Alfanon da tallafin karatun Turkiyya ya kunsa

A wannan makon zamu yi muku bayani akan alfanon da tsarin tallafin karatun Turkiyya ya kunsa da kuma ire-iren tsarukan da Hukumar YTB take gudanar da ayyukanta akai.

Alfanon da tallafin karatun Turkiyya ya kunsa

Idan baku manta ba, a mokon jiya mun zayyana muku daga cikin wasu ayyukan da Hukumar Tallafin Karutu ta kasar Turkiyya watau Hukumar YTB ke gudanarwa. A wannan makon zamu yi muku bayani akan alfanon da tsarin tallafin karatun Turkiyya ya kunsa da kuma ire-iren tsarukan da Hukumar YTB take gudanar da ayyukanta akai.

ALFANON DA TALLAFIN KARATUN TURKIYYA YA KUNSA

 Shin ko wasu irin alfano ne tallafin karatun Turkiyya ya kunsa ?

  1. Kudin kashi duk wata:

 

 • Masu karatun digiri na farko: Lirar Turkiyya 700 duk wata

 • Masu karatun diriği na biyu (Mastas): Lirar Turkiyya 950 duk wata

 • Masu karatun digirgir : Lirar Turkiyya 1400 duk wata

 

 • Masu bincike a fannoni daban-daban*: Lirar Turkiyya 3000 duk wata

 • Masu koyon yaren Turkanci a lokacin bazara**: Lirar Turkiyya 500 duk wata

 • Ma’aikata da malamai masu koyon yaren Turkanci domin sadarwa***: Lirar Turkiyya 2000 duk wata

 

* Tallafin ga wadanda ke gudanar da bincike ya kushi kudin kashi na duk wata ne kachal

** Tallafin koyon yaren Turkanci a lokacin bazara kuwa ya kushi kudin kashi duk wata, gurin zama, ishora ta lafiya da ayyukan raya al’adu da gargajiya.

*** Tallafi ga ma’aikata da malamai masu koyon yaren Turkanci domin sadarwa kuwa ya kushi kudin kashi duk wata, gurin zama, kudaden sufuri da kuma lamurkan raya al’adu da gargajiya.

Ga masu karatun digiri na farko, na biyu da digirgir kuwa, baya ga kudaden kashi duk wata ana kuma daukar musu wadannan nauyin:

2. Kudin makaranta

3. Tiketin jirgin zuwa Turkiyya da kuma na komawa bayan kammala karatu

4. Ishorar lafiya

5. Guraren zama

6. Koyon yaren Turknci na shekara daya

 

Iya lokuttan da tallafin zai dauka;

• Masu karatun digiri na farko: Shekara daya na koyon Turkanci da shekaru 4-6 (Ya danganta da iyakacin yawan shekarun da digirin ke dauka)

• Masu karatun digiri na biyu: shekara daya na koyon Turkanci da shekaru  2 na karatun kwas din

 • Masu karatun digirgir : shekara daya na koyon Turkanci da shekaru 4 na karatun kwas

  • Masu gudanar da bincike: Watanni 3-12

• Shirin koyon Turkanci lokacin bazara: Watanni 2

       • Shirin koyar da ma’aikata da malamai yaren Turkanci: Watanni 8-10

 

TALLAFIN MASU KARATUN DIGIRI NA FARKO

Wannan fanni ne na musanman  da aka tsarawa masu neman karutun digiri na farko. Kwasa-kwasan da zasu karanta sun hada tun daga fannonin fasaha zuwa fannonin lafiya da kuma fannonin sanin halayen rayuwan dan adam zuwa harkokin yau da kullun. Za’a iya ganin jami’o’i da kwasa-kwasan da dalibi zai iya zaba a shafin yanar gizo na Hukumar YTB. https://www.turkiyeburslari.gov.tr/

 

TALLAFIN KARATU A RUKUNAN GABA DA DIGIRI

Wannan rukunin ya kunshi tallafin karatun digiri na biyu da digirgir a fannonin kimiya da fasaha, lafiya, karatun halayen dan adam da kuma tattalin arziki a jami’o’in kasar Turkiyya. Za’a iya samun cikekken bayani game da jami’o’i da kwasa-kwasan da ake dasu a shafin Hukumar YTB ta yanar gizo kamar haka: https://www.turkiyeburslari.gov.tr/

A makon gobe muna fatan kawo muku bayanai game da wani daga cikin Hukumomin Cigaban kasar Turkiyya.

Ku huta lafiya.Labarai masu alaka