Shin ko NATO muhimmiyar kungiya ce?

Bayan kammala yaƙin ne ƙasashen dake bin tsarin demokradiyya suka kafa kungiyar NATO.

Shin ko NATO muhimmiyar kungiya ce?

A wasu bayanai da suka fita daga ƙasar Amurka a ƴan kwanakin nan sun yi nuni da kasancewar yadda Turkiyya ta ƙalubalanci Amurka akan taimakawa ƴan ta'adda a Siriya da kuma akan lamarin makamin S 400, lamarin daya sanya Amurkan binciken kasancewar Turkiyya a matsayar mambar kungiyar NATO. Shin ko kalaman mataimakin shugaban kasar Amurka da yake cewa “Dole Turkiyya ta ɗauki mataki guda” na nufin barazana ne ga yarjejeniya mai inganci tsakanin ƙawayen biyu, ko kuwa hakan na nufin jefa yarjejeniyar ƙasashen biyu ne cikin kwandon shara. Haka kuma amsar da mataimakin shugaban kasar Turkiyya Oktay ya bayar inda yake cewa “lta ma Amurka ya zama wajibi ta yanke hukunci ɗaya” shin hakan na nuni ne da ta kasance ƙawar Turkiyya mai inganci ko kuwa zaɓi ne ga Amurkan da ta ci gaba da goyawa ƴan ta'adda baya da zasu ci gaba da ƙalubalantar ƙawayenta a NATO ?

 

 Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da ferfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar siyasa a jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt.

Da farko dai waɗanda ke sukar kasancewar Turkiyya a ƙungiyar NATO bawai shugabannin kungiyar ko mambobin ƙasashen bane, wannan abu ne da Amurka ke yi ita tilo.

Abubuwan da suka ɗoru akan Turkiyya da kuma gudunmowar da NATO ke bata.

A yaƙin duniya na biyu ne ƙasashe masu ra'ayin Facism sunka yi rashin nasara. Ƙasashen dake da ra'ayin demokradiyya suka yi nasara. Bayan kammala yaƙin ne tsarin mulkin demokradiyya ya fara yaɗuwa a faɗin ƙasashen duniya.

Haka kuma bayan kammala yaƙin ne ƙasashen dake bin tsarin demokradiyya suka kafa kungiyar NATO.

A sanadiyar ƙalubalantar da Turkiyya ta fuskanta ƙarara daga Rasha a shekarar 1945  ya sanya Turkiyya zaɓen kasancewar ta da ƙasashen yamma.

Bayan dai kammala yaƙin duniya na biyu babban taimakon da NATO ta baiwa Turkiyya shi ne kasancewar ƙasar akan tsarin demokradiyya.

Da ba'a samu tallafin yin hakan daga waje ba da Turkiyya ta samu jinkirin ƙaddamar da mulkin demokradiyya.

A lokacin yaƙin cacar baki watau cold war ma NATO ta taimakawa Turkiyya a fagen kareta daga ƙalubalolin da suke fitowa daga ƙasar Rasha.

Baya ga wadannan gudunmawa da kungiyar NATO ta baiwa Turkiyya, kungiyar ta haifar ƙasar Turkiyya kuma kashe zunzurutun kuɗaɗe. A juyin mulki da aka gudanar a Turkiyya a shekarar 1960 da kuma gwamnatin da aka kafa sakamakon hakan lamari ne da ƙasashen NATO musamman Amurka ba zasu rasa ruwa da tsaki a kai ba. Tamkar dai yadda wata kungiyar Gladio ta ɓulla a ltaliya a sauran ƙasashen NATO ma basu tsira daga ire-iren hakan ba. Muna sane da kalaman shugaban ƙasar Amurka bayan juyin mulki a Turkiyya a shekarar 1980 inda ya furta cewa “yaranmu sun yi nasara” A baya bayan nan ma yunƙurin juyin mulkin da kungiyar FETO suka yi a ranar 15 ga watan Yuli da yawan masu nazari na bayyana cewar yunkurin nada nasaba da ƙasar Amurka.

 

Gudunmowar da Turkiyya ke baiwa kungiyar  NATO

 

Tun daga shekarar da aka kafa kungiyar kawo yanzu Turkiyya ta bayar da gudunmawar sojojin ta a duk lokacin da wata yaƙi ta ɓarke. Turkiyya ta rasa sojojin ta da dama musamman a lokacin yaƙin Koriya. Mijin gwaggo na ma na ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci yaƙin Koriya. A shekarar 2012 ma da jirgin NATO ya faɗo a Afghanistan mejon da ya hi shahada Şükrü Bagdatli abokina ne na ƙud da ƙud, a sabili da haka dukkanin su ina musu addu'ar samun rahamar Ubangiji.

