Tarrantizm: Sabuwar bakar akida a kasashen yamma

Bayan harin ta'addancin da mai ra'ayin nuna wariyar launin fata da nuna fifikon farar fata ɗan ƙasar Ostraliya mai suna Breton Tarrant ya kai a Niyuzelan da yayi sanadiyar rayukan Musulmi 50 ya sanya ta'addanci ɗaukar  wani sabon salon

Tarrantizm: Sabuwar bakar akida a kasashen yamma

Bayan harin ta'addancin da mai ra'ayin nuna wariyar launin fata da nuna fifikon farar fata ɗan ƙasar Ostraliya mai suna Breton Tarrant ya kai a Niyuzelan da yayi sanadiyar rayukan Musulmi 50 ya sanya ta'addanci ɗaukar  wani sabon salon amfani da ra'ayin wariyar launin fata da tsattsaurar ra'ayi. Ala külli halin, wannan sabon salon bai kasance ba face ƙyamar baƙi, lslama da bakar fata.

 

Mun sake kasancewa tare da ferfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar ilimin siyasa dake jami'ar Ankara Yıldırım Beyazıt.

 

Ƙyamar Yahudawa, Ƙyamar lslama

A ƙarni na ashirin a ƙasashen yamma an raɗawa ra'ayin ƙalubalantar yahudawa da suna “ƙyamar yahudu”. Haka kuma an sanya dukkanin yunƙurin nunawa musulmi banbanci da ƙalubalantar musulmi sunan “ƙyamar lslama”. Ayyukan ƙalubalantar da ƙyamar lslama basu kasance ba face abubuwan da suke jefa musulmi da sauran ma dukkan al'uma cikin halin ƙaƙanikayi. Wannan dai lamari ne dake da alaƙa da tunani da kuma ayyukan wasu tsiraru a doron ƙasa.

Wadannan munanan matakan basu kasance ƙalubale ga Musulmi kawai ba, har ma ga sauran al'ummar yamma da ba ƴan ra'ayin fifita farar fata bane. Bugu da ƙari hakan kuma zai kasance babbar matsala ga wadanda basa da ra'ayin nuna fifikon farar fata a wajen nahiyar Turai da ma a fadin duniya baki ɗaya.

 

Ra'ayoyin Facism, Nazi da Zionism

Wadannan dai ba sabbin ra'ayoyi bane da za'a ce ba'a san dasu ba. Babbar aƙidar wadannan kalmomin dai shi ne nuna wariya. Amma a halin da muke gani a yanzu wadannan miyagun ra'ayoyin sun wuce na wariyar launin fata kawai, domin masu ra'ayin nuna fifikon farar fata na ƙalubalantar har masu launi irin nasu ta ƙone musu gidaje, kashe su da kuma kai musu hare-haren ta'addanci iri daban-daban a nahiyar Turai. ldan muka dubi yadda masana suka bayyana a cikin littatafan su zamu ga cewa sun bayar da ma'anar ra'ayin Facism a matsayin ra'ayoyi dake nuna kyamar hukumomi da gwamnatin ƙasa. Ra'ayin Nazi kuwa sun bayyana shi ne a matsayin nuna fifikon da al'umman ƙasar Jamus sun ke yi wa kansu fiye da sauran ƙasashen duniya. Shi kuwa Zionism ra'ayoyi ne dake nuna wariyar ƙasa da kuma addini. Ra'ayin Zionism dai kamar yadda masani Thedore Herlz ya bayyana: ra'ayi ne dake goyon bayan yadda Yahudawa zasu kwache wasu yankuna da suka haɗa har da wasu yankunan kasar Turkiyya da ake kira Mevud domin kafa kataɓariyar ƙasar Yahudu a doron ƙasa. Shi kuwa Roger Garaudy ya bayyana Zionism ne a matsayin ra'ayin nuna wariyar launin fata da kuma yunƙurin mulkin mallaka. lre-iren waɗannan ra'ayoyin lsra'ila; da yawan masana, ganin irin cin zarafin da suke yi wa Falasɗinu ya sanya sun yi tir dasu. Kafa kataɓariyar ƙasar Yahudu bai kasance ba face nuna wariyar addini musamman ganin yadda akwai ƴan ƙasar lsra'ila mabiya addinin Orthodox da ƙasar bata mutuntawa.

