Garin Harran mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Wani gari mai suna Harran nada shekaru kimanin dububiyar, inda ya kasance babban cibiyar al’adu tun karni na daya bayan haihuwar annabi Isa (AS).

Garin Harran mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Wani gari mai suna Harran nada shekaru kimanin dububiyar, inda ya kasance babban cibiyar al’adu tun karni na daya bayan haihuwar annabi Isa.

Garin yana Kudu maso gabas a kasar Turkiyya, inda bai wuce kilomita 44 daga birnin Şanlıurfa ba. Garin yana matsayin mahadar Mezopatamya da tekun Bahar Rum.

 

Alluka da masu tone-tone suka biciko sun nuna cewa kimanin shekara dubu hudu sunan garin bai canja ba. Ma’nar kalmar kuwa an samota ne daga yaren Sumeriya inda ma’anar tana iya zama “tafiya” ko kuma “hanya”.

Garin Harran ya kasance yana wata hanya wande dole sai an biyata yayinda ake zirga zirgan kasuwanci. Kasancewar garin yana matsayin hanyar da ta hada mazopatamya da Anatoliya yasa garin na da al’adu iri iri.

Garin na da muhimmanci cikin tarihi musamman a bangaren ilimin kimiyyai, al’adu da kuma falsafa.

Yau ‘makarantar falsafar Harran’ da na daga cikin manyan makarantun falsafa guda uku a duniya. Jami’ar Harran wanda aka assasata tun karni na daya ta taka rawa wayen horan manyan malaman ilimi a duniya.

Daya daga cikin mayan malaman ilimin da suka yi karatu a jami’ar Harran shi ne haifaffen karni na 800 wato Sabit bin Kurra wada shi ne ya fassara littafan lissafi da aka wallafa a kasar Girka zuwa harshen Larabci, haka zalika da kuma littattafen magani.   Bayan haka mutun nan da ya lissafa nisan duniya zuwa wata, wato Battani, da kuma Jabir bin Hayyan wanda ya ilimantar da jama’a kan kwayar halitta na daga cikin mutananen da suka yi karatu a jami’ar. Bayan haka a bangaren ilimin addini İbn Teymiyya na da daga cikin mutanen da suka yi karatu a jami’ar.

Jami’ar ta daukaka a tarihi musamman wajen mayan bincikai da ta wallafa.

Garin ya kasan ce karkashen daular Musulunci dake hannun Turkawa har zuwa shekara ta shekerar 1260 inda sojojin Mangoliya suka kai hari. Daganan ne dai garin ya tarwatse ila yau.

Binciken da aka yi kan wani tudu mai tsawon mita 22 da ke garin ya nuna cewa anyi dubban shekaru ana rayuwa a garin ba tare da yankewa ba. Har yau ana cigaba da tone-tone domin gano sabin gidajen tarihi a garin.

Ganuwar Harran na  daga cikin manyan gidajen tari a garin. Bincike ya nuna cewa an gyara ganuwar a karni na 11 inda aka fadada ta sannan aka kara gina sabin dakuna.

A gefe guda Babban masallacin Harran da aka gina a karni na 8 na  daya daga cikin masallacen da aka fara ginawa a yankin Anatoliya. Masallacin dai shi ne Masallacin farko mai haraba da aka fara ginawa a yankin. Haka zalika shi ne na farko a bangaren kayan ado da ake sawa a bangon masallaci.

Mutun-mututumin da aka gina a lokacin Babila wanda ke wakiltar wani gwunki da ake kira Sin, gini mai sunan “garin annabi shuaibu”, Masallaci da aka yi lokacin babban malamin musulunci sheik Yahaya Hayat Al-Harrani na daga cikin wuren tarihi masu mahimmanci dake garin.

Baya ga wadannan “Gidajen Harran” na daga cikin wuraren tarihin da aka fi ziyarta. Gidajen suna da dadin zama inda lokacin zafi suke daukan sanyi da sanyi kuma suyi dumi. Gidajen dai suna karkashin kulawar kungiyoyin tone-tone tarihi na duniya.

Dubban mutane suna cigaba da ziyartar wannan garin tarihi mai matukar bansha’awa a ko wacce shekara. Baki daga cikin kasa da kuma kasar waje suna matukar farinciki da wannan gari wanda ke sa mutun ya fada cikin kogin tarihi.Labarai masu alaka