Birnin Istanbul mai dimbin tarihi dake nahiyoyin Turai da Asiya

Santambul birni ne da ke hada nahiyoyi biyu,wato Turai da kuma Asiya.

Birnin Istanbul mai dimbin tarihi dake nahiyoyin Turai da Asiya

Sabili da inda yake, a tsawon karnoni da dama birnin ya ci gaba da kasancewa da  muhimmiyar magamar kabilu da kuma al'adu masu dumbin yawa.

Santambul wanda aka kafa a karni na bakwai miladiya,ya kasance babbar matattarar kabilu mabambanta, al'adu masu tarin yawa,addinai marasa adadi da kuma manyan dauloli.

A tsawon tarihinsa, birnin ya zama cibiyar sanannu kana manyan daulaoli wadanda suka hada da daular Kirstanci ta Roma, daular Roma ta Gabas da kuma daular Musulunci ta Turkawan Usmaniyya.Yanayin wannan birnin wanda ke cike makil da alamomi da kuma tarihin kabilu da dama wadanda suka bambanta, na da kyan gaske kuma babu kamarsa a duk fadin duniya.Abinda yasa a shekarar 1985 hukumar raya al'adu, fasaha da kuma ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya ta saka sunan Santambul a jerin sunayen muhimman wuraren tarihi.

A duk tarihin bil adama ana kiran Santambul da suna "Rabin Tsibiri" sakamakon yadda a mashigin Halıç a arewaci,mashigin Istanbul a yammaci da kuma Tekun Marmara a kudanci suka yi wa birnin mai cike da tarihi, zobe.

An saka yankuna hudu na wannan rabin tsibirin a jerin sunayen wuraren tarihi mafiya muhimmanci na duniya a matsayin "Wuraren tarihi na Santambul".Wadannan yankunan sun hada da,tsohon birnin tarihi na Sultanahmet,tsararren wurin tarihi na Süleymaniye, tsararren wurin tarihi na Zeyrek da kuma tsararrun katangun tsohuwar birnin Santambul.

Tsohon birnin tarihi na Sultanahmet na kunshe da wurare kamar su, fadar Topkapı Saray, filin sukuwa, tsohon cocin Aya irini da kuma karamin masallacin Ayasofiya.

Topkapı Saray, fada ce ta sarakunan daular Musulunci ta Turkawan Usamniyya.Usamniyawa sun share karnoni da dama suna mulkar duniya daga wannan mashuriya kana katafariyar fadar ta shugabanci.Topkapı na a sahun daya daga cikin muhimman fadajin daular Usmaniyya...Sarkin Fatih Sultan Mehmet ne ya fara kaddamar aiyukan gina wannan fadar inda daga bisani aka kammala gina shi a karshen karni na 15 miladiyya.

A wancan zamanin fadar Topkapı Saray ta kasance wurin rayuwar akalla mutane 4000.

Darjar wannan fadar wacce aka gina a wani wuri mai fadin kusan eka dubu 80 ta fara faduwar warwas a sa'ilin da aka gina sabbin fadojoji.Amma an ci gaba da yi amfani da wannan muhimmin wurin a matsayin wurin adana tsarkakkun kayayyakin tarihin addinin Musulunci,baitulmali da kuma cibiyar buda kudade.


 

An fara bai wa jama'a damar ziyartar fadar Topkapı Saray a matsayin wurin ajje kayayyakin tarihi a shekarar 1923 bayan gushewar mulkin daular Usmaniyya.

A wannan fadar wacce a tsawon karnoni da dama ta kasance helkwata kana cibiyar Daular Usmaniya wacce ta mulki duniya akwai,kayayyakin tarihi masu kayatarwa wadanda suka samo asali daga fasahar kwararrun magina da kuma mazayyanan daular Usmaniyya wadanda suka hada da zane-zane masunkyan gaske, rubuce-rubucen hannu na addinin Musulunci, tufafi,makamai, hotunan da ake ratayewa a katanga,kayayyakin yau da kullum da kuma litattafan da ke dauke da labaran rayuwar ahlin fada gami da taskoki da kuma jauharan marasa misaltuwa wadanda suka fito daga fadojin Usmaniyawa.