 

Nuna fifikon farar fata watau Whiteizm?, Wasizm?, Tarrantizm?

Duk da dai mun fassara Facism a matsayin ra'ayin ƙyamar hukuma, Nazi ra'ayin nuna fifikon ƙasa da wariyar launin fata, Zionism kuma a matsayin ra'ayin ƙyamar wasu addini da nuna wariyar launin fata, bai kamata mu fassara ra'ayin nuna fifikon farar fata (White Supremacy) a matsayin ra'ayin da ake amfani da salon ta'addanci wajen kyamar wadanda ba fararen fata ba. Musamman ganin yadda ra'ayin nuna fifikon farar fatan ya canja zuwa ga lamurkan ta'addanci. Duk da dai bamu aminta akan cikakkiyar ma'anar da zamu bayyana wannan mugun tabi'ar ba, mun san ainihin tushen sa. Ganin yadda masu bin ra'ayin ke amfani da salon ta'addanci a harkokin su ya sanya ganin cewa ra'ayin nuna fifikon farar fata na kira ne ga masu ra'ayoyin Facism, Nazi da Zionism domin faɗaɗa wannan bakar kalmar ta Whiteizm. A halin yanzu dai, kalmar an ta'allaka ta da kalmomin ƙalubalanta, ta'addanci, nuna ƙyama da cin zarafi. Amma kamar yadda muka yi sharhi a makon jiya, bai kamata mu fassara ra'ayin akan haka ba, domin hakan zai kasance tamkar wata kashin kaji ga dukkan ilahirin fararen fata a doron kasa, haka kuma amfani da kalmar ta'addancin kiristoci domin ayyukan ta'addancin wani mai bin addinin Kirista, ko kuma amfani da kalmar ta'addancin musulunci domin ayyukan wani ko wasu masu bin addinin Musulunci bai dace ba kuma yin hakan ba'a yi wa addinan adalci ba. Yin hakan zai ƙara ƙarfin gwiwar ƴan ta'adda a doron ƙasa. Sabili da haka, ya kamata mu guje wa amfani da kalmar ta'addancin Whiteizm domin ayyukan ta'addancin da wani mai bin ra'ayin nuna fifikon farar fata ya yi, yin hakan ƙalubalantar dukkanin farar fata ce  a doron ƙasa.

 

ldan dai har muka fayyace Jamusawa daga masu ra'ayin Nazi acikinsu, muka kuma babbanta Yahudawa daga masu ra'ayin Zionism daga cikin su, toh ya zama wajibi mu ɗora kalmar Whiteizm bisa irin wannan ma'aunin, mu banbance zare da abawa.

ldan muka dubi ƙasidar da wanda ya kai harin Niyuzelan ya rubuta zamu iya fassara kalmar Whiteizm a matsayin Tarrantizm. Wannan ra'ayi na Tarrantizm bai shafi dukkan fararen fata ba. Domin a ƙasidar da ya rubuta ya yi nuni ga amfani da hanyar ta'addanci domin tabbatar da muguwar ra'ayin nasa.

A ƙarshe dai, kalmar nuna fifikon farar fata ta amfani da hanyar ta'addanci domin take hakkokin bil'adama da sauran hakkokin su sabuwar kalma ce a gare mu. Ko dai wace kalma za'a yi amfani da ita wajen bayyana ire-iren waɗannan miyagun ɗabi'u ya zama wajibi mu fayyace tare da banbance wanda ko wadanda suka aikata laifuka daga wadanda babu hannun su a ciki ko da ko mabiya tafarki ɗaya ne. Bi ma'ana; ko da zamu danganta ra'ayoyin Nazi, Facism, Zionism da Whiteizm bai kamata mu ta'allaka ra'ayi da laifukan nuna fifikon farar fata ga dukkanin fararen fata dake doron ƙasa ba.

 

Wannan sharhin ferfesa Kudret BÜLBÜL ne shugaban tsangayar ilimin siyasa a jami'ar dake nan babban birnin ƙasar Turkiyya watau Ankara Yıldırım Beyazıt.

 Labarai masu alaka