Zaben 2019: Ko Turkiyya ta kasance mai mulkin kama-karya?

An gudanar da zaɓuƙan magajen gari dana ƙananan hukumomi da aka fara a shekarar 1840 karo na 19 a ranar 31 ga watan Maris 2019 a faɗin ƙasar Turkiyya.

Zaben 2019: Ko Turkiyya ta kasance mai mulkin kama-karya?

An gudanar da zaɓuƙan magajen gari dana ƙananan hukumomi da aka fara a shekarar 1840 karo na 19 a ranar 31 ga watan Maris 2019 a faɗin ƙasar Turkiyya. Jam'iyyun da suka yi haɗin gwiwa karkashin Haɗaƙar Jamhuriyar sun samu kaso 51.6 cikin ɗarin kuri'un da aka jefa. Jam'iyyun da suka yi haɗin gwiwa karkashin Haɗaƙar Ƙasa kuwa sun samu kaso 37.5 cikin ɗari. ldan muka kwatanta da kuri'un da jam'iyyu suka samu a zaɓuƙan shekarar 2014; jam'iyyar adalci da  cigaba watau Ak parti ta samu kaso 43.1 cikin ɗari a shekarar 2014 a wannan shekarar kuwa ta samu kaso 44.3 cikin ɗari sai dai yawan magajen garin da ta samu a shekarar 2014 sun ragu daga 48 zuwa 39. lta kuwa jam'iyyar CHP yawan kuri'un da ta samu sun ƙaru daga kaso 26.6 zuwa 30.1 cikin ɗari haka kuma yawan magajen garin da ta samu sun ƙaru daga 14 zuwa 21. Jam'iyyar MHP kuwa yawan kuri'un data samu a shekarar 2014 sun ragu ne daga kaso 17.8 zuwa kaso 7.3 cikin ɗari sai dai yawan magajen garin da ta samu sun ƙaru daga 8 zuwa 11. Sai kuma jam'iyyar HDP wacce a dukkanin zaɓukan biyu ta samu kaso 4.2 cikin ɗari amma yawan magajen garin da ta samu a shekarar 2014 sun ragu a zaɓen bana.

 

Mun sake kasancewa tare da ferfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar ilimin siyasa dake jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt.

 

Abin tambaya anan shi ne, menene sakamakon wannan zaɓen ke koyarwa? A wannan ƙasidar nawa ina son inyi sharhi akan ma'anar wannan sakamakon zaben magajen gari dana ƙananan hukumomin Turkiyya akan ƙasar dama a duniya baki daya.

 

Waɗanda suka fi faɗuwa a zaɓen sune masu ikirarin “Turkiyya ƙasar mulkin kama karya ce”

 

Duk da dai wannan zaɓen na ƙananan hukumomi ne kafafen yaɗa labaran ƙasashen duniya sun haska zaɓen ƙwaran gaske. Babban dalilin da ya haifar da hakan shi ne kasancewar canjin mulkin da aka samu a manyan biranen ƙasar da suka haɗa da lzmir da babban birnin ƙasar Ankara. Duk da dai wadanda ke kirar kasar Turkiyya mai mulkin kama karya lamarin ya faru yadda suka so, sun sha mamaki akan yadda zaɓen ya kasance duk da sauyin da aka samu a manyan biranen kasar. Ƙasashen yamma da kafafen yaɗa labaransu dake yi wa Turkiyya wacce ta kwashe shekaru 180 tana gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi wani kallo na daban sun tilastu da fahimtar yadda sakamakon zaben ya kasance. Sakamakon zaben na nuni da wadanda ke yiwa Turkiyya farfaganda ta ƙarya karensu ya sake kama zaki, bugu da ƙari wadanda dai suka fi faɗuwa a wannan zaben sune masu sukar shugaba Recep Tayyip Erdoğan da yana mulkin kama karya.

Shin ko a wata ƙasar akwai jam'iyyar komunist a halin yanzu, in akwai ko tana iya cin zaɓe? Wannan tambaya ce da ban san amsarta ba. A wannan zaɓen Jam'iyyar Kwaminis ta Turkiyya (TKP) ta lashe zabe a garin Tunceli. Hakan ya faru duk da ƙalubalen da kungiyar ta'addar PKK ke yi da kuma matsin lambar jam'iyyar HDP. Wannan bai kasance hasashen karya da suke wa Turkiyya ba, ɗaya ne dai daga cikin hujjojin kyakkyawar demokradiyyar ƙasar.

 

Jam'iyyar AK Parti: Nasara da gargaɗi

Jam'iyyar AK Parti da ta samu kuri'u kashi 44.3 cikin ɗari wannan ne dai karo na 15 tana lashe zaɓukan ƙasar tun lokacin da aka kafa ta. Jam'iyyar Akan parti da ta kasance akan karagar mulki tun da aka kafata a shekarar 2002 a zaɓen bana ta samu ƙarin yawan kuri'u da kaso ɗaya cikin ɗari duk da matsalolin tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta, wannan na nuni ga ƙara samun nasara ga Jam'iyyar. ldan aka kwatanta da kuri'un da ta samu a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 24 ga watan Yuni shekarar 2018 inda ta samu kaso 52.3 ƙarƙashin haɗakar jamhuriyar za'a ga cewa ta rasa yawan kuri'u kaso 0.7 cikin ɗari ne kachal. Sai dai a zaben banan duk da yawan kuri'un da take samu sun ƙaru jam'iyyar ta rasa shugabancin manyan biranen ƙasar. A jawabin da shugaban ƙasa Erdoğan ya yi za'a koyi darasi akan dalilan da suka haifar da hakan kuma za'a ɗauki matakan da suka dace.

