Masallacin Divrigi Ulu mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Tare da kyawawan gine-gine da kuma katangunsu da aka kawata da kayatattun zane-zane da kuma da duwatsu, Masallacin Divriği Ulu da cibiyarta ta kiwon lafiya,wato Darüşşifa ,sun kasance a jerin muhallai mafiya muhimmanci na yankin Anatoliyan kasar Turkiyya.

Masallacin Divrigi Ulu mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Wadannan gine-ginen wanda aka samar da su a kusan 775 da suka shude,na kunshe ne da masallaci da kuma asibiti...Hukumar raya al'adu da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta saka sunayen wadannan gine-ginen a jerin muhammin wuraren tarihi na duniya.

Babban masallaci da kuma cibiyar kiwon lafiya ta Darüşşifa wadanda ke a gundumar Divriği ta jihar Sivas  da ke a tsakiyar yankin Anatoliyan kasar Turkiyya,a gina su ne a zamanin masarautar Mengücekoğulları  wacce a karkashin mulkin daular Turkawan Seljukawa.An masallacin a gina shi tsakiyar karni na 13 miladiya karkashin umarnin sarkin masarautar Mengücekoğulları,Ahmed Şah,cibiyar kiwon lafiya kuma,an gina ta a wannan zamanin karkashin umarnin sarauniya Turan Melek.Babban magini Ahlatlı Hürrem Şah ne ya jagoranci wadannan gine-ginen. Muhimman safalolin masallacin Divriği da kuma cibiyar Darrüşşifa wandada ke da matsayi na musamman a tarihin gine-ginen yankin Anatoliyan Turkiyya a karni na 13 su ne,zane-zanen da aka kawata kofofi da kuma katangun wadannan wuraren na tarihi...Yadda ba a maimaita dubban zane-zanen da ka yi a mafiya kyawawan misalan aikace-aikacen duwatsun wadannan katangun,na a jerin ababen da ke kara daukar hankali.

Masallacin mai kubbobi biyu,na rufe ga baki daya da yankakkun duwatsu an da aka tsara duba madaidaicin tazara daga tsakiyar wurin ibadar.Masallacin na da kofofi uku.A kofar farko wacce ake kira da "Kofar Aljanna" akwai zane-zanen furenni da na fulawowi. 

A kofar yamma,akwai zane-zanen da ke kama da dinke-dinke.A wannan kofar wacce kazalika ke dauke da zane-zanen furennin Tulip,akwai tambarin daular Turkawan Seljuk,mikiya mai kai biyu da kuma tambarin masarautar Mengücek durkusasshiyar tsuntsuwa.

A kofar gabas,wato kafo ta uku kuma,akwai gambun da ake kyautata zaton an yi amfani da shi a masallacin Shah.Shi yasa a ke kiran wannan kofar da "kofar Shah".

Ya zuwa yanzu, masallacin na ci gaba da jan hankali sakamakon katakon Ebony,ice mafi tsawon rai a duk fadin duniya da aka yi amfani da shi wajen sarrafa munbarin wurin ibadar.

A Masallacin akwai wasu akwatina biyu da ke kunshe da amanonin mutanen dauri, wadanda aka samar da su ta hanyar sarrafa wani dutse daya tak.A wadannan akwatinan,jama'a na ajje muhimman kayayyaki da kuma jauharansu, a duk lokacin da suka kuduri zuwa wani wuri.Kazalika an sassaka akwatin dutse na biyu da ke a tsakiyar wannan masallacin da zummar ajje sadaka da kyaututtukan da yakamata a bai wa mabukata, masu karamin karfi da marasa gata.

Cibiyar kiwon lafiya ta  Darüşşifas ta gundumar Divriği na a jerin asibitoci mafiya tsufa na yankin Anatoliya da mu tarar a zamaninmu na yau.

A wancan zamanin,an gina wannan cibiyar kiwon lafiyar da zummar magance cututtukan da suka danganci gangar jiki da kuma ruhin bil adama.A lokacin daular Musulunci ta Usmaniyya kuma,asibitin ya ci gaba da aiki,inda aka kuma yi amfani da shi a matsayin makaranta.

Idan kun ziyarci yankin Sivas da nufin kashe kwarkwatan idanu a masallacin Divirği da kuma cibiyar kiwon lafiya ta Darüşşifa,kar ku sake ku koma gida ba tare kun yada zagaya a muhallan tarihi,makaratun islamiyya da kuma hasumiyoyin wannan yankin gami da yin nutso a karkashin kankarar koramar Tödürge.Kazalika ku dandana dadadan girke-girken yankin,wadanda suka hada da gurasa,dunkulallen shinkafa a ganyen inibi (Yaprak sarması) da kayna kwalam  da makulashen na Yufka.Labarai masu alaka