 

Ayasofiya na a jerin daya daga cikin muhimman gine-ginen birnin Santambul...An fara kaddamar da aiyukan gina wannan tsohon cocin a zamanin daular Bizans a wajejen shekaru 500 gabanin haifuwar Annabi Isa (AS).Cocin ya shahara haikan saboda kubbarsa.A yau, ana ci gaba da amfani da wannan babban wurin tarihin wanda  salon gininsa yasa aka bude wani sabon shafin a tarihin gine-ginen duniya, a matsayin gidan ajje kayayyakin tarihi.

An gina yankin da ake da "Filin Sukuwa" a wajejen shekaru 200 kafin haihuwar Annabi Isa (As) da zummar gudanar da aiyukan da suka danganci wasannin motsa jiki da kuma zamantakewarmu ta yau da kullum.A yau ba riski komai na wannan wurin ba face baraguzai.

 

 

Aya irini da kuma karamin masallacin Ayasofiya, muhimman cocuna ne biyu da mabiya addinin Kirista na shiyyar Ortodocs suka gina a zamanin daular Bizans.

Süleymaniye, masallaci ne da babba kana hamshakin maginin nan na sarkin daular Musulunci ta Turkawan Usmaniyya, Mimar Sinan ya gina a karni na 16 miladiyya karkashin jagorancin sarki Kanuni Sultan Suleman.A yau,Sulemaniye ya kasance daya daga cikin wuraren tarihin da suka sa Santambul ke ci gaba da shanawa a idanun duniya.An gina masallacin a matsayin wata katafariyar kuliya wacce za ta magance matsalolin mutanen Santambul a fannonin da suka jibanci addini,zamantakewa da kuma raya al'adu.

 

 

A wajen masallacin akwai,asibiti,wurin wanka,gidan sauke baki,makarantun İslamiyya hudu,tsangayar ilimin kiwon lafiya da kuma cibiyar tallafa wa marayu da kuma marasa gata.Kawo yanzu, da yawa daga cikin wadannan wuraren na ci gaba da aiki.

A yankin tsararren wurin tarihi na Zeyrek akwai, masallacin Zeyrek, haikalin Pantakrotar da kuma wani muhimmin wurin da ke kunshe da cocuna uku na kiristan Ortodocs....An gina haikalin Pantokrator a karni na 12 miladiyya,wanda aka maida makarantar Islamiyya bayan da aka bude birnin Santambul.

 


Wannan yankin na da matukar muhimmanci sakamakon yadda ke cike makil da misalai da dama na kyawawan gine-ginen muhallan Usmaniyawa, tsarin rayuwarsu da kuma salon ginin wancan lokacin.Gadije mafiya tsufa na Santambul ma na wannan yankin.

UNESCO ta saka suna Zeyrek a jerin sunayen muhimman wuraren tarihin da ke fuskantar barazanan gushewa da doron duniya har illa mashallah.Abinda yasa ta yanke shawarar sake gina yankin.

Tsararrun katangun Santambul na gaf da tsohuwar cibiyar birnin mai dumbin tarihi da kuma tekun da ke kewaya da shi.

 

An fara gina katangun a karon farko a karni na 4 miladiyya inda daga bisani a tsawon shekaru da dama aka dinka yi ma ta kari da kuma kawo sauye-sauye marasa adadi.

Manyan kofofin wadannan katangun wasu alamu ne da ke nunawa jama'ar da ke kawo ziyara Santambul irin karfi da Daular Usmaniyya ta ke da shi. Kawo yanzu ana ci gaba da amfani da wannan kofofin. A zamanin sarakunan Usamniyya an yi sabunta wadannan kofofin sau bila adadin,kazalika an sake gina wasu daga cikin sassan wannan yankin.

babu kamar tarihin Santambul wanda kyansa ya zama abin ilhama ga marubutan litattafi,sha'irai da kuma mashiryan fina-finan duniya ga baki daya.Abinda a bara, kusan masu yawo bude ido milyan 14 suka ziyarci birnin da nufin kashe kwarkwatn idanunsu.



Labarai masu alaka