Tsohon garin Cumalikizik mai tarihi dake Turkiyya

Kauyen Cumalıkızık na yankin Marmaran kasar Turkiyya.

Tsohon garin Cumalikizik mai tarihi dake Turkiyya

Kauyen Cumalıkızık na yankin Marmaran kasar Turkiyya,wanda kawo yanzu yake ci gaba da shanawa sakamakon gajajjen kyan yanayinsa wanda ya samo asali daga tarihinsa,ingatattun gidaje da kuma kyawawan titunsa,tabatacciya kana kwakkwarar hujja ce ga dukannin wadanda suka dasa ayar tambaya kan: "Shin yaya rayuwar karkara ta ke a yankin Anatoliya a zamanin Daular Usmaniyya ?"

A shekarar 2014, Hukumar raya al'adu da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya,UNESCO ta saka sunan Cumalıkızık da na iyakokin jihar da ke kunshe da shi a jerin wurare tarihi mafiya muhimmanci na duniya.Sabili da wannan yankin na da babban matsayi,musamman ma a wajen gabatar wa duniya tarihin Musulunci ta daular Usmaniyya...

A jihar Bursa,akwai muhimman wuraren tarihi 6 da hukumar UNESCO ke gwagwarmayar karewa ta hanyar amfani da taken "Bursa da Cumalıkızık: Gabashin Daular Usmaniyya",wadanda suka hada da kulliyar Orhangazı da yankin Hanlar da ta kunsa,Kulliyar Hüdavendigar,kulliyar Yıldırım,koriyar Kulliya,Kuliyyar Muradiye da kuma shi kansa kauyen Cumalıkızık...

Tun daga farko karni 14 miladiya, Bursa,wanda ya kasance babbar hekwata ta farko ta daular Usmaniyya,ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a tarihin yankin ta hanyar bunkasa babu kakkautawa a fannonin da suka danganci zamantakewa,al'adu da kuma kasuwanci.A zamanin mulkin daular Musulunci ta Usmaniyya,an gina masallatai,makarantun Islamiyya,katafarun kaburbura,muhallan sauke baki,gidajen wanka,cibiyoyin tallafa wa marasa gata da kuma galihu,asibitoci da kuma shaguna siyar jauharai masu dumbin yawa.Tsarin birnin Bursa ya zama misali ga sauran biranen daular Turkawan Usmaniyya da aka gina daga baya.

A jerin manyan dalilan da suka sa sunan Bursa ya kasance a a jerin muhimman wuraren tarihi,akwai kyaukywan yanayin garin da kuma ingantattun alamomin da ke nuna kafuwar wata babbar daular Musulunci a yankin Antoliyan kasar Turkiyya wacce kuma ta mulki duniya ga baki daya.

Gidajen da aka gina a kimanin shekaru 700 na kafuwar Daular Usmaniyya,na jan hankalin maziyarta ta hanyar karkanta tunaninsu daga zamaninmu na yau ya zuwa karnoni aru-zaru da suka gabata.

Kawo yanzu,kauyen Cumalıkızık wanda ke a tazarar kilomita 13 daga tsakiyar birnin Bursa, a gabar tsaunin Uludağ na ci gaba da haskawa saboda babu abinda ya sauya daga kyaukyawan yanayi da kuma tsarin cude-ni-in-cude-ka da al'umar wannan yankin  ta gada tun kakanni da uwaye. A tashin farko,akwai gidajen da aka gida duba da salon maginan daular Usmaniyya,wadanda ke kama da budaddun cibiyoyin ajje kayayyakin tarihi sakamakon titunan duwatsu masu kunshe da hanyoyin kwararar ruwan sama da ke a tsakiyar su da kuma maka-makan gine-gine da sassaken tarihi da suka kunsa.....Gidajen laka,katangu masu launuka iri-iri da kuma famfunan da ke jere kan tintuna zasu dauke ku daga wannan duniya don isar ku zuwa duniyar mazan dauri.

Duk da cewa kowace shekara,Cumalıkızık na karbar bakwancin dubun dubatan masu yawon shakatawa,kawo yanzu aiyukan da suka jibanci noma na ci gaba da bunkasa.Mazauna wannan kauyen na siyar da albarkatun nomansu a kasuwannin yankin....

Idan har kafufunku suka kai ku Bursa,muna shawartar ku da kar ku koma gida ba tare kun ziyarci, tsaunin Uludağ,gidajen waha wadanda ruwansu ke matukar warkarwa,sayen  yadinan silki na yankin da kuma dandana dadadan girke-girke,wadanda suka hada da İskender kebabı,kayan kamulashen Kemalpaşa da kuma alawar Chestnut,wato kestane şekeri.Labarai masu alaka