 

Yaɗuwar Jam'iyyar CHP a Turkiyya

Babban jam'iyyar adawa watau CHP ta samu ƙarin yawan kuri'u idan aka kwatanta da zaɓukan da aka gudanar a baya. Sai dai yawan kuri'un data samu kaso 30.6 cikin ɗari a lokacin zaben shugaban kasar da ta tsaida Muharrem İnce sun ragu. Jam'iyyar CHP na kallon wannan zaɓe a matsayin nasara ne kasancewar yawan kuri'un da take samu a manyan biranen ƙasar sun ƙaru.

 

Duk da yawan kuri'un data samu a manyan biranen ƙasar da suka haɗa da Ankara, lstanbul da Antalya idan muka dubi mafi yawancin yan takarar da ta tsaida mutane da basa bin ainihin ra'ayoyin jam'iyyar. ldan muka dubi ainihin aƙidar Jam'iyyar CHP zamu iya tunawa da ƴaƴan Jam'iyyar da suka ƙalubalanci shugaba Erdoğan a lokacin da ya karanta Suratul Fatiha bayan kammala zaɓen shekarar 1994. Amma a zaɓen bana sai gashi munyi karo da ɗan takarar wannan jam'iyyar na magajin garin lstanbul watau Ekrem İmamoğlu yana ta karanta Suratul Yasin a lokacin yaƙin neman zaɓe. Samun ya'yan jam'iyyar CHP masu mutunta al'adun Turkiyya na nufin ci gaban ƙasar baki daya. A kasidar dana rubuta kwanakin baya nayi nuni da ana bukatar wadanda zasu yi haddin kai da aiki bisa akida ɗaya saɓanin tarzoma da matsin lamba domin cimma manufar tsarin shugaban ƙasar da aka kafa a kasar.

 

Dük da sun zaɓi HDP manufarsu ba “Kürdistan” ba amma Kurdawa masu jefa kuri'a.

A duk lokutan zaɓuka a ƙasar jam'iyyar HDP kan yi amfani da kalaman raba kawona a ƙasar. A gabashin ƙasar takan yi ikirarin cewa al'umma su jefa mata kuri'a domin tabbatar da Kurdistan. A zaɓen bana dai Jam'iyyar HDP ta rasa magajen gari hudu a yankunan da ta saba cin zaɓe. A inda ta rasa garuruwan Şırnak, Ağrı da Bitlis ga Jam'iyyar Ak parti ta kuma rasa garin Tunceli ga jam'iyyar TKP. Hakan dai na nuni da Ƙurdawan gabashi da kudu maso gabashin kasar Turkiyya suna goyon bayan kasancewar Turkiyya tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Haka kuma wannan zaɓen na nuni da Ƙurdawan kasar sun yi a'manna da haɗakar da jam'iyyun Ak parti da MHP suka yi da kuma ayyukan da suke gudanar wa a fadin ƙasar.

 

Shin ko raguwar fita zaɓe nada nasaba da rashin alamar wasu jam'iyyu akan  kuri'a?

 

ldan muka kwatanta yawan fita zaɓe da wasu ƙasashen dake demokradiyya zamu ga cewa a Turkiyya ana fita zaɓe ƙwaran gaske. A wannan zaben ƙananan hukumomi da aka gudanar kaso 84 cikin ɗari ne suka fita suka jefa kuri'unsu. Sai dai idan kuma muka kwatanta da zaɓukan ƙananan hukumomi da aka gudanar a baya zamu ga cewa an samu raguwar fita zaɓe da kaso kashi 5 cikin ɗari domin a waccan lokacin kaso 89 cikin ɗari ne aka samu. Wannan raguwar fita zaɓen da aka samu bai da alaƙa a alamun jam'iyyun sai dai haɗakar da jam'iyyun suka yi da juna ka iya zama dalili. Mutanen da sun kwashe shekaru fiye da goma suna baiwa Jam'iyyar da suke ra'ayi kuri'a a wannan karon sun tilastu da su zaɓi wata jam'iyya daban wacce ba nasu ba. Sabili da haka ya zama wajibi a zaɓukan gaba a yi wannan haɗakar ta yarda ko wacce jam'iyya zata kasance a kuri'a.

Wani abu kuma da zamu duba game da wannan zaɓen shi ne yadda jam'iyyar MHP duk da  yawan kuri'un da ta samu ya ragu daga kaso 17.8 cikin ɗari a shekarar 2014 zuwa kaso 7.3 a bana yawan magajen garin da ta samu sun ƙaru daga 8 zuwa 11. A yayinda Jam'iyyar Good Party watau iyi parti bata samu kujera ko kwara ɗaya ba jam'iyyar Saadet parti yawan kuri'un data samu a zaɓen da kaso 2.7 cikin ɗari bai canja ba a bana.

Da ƙarshe dai, a duk lokacin da aka jefa kuri'a a ƙasa hakan na nufin bunƙasar demokradiyyar ƙasar. ldan dai muka dubi sakamakon zaben da idon basira zamu ga cewa zaɓe dake nuni ga ci gaban ƙasar Turkiyya baki ɗaya.

 

Wannan sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban tsangayar ilimin siyasa a jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt.Labarai masu alaka