Tsohon garin Catalhoyuk mai dubunnan shekaru dake Turkiyya

Tsohon garin Catalhoyuk mai dubunnan shekaru dake Turkiyya.

Tsohon garin Catalhoyuk mai dubunnan shekaru dake Turkiyya

A Turkiyya akwai garuruwa da dama wadanda mallaki ne na mutanen dauri....Dandalin Çatalhöyük na zamanin Jahiliyya na Neolithic na daya daga cikin wadannan wuraren na tarihin.

Tarihi ya nuna cewa Çatalhöyük, matattara ce ta dubban alamomi marasa misaltuwa da ke bada shaida kan kyaukyawar zamantekawar al'umomi da kuma cudanyar al'adu a wannan yankin, shekaru dubu 9 da 500 da suka gabata.Çatalhöyük wani babban sansani ne wanda babu kamar sa,mai cike makil da kayayyakin tarihi kan noma,rayuwa da kuma al'umomin wannan yankin...

An yi amanna cewa,Çatalhöyük da ke a tazarar kilomita 11 daga gundumar Çumra na jihar Konyan tsakiyar yankin Anatoliyan kasar Turkiyya,na a jerin wuraren da mutanen zamaninnikan farko suka rayu,kuma duba da kayayyakin tarihin da aka tono a wannan yankin,ana hasashen yawan al'umar Çatalhöyük ya haura mutum dubu 8.

Sunan wannan Çatalhöyük, wanda ya kasance a jerin tsaffin yankunan zamanin jahiliyya na Neolithic 'yan kalilan wadanda basu ruguje ba, ya fito ne daga kananan tuddan da ke a gabashi da kuma yammancin garin.Sabili da dukannin wadannan fasalolin na Çatalhöyük ne, tun a shekarar 2012 ya zuwa yanzu,Hukumar raya al'adu da kuma ilimi na Majalisar Dinkin Duniya ya saka sunan wannan garin a jerin muhimman wuraren tarihi na duniya.

Tuddan na Çatalhöyük, hawa-hawa ce na tarin ruguzazzun kayayyakin da suka samo asali daga girgizar kasa da kuma yake-yake.Shi yasa suka kasance wasu muhimman taskoki da ke kunshe da kayayyaki masu dumbin yawa na zamaninnika mabambata na tarihin mutanen farko.

Tuddan na Çatalhöyük na a wurare biyu mabambanta da ke a gabashi da kuma yammacin garin...A tone-tonen da aka gudanar a tudun Gabas an yi nasarar gano hawa 18 na muhallan mutanen zamanin jahiliyyar Neolithic.Wadannan hawa-hawan wadanda ake hasashen cewa an samar da su a shekaru 7000 da suka gabata,sun kasance wani babban rumbun sani da ke kunshe da muhimmin sani da kayayyaki masu yawan gaske dangane da tarihin gine-gine da aiyukan hannun mutanen da.

A tudun yamma kuma,an sanar da cewa, shekarunsa 6000 duba da kalandar miladiyya haihuwar Annabi Issa (As) kana,wadanda yayi daidai da zamanin bullowar addinin Kiristanci shiyyar Katolika.Duniya ta shaida cewa,wannan tudun yamma cigaba ne na gine-ginen al'adun na gabas...

A tsawon shekaru 2000,an yi amfani da wannan tuddan wadanda ke a wani fili mai fadin eka 14,a matsayin wuraren rayuwa na jama'a.

Girman garuruwa da kuma tsarin muhallan Çatalhöyük, wani babban misali ne na kwarewa da kuma gaggarumin cigaban da ake da shi a wancan zamanin a fannin fasahar tsara birane,duba da  tunace-tunacen adalci da bukatun al'uma.Mafiya bayanannun fasalolin wadannan gidajen su ne,kasancewa girmansu daya kana ana shiga cikinsu ta hanyar amfani da wata matattakalar da ke kallon rufin kowane daga cikinsu.Dukannin gidajen na kallon juna,kuma suna a fili daya.

 

An yi hasashen cewa,musababbin kasancewar gidajen a irin wannan yanayin shi ne,karfaffiyar alakar da ke tsakanin 'yan gida daya da kuma fifita rayuwar bai-daya da mutanen wancan zamanin suka yi.

A katangun gidajen an yi zane-zane kala daban-daban,wadanda suka hada da furenni,labaran farauta,raye-raye,fenti,taurari,berawu da kuma tumaka.

Da yake gidajen da ke garin zamanin jahiliyya na Neolithic na Çatalhöyük na jere daya bayan daya,babu titi ko daya tak.Ana amfani da rufin muhallai a matsayin tituna,shi yasa ake bi ta kan gidaje,a duk lokacin da aka bukaci zuwa daga wannan  sashe ya zuwa wancan.

Sakamakon tone-tonen da aka gudanar a yankin sun nuna cewa,mutane da suka fara rayuwa a Çatalhöyük maharba ne kana masutan 'ya 'yan itace a dokar daji.Kazalika,an gano cewa daga bisani sun fara noma da kuma kiwata shanu da tumaki a gidajensu.

A tone-tonen tudun gabas,an yi kacibus da kananan gumaka na abar bauta "Babbar Uwa", ko kuma "Mother Godness" a Turance.Gumakan wadanda aka sassaka su ta hanyar amfani da gasasshiyar laka,farfasassun duwatsu  da alli,na tsawon santimita 5 zuwa 15.

A yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da tone-tonen gano kayayyakin tarihi a garin Çatalhöyük.Labarai masu alaka