Garin Bergama mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Arewacin Turkiyya, musamman ma yankunan da ke a gabar tekun Aegean na cike makil da kayayyakin tarihi.

Garin Bergama mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Bergama wanda ke a akalla tazarar kilomita 100 daga birnin Izmir, na a jerin wadannan muhimman wuraren tarihin wadanda magama ne na al'adu bambanta...A wuraren da ke a manisanciyar tazara,akwai wani kyaukyawan yanayin tarihi da ke nuna cewa,kabilu masu dumbin yawa sun rawu a wannan yankin a wasu zamaninnika da suka gabata.Kazalika,akwai muhimman alamomi da dama da ke nuna dukannin matakan da bil adama ya cimmawa a wajen bunkasa rayuwarsa.

A shekarar 2014,kungiyar raya al'adu, kimiyya da kuma ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya,UNESCO ta saka sunan Bergama,wanda daya ne daga cikin manya, kyawawa kana katafaran cibiyoyin al'adu da kuma fasaha,a jerin sunayen muhimman wuraren tarihi na duniya.

Bergama,magamar al'adu barkatai na cike makil da kayayyakin tarihin na zamanin daulolin Helenistic,Roma, gabashin Roma da kuma daular Musulunci ta Turkawan Usmaniyya.Da yake daya bayan daya,kabilu daban-daban sun rayu a wannan yankin,Bergama ya kassance daya daga cikin biranen zamanin mutanen dauri wadanda babu kamar su,musamman ma idan aka yi la'akari da salon gine-ginen gari.

A cewar rubuce-rubucen mutanen da,garin da a yau ake kira da suna Pergamon, ya kasance babban helkwatar masarautar ahlin Attalos a wajejen shekarar 200 miladiyya.Kazalika birnin ya cimma matsayin babbar cibiyar al'adu,fasaha da kimiyya da kuma siyasa.Bayan haikalai,gidajen wasannin kwaikwayo da kuma fadojin da ya kunsa, a Bergama an gina wani babban gidan litattafai.

A Bergama, a shekarar 133 miladiyya, bayan rugujewar daular Roma,an gina asibitin Asclepion, daya daga cikin muhimman cibiyoyin kiwon lafiya na wancan zamanin.

Yankin na kunshe da manyan wuraren tarihi tara, wadanda suka hada da Pergamon, Tsarkakken dandalin Kibele,Tudun İlyas,Tudun Yığma,Tudan İkili, Tudan Tavşan, Tudun X Tepe, Tudun A Tepe da kuma tuddan Maltepe.

An fara yi wa birnin daukar sakainar kashi a lokacin daular Bizans.Bergama ta zama wani katafaren kauye marar amfani sakamakon sauya hanyoyin kasuwanci da attajiran duniya suka yi.

Birnin tarihi Bergama ya fara kasancewa a karkashin ikon daular Musulunci ta Turkawan Usmaniyya a farkon karni na 14.A wannan zamanin an fafada birni da kuma sauya al'adunsa.An gina gidajen wanka,gadoji,gidajen sauke baki,kasuwanni da kuma rufaffun cibiyoyin cinikaiyya duba da salon gine-gine na daular Usmaniyya.

An fara gudanar da tone-tonen gano kayayyakin tarihi a karon farko a wajejen shekarar 1870.A yau, an gano kusan illahirin yankunan wannan tsohon birnin.Wani bangare na wadannan kayayyakin tarihin an adana su a gidan ajje kayayyakin tarihi na Bergama,wanda shi ne gidan ajje kayayyaki na farko na kasar Turkiyya.

Bergama Akropölü,inda a nan ne ahlin sarakunan wannan yankin,manyan jiga-jigai da kuma hafsoshin soja suka rayu,na da fasololin gine-gine marasa misaltuwa.A yau, abun bakin ciki ne, ganin yadda babu abinda ya saura daga daya daga cikin muhimman wuraren ibada,wato haikalin Athena face gimshikansa.Birnin na asali na a gidan ajje kayayyakin tarihi na Pergamon da ke Balin.Haka zalika,wani muhimmin ginin tarihin na daban,wato haikalin Zeus ma, na a birnin Balin na Jamus.

Haikalin Agora da na Dionysos, da kuma wani gidan da ke kunshe da sama da litattafai dubu 200 a wancan zamanin,na a sahun muhimman gine-ginen Bergama.Ana kyautata zaton cewa, daya daga cikin kwamandojin soja na daular Roma Marcus Antonius ne ya bai wa sarauniyar Misira Cleopatra kyautar wadannan litattafai.

Gidan wasan kwaikwayon Bergama, shi ne wurin tarihin mafi muhimmanci bayan haikalolin daulolin Girka da na Roma.Wannan ginin na kan wani tsayayyen gimshiki.Abinda yasa ya kasance gini mafi inganci da nagarta.Wannan gidan wasan kwaikwayon na daukar akalla 'yan kallo dubu 10.

A yankin da aka fi sani da suna birnin kasa,akwai Agora,makarantar Gunki,muhallai da kuma haikalin Serapis.Wannan wurin wanda aka maida shi coci a washegarin rungumar addinin Kiristanci da daular Roma ta yi,ya kasance daya daga cikin tsarkakkun cocuna guda bakwai da aka ambaci sunansu a litattafin Injila.Ya zuwa yanzu,wannan cocin ya kasance majami'a daya tilo da aka gano .

Haikalin Demeter da kuma Gymnasion da aka gina da zummar bai wa 'yan wasan motsa jiki damar karawa da juna,sun kasance a sahun wurare mafiya muhimmanci na Bergama.

Bugu da kari,a wannan birnin na mazan dauri wanda ya ci gaba akwai wata katafariyar cibiyar kiwon lafiya, wacce aka gina da nufin daukaka sunan abin bautan Asklepios, mai kula lafiyar bil adama da ta dabbobi.Haka zalika, Asklepion ya kasance daya daga cikin manyan cibiyoyin warware matsalolin da suka jibanci kwakwalwa.A wannan cibiyar,an gudanar da gwaje-gwaje da kuma nazarce-nazarce da dama a fannin kiwon lafiya.

Shawararmu ga masu sauraranmu da ke da aniyar zuwa yankin Antoliyan kasar Turkiyya da zummar kai ziyara tsohon birnin tarihi na Bergama shi ne,kar su sake su koma gida ba tare da sun amfana da ruwa mai warkawa na wuraren waha da kuma dandana dadadan abinci da kayayyakin makwalashe na wannan yankin,wadanda suka hada da kala daban-daban na cikwi da  halawar Lokum,wato Turkish Delight.Labarai masu alaka