 

Turkiyya takan yi tsaye tsayin daka a lokacin kai  gudunmawar NATO ga ƙasashen Musulmi domin ganin an gudanar da dukkanin matakan bisa ƙa'ida. Turkiyya takan ƙalubalanci kungiyar duk lokacin da ta yi yunkurin ɗaukar matakan mamaya a ƙasashen Musulmi. Da babu Turkiyya a cikin NATO da ire-iren waɗannan sharhin da zamu yi sun kasance masu ɗinbin yawa.

 

Shin ba za'a iya rabuwa da NATO bane? Ko kuwa NATO zata iya kasancewa ba tare da Turkiyya ba ?

 

ldan muka dubi ƙasashen dake kan gaba a ƙarni na 20 kamar su lngila, Faransa, Jamus, Amurka, Rasha da Daular Usmaniyya, a ƙarni na 21 sune ke kan gaba a fagen iko idan muka ƙara China da Turkiyya da Daular Uthmaniyya ta haifa.

Tarihi ya nuna cewa Turkiyya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ba'a yi wa mamaya, duk da dai a halin yanzu ta kasa ayyanar da abubuwan da suka rataya a wuyarta bata yi sakacin kare siffofin kare kanta ba. Turkiyya ita ce ƙasar Musulmi tilo da take mambar NATO. Turkiyya ta kasance a NATO bayan gayyatarta da shugaban ya yi da ƙasar Spain a akan wata yarjejeniya ta musamman.

Turkiyya a cikin kasashen NATO ba zata taɓa ayyanar da alaƙa kamar sauran ƙasashen yamma ba. Ba dai za'a iya kwatanta gudunmowar da Turkiyya ta baiwa kungiyar NATO da na wasu kasashe kamar Girka da Italiya ba. A fagen samar da lumana a fadin duniya Turkiyya ta taka rawar gani ƙwaran gaske da wasu ƙasashen yamma mambobin NATO ba yi ba, a sabili da haka ya zama wajibi kungiyar NATO, Rasha, yammaci, arewaci, kudanci, gabashi da dukkanin sassan duniya su ƙulla yarjejeniya mai inganci da Turkiyya. Domin basu da wata zaɓin da ya fiye musu Turkiyya ko a tsakaninsu.

 

Akwai wadanda ke sharhin cewa ba zai yiwu ga Turkiyya ta fice daga NATO ba, sabili da kungiyar na taimaka mata duk lokacin da Rasha ta nemi ta ƙalubalance ta a yankin. Suna kuma ikirarin cewa Turkiyya ta kasance cikin matsin lambar Rasha a lokacin da bata cikin kungiyar NATO. Wannan sharhin gaskiya ne, sai dai a lokutan da NATO take baiwa Turkiyya gudunmawa domin ƙalubalantar Rasha ba tana yi ne domin tallafawa Turkiyya ba, tana yi ne kawai domin ragewa Rasha ƙarfin iko a yankin domin idan Rashar ta ƙarfafa ƙalubale garesu zata koma. Abin nufi anan shi ne koda Turkiyya bata kasance mambar NATO ba dole NATO ta bata waɗannan gudunmowar. Misali lndiya ba mambar NATO ɓace amma sai gashi Amurka na bata gudunmowa fiye da ko wace mambobin NATO ba komai ba domin ƙalubalantar ƙarfafan ƙasar China a fadin duniya. A yadda duniya ke sauya wa a yanzu musamman yadda NATO ta fuskanci China da Rasha zata iya baiwa ko wace ƙasa gudunmowa domin ƙalubantarsu.

Haƙiƙa akwai bukatar Turkiyya ta ci gaba da kasancewa a matsayar mambar NATO, amma ba zata rungume hannu ta yi shiru ba a lokacin da Amurka da NATO ke ƙoƙarin sauya gabas ta tsakiya da kuma tallafawa ta'addanci.

ldan muka dubi ƙasashen Brazil, lndonisiya, lndiya, Malesiya, Pakistan da China dake taka leda a harkokin duniya a yau dukkanin su ba mambobin NATO bane. Ala kulli halin Turkiyya zata iya zaɓan kasancewar ta ko rashin kasancewa a cikin kungiyar NATO. Bari inda kammala wannan sharhin nawa na yau da kalaman lsmet lnonu. A shekarar q1964 ya ƙalubalanci wasiƙar da Johnson ya rubutawa Turkiyya inda yake cewa: A lokacin da  samar da sabuwar duniya, a lokacin ne Turkiyya zata nemi gurinta”

Duk da yake idan Turkiyya ta fice daga NATO zata rasa wasu dama zata ci gaba da ayyukan ta lamun lafiya, haka kuma idan NATO ta rasa Turkiyya ba abubuwa kaɗan zata rasa ba.

 

Wannan sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban tsangayar ilimin siyasa a jami'ar Ankara Yıldırım BeyazıtLabarai masu alaka