Ka'idojin zaben dalibai domin tallafin karatun Turkiyya

A yau zamu bayyana muku ire-iren tsarukan da ɗaliban dake neman nasarar samun tallafin karatu a Turkiyya zasu bi; da kuma ƙâidojin da ake bi domin zaɓan ɗaliban a ko wacce shekara.

Ka'idojin zaben dalibai domin tallafin karatun Turkiyya

Barkanmu da sake saduwa damu a cikin shirin mu mai suna Hukumomin Ci Gaban Turkiyya. A wannan makon ma zamu ci gaba da bayani akan ayyukan hukumar bayar da tallafin karatu ta ƙasar Turkiyya watau YTB. A yau zamu bayyana muku ire-iren tsarukan da ɗaliban dake neman nasarar samun tallafin karatu a Turkiyya zasu bi; da kuma ƙâidojin da ake bi domin zaɓan ɗaliban a ko wacce shekara.

YADDA AKE ZAƁEN ƊALlBAN

A lokacin da ake zaɓen wadanda suka cancanci samun tallafin karatun; baya ga nasarorin jarabawowi a makarantu ana kuma yin la'akari da ayyukan hidima ga al'umma da kuma wasu nasarorin da ɗalibi ya samu a rayuwarsu.

 

  1. MATAKlN FARKO:

A matakin farkon zaɓen ɗaliban da suka cancanci samun tallafin; ana duba yawan makin ɗalibai a makarantu, shekaru da kuma duba yawan makin waɗansu takardun da ake buƙata.

 

  1. TATTANCEWAR ƘARSHE:

Masanan kan fitar da sunayen da suka dace domin gayyatarsu intabiyu. Ana dai zaɓen daliban ne dangane da makin jarabawar su, jami'o'i da kwasa-kwasan da suka zaɓa, rubuce-rubucen da ɗalibi ya yi, irin aikin da suke da niyyar yi, ƙasidar da suka gabatar da sauransu..

 

3. lNTABlYU: Masana kan gudanar da intabiyu ga ɗaliban da aka zaɓa daga ƙasashe fiye da 100.

 

4. ZAƁEN ƊALlBAN DA SUKA Yl NASARA:

Kwamitin intabiyu ce keda alhakin bayyana waɗanda suka yi nasarar samun tallafin karatun bayan sun kammala dukkan tattancewa daga dukkan ɗaliban da suka miƙa takardunsu.

 

ƘAlDOJlN ZAƁEN ƊALlBAN DA SUKA Yl NASARA:

Akan dai gayyaci ɗaliban da suka cancanta daga cikin waɗanda suka miƙa takardunsu domin halartar intabiyu a ƙasashen su. A wasu lokutan kuma, ta kan ɗauro a gudanar da intabiyu ɗin ta yanar gizo ko ta wayar tarho. Kwamitin intabiyu a ko wacce ƙasa ta kan kunshi wakilin hukumar YTB da kuma Malami ɗaya daga cikin jami'o'in ƙasar Turkiyya.

lntabiyun da ake gudanarwa cikin mintuna 15-30 yakan kasance kamar haka:

  1. Sallama da gaisawa
  2. Duba takardun ɗalibi
  3. Tambayar ɗalibi dalilan da suka sanya shi neman tallafin karatun
  4. Tambayar ɗalibi game da nasarorinsa a fagen karatu da kuma irin aikin da yake da niyyar yi bayan kammala karatu
  5. Rufewa da kuma yin tambaya daga ɗalibi zuwa ga kwamiti.

 

 

 

 

 Labarai masu alaka