Birnin Sinop mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Wani birni da ake Kira Sinop na daya daga cikin wurare masu matukar bansha’awa a yankin Bahar Asuwad a kasar Turiyya.

Birnin Sinop mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Wani birni da ake Kira Sinop na daya daga cikin wurare masu matukar bansha’awa a yankin Bahar Asuwad a kasar Turiyya. Tekun Bahar Asuwad da kuma kyakkyawar dabi’ar da ta zagaye birnin na daga abubuwan dake jan hankalin masu ziyara.

An kafa birnin ne dai a matsain wurin kasuwanci a shekara ta 700 kafin haihuwar annabi Isa. Bincike ya nuna cewa Asopos ne ya sakawa garin suna, inda dai yaba birnin sunan ‘yar sa, wato Sinope. Wani bincike daban kuma cewa ya yi an samo sunan ne daga wurin Assuriyawa, inda suka bawa garin sunan gwunkin su, wato Sin.

Binciken tone-tone sun numa cewa birnin ya kasance yana da yawan jama’a tun karni na daya bayan haihuwar annabi isa. Kasancewar jiragen ruwa suna iya zirga zirga ciken sauki a birnin yasa ja’ama na jin dadin zama a birnin. Baya ga haka muguwar iskar dake tasowa daga tekun bahar Asuwad bata isowa birnin. Wannan na daga dalilin daya sa ake kara samun yawan jama’a a birnin. A lokacin mulkin sarkin Makedoniya Iskandar ne dai birnin ya kara bunkasa, inda sarkin ya tattaro masu ilimin falsafa da kimmiya domin suyi ayyukan ilimi. Daga baya dai birnin ya koma hannun daular Rumawa da daular Bazantiya, inda a karshen karni na 11 mulkin birnin ya koma hannun Turkawa. 

Shuke-shuken dabi’a da gidanjen tarihi masu bansha’awa na daga ga cikin abubuwan dake daukan jan maziyarta. Cikin tsofaffen wuraren ziyarar kuwa ita ce rijiyarnan mai suna Hamsilos. Wani lokaci a cikin tarihi an kasance ana boye jiragen ruwan yaki a cikin rijiyar, inda a yau kuma masu kamun kifi suke buya yayinda iska ta taso. Wannan rijiya dai babu irin ta a duniya idan banda wata rijiya wadda ke kasar Noway.

Sarıkum, Karakum da kuma Akliman na daga cikin wuraren da masu yawan shakatawar teku suka fi ziyarta.

Haka zalika Matsirga mai suna Erfelek na gada cikin wuraren za yakama masu son yawo cikin dabi’a su ziyarta. Matsirgar tanada idanuwan ruwa manya da kanana har 28, inda mutun sai ya taka matakala 28 kafin ya iso idon ruwan karshe, inda a nan ne dai maziyarta ke shan kafen Turkiyya.  

Wani wuren ziyara kuma shine ganuwar Boyabat. Ganuwar dai an yi ta ne a shekara ta 700 kafin haihuwar annabi Isa.

Haka zalika hasumiya mai fitila wanda Turkawa suke kira İnceburun Deniz feneri na daga wuraren da aka fi ziyarta a birnin Sinop. Hasumiyardai an gina ta ne a karni na 19, ina ila yau tana ci gaba da nunawa jiragen ruwa hanya. Baya ga haka maziyarta na iya hawa hasumiyar domin kallon dabi’ar bahar Asuwad mai ban sha’awa.

Daya daga cikin waruren gidan tarihin dake birnin Sinop shine gidan Kurkukun Sinop. Gidan kurkukun dai an ginasa ne a matsayin ganuwa a shekaru darruka da suka gabata, inda daga baya aka sauya tsarin ginin sannan aka kara dakuna da dama. Ginindai anyi anfani da shi a matsayin masana’antar kera jiragen ruwa daga baya kuma aka mai dashi gidan kurkuku inda a yau ake anfani da shi a matsayin gidan tarihi.

Akgöl, Kogon İnaltı, da gidan tarihin ilimin tone-tonen tarihin Sinop na daga cikin wuraren da yakama dukkan mai yaban bude ido ya ziyarta a birnin Sinop.

A gefe guda, Sinop ne birnin da aka haifi ficiccen malamin falsafa Diyojen. Sannan mutanen birnin sun fi kowa jin dadin rayuwa a binciken da kanfanin kidayar Turkiyya ya kaddamar.

Ko da ba fada ba, gidajen tarihi da kuma dabi’ar dake birnin Sinop su ne dai sinadarin da ke sa jama’ar birnin cikin walwala. To kuma idan harkunason shakatawa cikin dabi’a to kuyi maza ku je birnin Sinop.


Tag: Sinop , Tarihi

Labarai masu alaka