Garin Diyarbakir mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Diyabakır, gari ne da ke a kudu masu gabashin yankin Anatoliyan kasar Turkiyya.

Garin Diyarbakir mai dimbin tarihi dake Turkiyya

Diyabakır, gari ne da ke a kudu masu gabashin yankin Anatoliyan kasar Turkiyya.

Sabili da yanayin inda ya kasance, garin ya zama magamar al'adu da kuma kabilun daulolin marasa adadi wadanda suka gushe shekaru aru-aru da suka gabata.Shi yasa a yau ma, riskar alamomin dukannin wadannan daulolin a tituna,masallatai,cocina,gadoji da hanyoyin Diyarbakır,abu ne mai saukin gaske.Kawo yanzu tarihi mai gushe ba a Diyarbakır,ya makale a ruwa da kuma iskar wannan yankin.

Kama daga kabilun Hurriyawa, asuriyawa,Farisawa, Romawa, Bizansiyawa, Abbasiyawa, Seljukawa da kuma Turkawan Usamniyya,akalla kabilu iri daban-daban 33 ne suka kafa daular su a garin na Diyarkabır.Yankin wanda duniya ta sani da kasancewa budaddiyar kofar Asiya kan daular Mesopotamia,ta shahara haikan a matsayin muhimmiyar cibiyar kasuwanci da kuma gadar al'adun duniya. Da yake ya kasance a kan babbar hanyar nan ta Silki,wato Silk Road, shi yasa aka gina mafiya kyawawan gidajen hutu na ayarin attajirai da kuma gadojin da babu kamar su a duk fadin duniya.Katafariyar hasumiyarta da kuma lambunan Hevsel sun kasance a jerin muhimmai wuraren al'adu da na tarihi na Diyarbakır.

 

Hasumiyar Diyarbakır,ta yi dukannin hasumiyoyin duniya fintinkau,ganin yadda ta kunshi tarihin kusan illahirin manyan daulolin duniya.Hasumiyar wacce aka gina duba da al'adu da kuma bukatun wannan yankin, na shekaru 7000 da ginuwa.

 

Kama daga katangunta masu tsawon kilomita biyar da rabi,rubuce-rubuce da kuma adon da aka kawata su da su gami da kayatattun kalandojin hasashen kaddara,wato horoscope,Diyabarkır ya tanadi rayayyun alamomin tarihi da na  wayewar mazajen dauri.Tagwayen katangun wannan garin na da kofofi biyar wadanda ke kallon wajen Diyarbakır.Bayan katangar China,Diyarbakır ne ya tanadir katangun mafiya tsawo a duk fadin duniya.

Lambunan Hevsel na a tsakiyar katangun Diyarbakır da kuma kogin Nicle...A tsawon dubban shekaru,an yi amfani da wannan yankin a matsayin wani gaggarumin wurin noma.Watakila,ya kasance daya daga cikin rumbunan mafiya tsufa na yankin Mesopotamia.A lokacin da ruwan kogin Nicle ya janye, al'umomin wancan lokacin na shuka alkama da kuma shahararriyar kankanar Diyarbakır,'ya 'ya itatuwa da kuma kayan lambu masu dumbin yawa a albarkatacciyar kasar da ke shimfide a yankin.An sanar da cewa yawaitan albarkatun noman Diyarbakır na da nasaba ne da amfani da kashin tsuntsaye da aka kwashe karnoni da dama ana yi a matsayin taki.

Lambunan Heysel, sun kasance aljannar tsuntsaye mafi girma na yankin Anatoliyan Turkiyya. Bayan sama da jinsin tsuntsaye 180,akwai karnukan ruwa,dila,Yanyawa,kurege, bushiya da namun daji masu yawan gaske a wadannan lambunan.Yankin na matukar daukar hankali sabili da kyan yanayin da yake da shi.

Wadannan kyawawan katangu da kuma lambunan,sabili da yadda suke cakude a cikin wani yanayi mai ban ta'ajibi da ban sha'wa,yasa suka kasance a matsayi na 14 a jerin muhimman wuraren tarihi da na al'adun duniya na kungiyar raya al'adu da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya,UNESCO.An dai saka Diyarbakır a jerin muhimman tarihi na duniya a shekarar 2015.

Shawararmu ga maziyartan Diyarbakır shi ne,bayan hasumiya da lambunan Hevsel,kar su sake su koma gidajensu ba tare sun zagaya kasuwar tarihi ta "Sipahiler Çarşısını ",Muhallin Hasan Pasha","Masallacin Uluccami","Gidan Nana Maryam AS", gidan hutun attajirai,tsaffin gidajen Diyarbakir da kuma gidajen ajje kayayyakin tarihi ba.

Kazalika,dandana dadadan girke-girken wannan yankin kamar su "Nardan Aşı" mahadin Bulgur (dafa-dukan alkama), Kıyma (narkakken nama) da kuma yazuzzuka iri-iri,abincin "Meftune" mai kunshe da naman rago,kabewa da kuma yalon turawa,sai kuma girkin "Kaburga Dolması" wanda aka yi da hakarkarin akuya,na daga cikin karin shawarwarin da zamu bai wa duk wani maziyarcin yankin Diyarbakır.

 

 Labarai masu alaka