An kashe jami'an tsaro 3 da fursunoni 29 a wani gidan kurkuku dake Tajikistan

Sakamakon wani rikici da ya barke a gidan kurkukun da ake daure da 'yan ta'addar Daesh a Tajikistan gandirobobi 3 da fursunoni 29 sun rasa rayukansu.

Ma'aikatar Shari'a ta Tajikistan ta fadi cewar rikicin ya barke a lokacinda 'yan ta'addar Daesh suka caka wa gandirobobi 3 da fursunoni 5 wuka tare da kashe su a gidan yarin dake kusa da Dushanbe babban birnin kasar.

Sanarwar da Ma'aikatar ta fitar ta kara da cewar jami'an tsaron da suka kai farmaki kan gidan yarin dake da fursunoni dub 1,500 sun kashe 'yan ta'addar Daesh 24 inda daga baya aka sake tabbatar da tsaro a cikinsa.

An bayyana cewar wanda ya fara tayar da rikicin shi ne Behruz Gulmurad dan gidan tsohon kwamandan Daesh Gulmurad Halimov.

 Labarai masu alaka