Yadda ake sarrafa kayan ciki a Turkiyya

A yau zamu yi maku bayani akan wani nau'in abincin da ake kira “sakatat” a ƙasar Turkiyya wanda mutane ke so ƙwaran gaske kuma suna yawan cinsa ta fannoni daban-daban

Yadda ake sarrafa kayan ciki a Turkiyya

Barkanmu da sake saduwa damu a cikin wani sabon shirinmu mai suna Abincin Turkiyya. A yau zamu yi maku bayani akan wani nau'in abincin da ake kira “sakatat” a ƙasar Turkiyya wanda mutane ke so ƙwaran gaske kuma suna yawan cinsa ta fannoni daban-daban. A ma'anar ƙamus, wannan nau'in abincin na nufin abubuwan da ake dafawa daga jikin dabbar da aka yanka amma banda tsoka. Abinda ake nufi anan dai shi ne kayan cikin dabban, wadanda suka haɗa har da ƙafafuwa, kai, hanji, huhu, hanta, ƙoda da tumbi. Duk da dai wannan nau'in abincin ya yi suna a ƙasar Turkiyya dama faɗin duniya, daga ƙarnin baya bayannan suna, kima da darajar wannan nau'in abincin ya ragu kwaran gaske. Haka ma a Turkiyya wannan nau'in abincin da ake yawan sarrafa wa a fadar gwamnati lokacin daular Usmaniyya da ma gidaje da dama a halin yanzu ba a ko wane gida ne zaka tarar dashi ba. Duk da haka a ƙasar Turkiyya akwai gidajen abincin dake da kwararrun dake sarrafa wannan nau'in abincin. Wadannan gidajen abincin na sarrafa romon kayan ciki iri daban-daban musamman wanda ake kira “işkembe” A wannan makon zamu yi maku bayani akan yadda ake sarrafa “işkembe çorbası” watau miyan kayan ciki a ƙasar Turkiyya.

    

Domin yin irin wannan miyan ana bukatar wadanan kayyayaki;

Kayayyaki :

  • Gram 500 na kayan cikin rago ko sa
  • Kofi 10 na ruwa
  • Cokali biyu ba garin fulawa
  • Cokali biyu na mai
  • Ƙwai ɗaya
  • Ruwan Lemon tsami na lemon ɗaya
  • Rabin kofi na Vinegar
  • Tafarnuwa 6-7
  • Garin tattasai
  •  Gishiri

 

Yanzu kuma sai yadda ake sarrafa wa; Da farko dai za'a wanke kayan cikin sosai sai a tafasa haɗe da gishiri da kofi 10-12 na ruwa har sai ya yi laushi. Za'a dinga kwashe kumfar dake tasowa, a lokacin da kumfar yabar tasowa za'a rufe tukunyar a ci gaba da dafawa har kimanin awa 1-1.5 lokacin da kayan cikin zai yi laushi. Za'a tsame kayan cikin a kuma yayyanke ƙanana-ƙanana da wuƙa. Daga nan kuma sai a ɗora wani tukunya saman wuta a  zuba mai Cokali biyu da garin fulawa Cokali biyu a soya na ƴan mintuna. Daga nan kuma sai a  ɗebi  ruwan kayan cikin a zuba a cikin tukunyar tare da ci gaba da motsawa. A yayinda ruwan ya tafasa sai a zuba yankakkun kayan cikin a ciki. Daga nan kuma sai a zuba ruwan ƙwai da ruwan lemon tsami a cikin ɗan sauran ruwan kayan cikin a motse sosai a kuma zuba cikin tukunyar. Bayan an dafa na kamar mintuna uku sai a kashe wutar a sauke tukunya. A halin yanzu dai miyan kayan ciki ya kammalu. Yanzu kuma sai a dake tafarnuwan ƙwara 6-7 a kuma garwaye da Vinegar kofi biyu. ldan kaga dama kana iya zubawa kai tsaye cikin miyan ko kuma sai bayan an raba a cikin kwano a zuba daga baya.

A more lafiya!

 

A cikin shirin mu mai suna Abincin Turkiyya a wannan makon mun bayyana muku yadda ake sarrafa “işkembe çorbası” watau miyan kayan ciki a Turkiyya. A makon gobe kuma zamu zo muku da wani nau'in abincin Turkiyya mai daɗi.

Ku huta lafiya.

 

 Labarai masu alaka