Jidali da tashin hankali tsakanin Amurka da Iran

Ga dukkan alamu a halin yanzu ba Amurka ce ke jagorantar tattalin arziki, kimiyya, fasaha, siyasa da ɗa'a (adalci, hakkin bil'adama da tarbiyyar) duniya ba

Jidali da tashin hankali tsakanin Amurka da Iran

Babban masani a duniyar lslama Ibni Haldun ya danganta gwamnati da bil'adama. Kamar yadda ya bayyana ƙasashe tamkar bil'adama ne ana haihuwarsu, suna girma suna kuma mutuwa. Masanin daular Usmaniyya Katip Çelebi ma ya yi irin wannan sharhin. A haƙiƙanin gaskiya mun ga yadda ƙasashe da dauloli suka ɓace daga doron ƙasa. Kamar dai yadda nayi bayani a baya, abu ɗaya da bai canjawa shi ne canjin karan kansa.

 

Mun sake kasancewa tare da ferfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar ilimin siyasa a jami'ar Yıldırım Beyazıt.

 

A halin yanzu dai mun kasance cikin irin wannan yanayin. Ga dukkan alamu a halin yanzu ba Amurka ke jagorantar tattalin arziki, kimiyya, fasaha, siyasa da ɗa'a (adalci, hakkin bil'adama da tarbiyyar) duniya ba. Ba'a kuma hasashen Amurka zata iya dawo da martabar ta na jagorantar wadannan fannoni. A sabili da haka ne take kokarin daukan matakan ƙalubalantar lamurkan tattalin arziki, katsalandar siyasa da mamaye domin kare martabar ta da ikonta a fadin duniya.

lre-iren waɗannan matakan kare kai na karantar damu munanan ƙarshe, ba wai abubuwan da zasu haifar da ƴaƴa masu ido ba.

 

lre-iren waɗannan matakan tada ƙayan baya, da Amurka ke ɗauka ta amfani da ƙarfin soja da kuma tattalin arziki tafi ayyanar dasu akan lran fiye da  China, ƙasashen yamma, ƙasashen Latin dama Turkiyya. Musamman yadda Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ita tilo hakan ya ƙara tada hankalin yankin Hormuz baki ɗaya.

Amurka a kodayaushe tana jan kunne tare da yiwa lran barazana akan yunƙurin ta na mallakar makaman nukiliya. Haƙiƙa bai kamata a mallaki makaman da zasu iya hallaka ba wai ɗan adam kawai har da dukkanin halittu a doron ƙasa kamar yadda Amurka ta yi a ƙasar Japan. Tabbas yadda makaman nukiliyar Iran zasu kasance ƙalubale a doron ƙasa haka ma makaman Amurka, lsra'ila da lndiya suka kasance. Yadda ma lsra'ila wacce ta tanadi makaman masu guba tana amfani dasu a yankin hakan ya ƙara ɗaga ingancin lran a yankin.

 

Yaɗuwar manufar lran

Duk da ƙalubalantar da Amurka ke yi, lran tana da magoya baya a yankin. Hakan nada nasaba da matakan yaɗa mazhabar da lran ɗin ke kai a yankin. A halin yanzu lran ce keda ikon manyan biranen ƙasashen lraƙi, Siriya, Yaman da Lebanon.

lran na ɗaukar matakan yaɗa manufarta tamkar yadda ƙasashen jari hujja ke yi a doron ƙasa. A yayinda take katsalandan a kasashen dake kudanci da ita tana kuma isar da sakonta ga wasu ƙasashen da take da ra'ayi dasu.

lsra'ila ce tafi damuwa da wannan manufar yaɗa mazhaba da lran ke yi a yankin, wannan shi ne babban dalilin da ya sanya lsra'ila ƙaddamar da wasu matakai a yankin gulf domin ƙalubalantar lamurkan lran a yankin. Abin nuni anan ko dai matakan lran a yankin na damuwar lsra'ila ko a'a, matakan na lran sune umul aba'isan matsalolin da ƙasashen Musulmi a yankin suke ciki.

