alaka