 

Katsalandan ɗin Amurka

Za'a dai iya sukar Iran sabili da waɗannan abubuwan da take yi da muka ambata da ma waɗanda bamu ambata ba. Amma ƙalubalantar da Amurka ke yiwa lran ba abu ne da za'a taɓa ɗauka da idanun basira ba. Sabili da ita kanta Amurka ba kasace dake tafiya akan tafarkin adalci ba. Amurka na ƙalubalantar lran ne kawai domin biyar buƙatun ta, musamman irin jari hujjan ƙarnin na 19 da 20. A yau matakan da shugaba Donald Trump ke ɗauka a fadin duniya yama fiye waɗanda shugaban garin lndiyawan yankin Eskimo ya gudanar a garinsa.

A ɗayan barayin kuma muna sane da ƙasashen da Amurka da wasu ƙasashen yamma suka mamaya har ila yau basu taɓa samun sukuni ba. A yankunan sai mace-macen miliyoyin mutane, zubar da hawaye, yin hijira daga yankunan dake cikin uƙuba, rashin adalci da ta'addanci.

 

Sakamakon da Katsalandan zai iya haifar wa

Ba mamaki dukkanin ƙalubalantar da Amurka ke yiwa lran tana nemanta tabi ƙa'idodinta ne kawai. Kamar yadda ya faru a kwanakin baya, a wannan karon ma matsalar ka iya haifar da babban damuwa kwarai da gaske. Muna dai fatan kar lamarin ya yi ƙamari, duk da mun kasance cikin yanayin da muke ta ganin yiwuwar barkewar yaƙi a ko wacce rana, lamarin da ba zai haifar kowa ɗa mai ido ba.

A gabas ta tsakiya kamar yadda lran ta yi a wasu ƙasashe, ta jagula lamurkan Siriya kuma sabili da haka lamurkan yankin sun taɓarɓare baki ɗaya. Koda za'a iya kawo karshen fitinun da suka rage a gabas ta tsakiya a halin yanzu yankin zai kasance fagen baje kolin ƴan jari hujja tamkar yadda lamurka suka gabata a lokacin yaƙin duniya na farko. A cikin wannan halin dai Turkiyya tafi ko wace ƙasa jin jiki kasancewar yadda lamurka suka dagule a Siriya. Yadda ƙasashen yankin suka taɓarɓare wasunsu kuma suka kasance ƙasashen jeka na yi ka, na tabbatar da nasarar matakan ƙarfafa lsra'ila a yankin. lsra'ila ce dai wacce taci riban ƙalubalantar da Amurka ke yiwa lran dama yadda Siriya ta kasance. Dukkanin matakan da lsra'ila ke ɗauka a yankin ba wai domin ƙashin kanta take yi ba, tana yi ne domin inganta lsra'ila. lndai akwai wasu ƙasashe da zasu saura da iko a yankin toh , lsra'ila ne da Amurka.

 

Me Turkiyya zata iya yi ?

 

Turkiyya ce wacce tafi ko wace ƙasa fahimtar cewa shiga tsakanin hukumomin ƙasa da ƙasa a yankin ba zai iya kawo karshen rikicin yankin da ta'addanci ya mamaye ba. A dalilin haka ne Turkiyya ke daukar matakan tabbatar da lumana bisa adalci a yankin. Dukkan matakan da Turkiyya ta dauka a kasashen Siriya, Misira, lran da lraƙi tayi su ne bisa tubalin adalci.

A cikin wannan halin, Turkiyya na ƙara tabbatar da tarbiyya a yankin ta ɗaukar matakan da zasu kauda dukkanin fitinu da rigingimu a yankin. Turkiyya zata iya haɗaka da ƙasashen nahiyar Turai, China, Rasha dana yankin gulf har ma da Amurka da lran domin samar da lumana a yankin.

Turkiyya tana sake ɗaukar matakan da ta ɗauka da Brazil da lran a kwanakin baya. Da hakan ne ta dauki wani mataki da Rasha lamarin da ya kange dubban Siriyawa daga faɗawa cikin halin ƴan gudun hijira. Turkiyya zata iya taimakawa wajen samar da zaman lafiya a yankin lndiya, Afirka, Balkan da Afganistan. Duk da dai ƙasashe da yawa basu kasance masu tafiyar da hurɗa akan ɗa'a ba, Turkiyya a matsayar ta na shugaban Tarayyar Ƙasashen Musulmi a halin yanzu zata iya daukar matakan da zasu kange barkewar yaƙi tsakanin Amurka da lran.

Wannan sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban tsangayar ilimin siyasa a Jami'ar Ankara Yıldırım BeyazıtLabarai masu alaka