Tarrant dan ta'adda ne Kirista?

Mun sake kasancewa tare da ferfesa Kudret Bulbul shugaban tsangayar siyasa dake jami'ar Ankara Yildirim Beyazit.

Tarrant dan ta'adda ne Kirista?

Harin ta'addancin da ɗan ƙasar Ostraliya mai suna Breton Tarrant ya kaiwa masallatai biyu a ranar juma'a 15 ga watan Maris shekarar 2018 a ƙasar Niyuzelan ya yi sanadiyar rayukan Musulmi 50. A yayinda Yamma bata ko nuna wai an kai harin ta'addanci da ya yi sanadiyar rayuka ba, maharin ya yaɗa haifan bidiyon nasa a yanar gizo. Kafar yaɗa labaran Sanal da ma gidajen talabijin da dama sun dinga yaɗa bakar harin da aka kaiwa Musulmi.

Shin wannan wani laifi ne ? Ko ta'addanci ne ?

  Wannan tambayar bata ko taso ba , amma kafafen yaɗa labaran ƙasashen yamma dama wasu ƴan siyasa basa kallon wannan harin a matsayin ta'addanci. Ma'anar ta'addanci dai shi ne tsoratar da mutane da hanyar kai musu hare haren domin biyan buƙatun Siyasa.  Tarrant wanda ya kwashe kwanaki yana shirin ta'asar da ya aikata ta kaiwa Musulmi hari kashe 50 da raunana wasu da dama, ba'a kallon sa a matsayin ta'addanci, duk da ko ya wallafa wata ƙasidar mai shafi 74 dake bayyana hujjar sa na ƙalubalantar bakar fata da baki a nahiyar Turai.  .

Ba za'a iya kare demokradiyyar da yanci a nahiyar Turai ba kuma.

A nahiyar Turai ra'ayin nazi da facism dake karya tattalin arziki na ci gaba da yaɗuwa. ldan aka kwatanta da sauran ƙasashen za'a ga nuna wariyar launin fata yafi yawa a nahiyar Turai fiye da sauran ƙasashen duniya. Wannan lamarin tsattsaurar ra'ayi na ci gaba da yaɗuwa tamkar yadda yake a lokacin yaƙin duniya na biyu a nahiyar.

Bayan kashe musulmai 50 a Niyuzelan dukkanin addinai, ƙabilu a nahiyar sun ƙalubalanci lamarin. Hakan dai na nuni da hadin kai da goyon baya ga Musulmi. Duk da dai shugabannin siyasar yamma sun yi shiru akan lamarin, yadda firaministan Niyuzelan Jacinda Ardern ta ƙalubalanci lamarin ya nuna da akwai shugabannin masu kima a nahiyar. A cikin wannan yanayin ne firaministan ta daura dankwali ta kaiwa musulmi ta'aziyya. Ta kuma bayyana cewar wannan harin na ta'addanci ne da ba za'a yarda da shi ba, inda ta ƙara da cewa kowa nada yanci zama a cikin ƙasar Niyuzelan ba tare da tsangwama ba.

Kiristoci ‘yan ta'adda ne ?

A dai dai lokacin da kafafen yada labarai na kasashen yamma ke bayyana ayyukan ta'addanci da Musulmi ya kai a matsayin ta'addanci basa ganin irin harin da  Tarrant ya kai a matsayin ta'addancin Kiristawa.

Siyasa da kafafan yada labarai a yammacin duniya, idan Musulmi ya aikata laifi suna alakanta shi da dan jihadi, mai son shari’a da sauran siffofi, amma babu wani da ya kira Tarrant “Dan ta’adda Kirista”. Idan haka ne maganar Tarrant na kira da zai kashe dukk wadanda suke rayuwa a yammacin duniya banda farar fata. A bayanansa da manufofin akwai Kiristanci sosai. Idan akwai bukatar alakanta wani hari da Addini, to akwai dalilai da dama da za su saka a hada wannan harin da Kiristanci. Saboda idan har za a alakanta Addini ko wani tunani da asu ‘yan ta’adda to ana musu hidima ne kawai. Ba za a samar da zaman lafiya a duniya ba idan za a dinga alakanta harin da Musulmai suka kai da Musulunci ko Kiristanci da wanda Kiristoci suka kai.

Watakila dai zai fi dacewa a alakanta wannan hari da ta’addanci ‘yan kuros mai makon Kiristanci.

Duk da wadannan abubuwa, bai kamata a kalli batun kamar yadda Yammacin Duniyaayke kallo ba. Yammacin duniya ba malamanmu ba ne saboda idan muna so mu nuna musu ba ma jin dadin yadda suke alakanta hare-hare da Musulunci, to sai mu ki alakanta wannan da Kiristanci.  
A gefe guda, yadda suka mayar da ta’addanci hanyar amfani, hada Addinai da ta’addanci, da yadda tsawon daruruwan shekaru alakar Addinai da tsaurin ra’ayi suka gushe, ya sanya suna ba wa ta’addanci gudunmowa. Kamar yadda muka tattauna da abokina Berat Ozipek, za a iya gani a loakcinda ake Jihadi, ake yada Addinin Musulunci da aiki da Shari’ar Musulunci, Musulmai, Yahudawa da Kiristoci na rayuwa a waje daya. Saboda haka ne wannan abu ya zama misali mafi kyau wajen tabbatar da kaunar juna a zamantakewa, kuma ba a wani waje aka ga hakan ba sai a karkashin yankunan Musulunci na Daular Usmaniyya, Daular Andalus, da ta Indiya. A wadannan lokutan ba wani Musulmi da ya yi tunanin 11 ga Satumba za ta zo da za a kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba. Kamar yadda aka gani tare da FETO, babu wanda ya yi mafarkin wani zai yi amfani da makamai tare da harbe jama’arsu da jiragen f16. Duk wadannan abubuwa ne da suka faru a kwanakin nan na zamanin yau. Gumakan Budah dake Tora Bora, sannan an rusa Afganistan ba a lokacin da ake shugabancin jama’ar kasar da Shari’ar Musulunci da jama’a suke daukar Jihadi da muhimmanci ba, sai a zamanin yau da babu hakan.

Harin da Tarrant ya kai, daidai yake da na masu tsaurin ra’ayin da suka kai harin 11 ga Satumba da 15 ga Yuli. Dukkan wadannan ukun, sun nuna rashin tausayi, rashin sanin ya kamata da kyamar dan adam ta hanyar kashe ‘yan ba ruwana da ba su ji ba ba su gani ba. Yadda Tarran ya kashe mutane da bindiga, Usama bin Laden da jirgi, ‘yan ta’addar FETO da f16 abu daya ne.

Dole a dauki matakan hana amincewa tda aiyukan ta’addanci ta hanyar daina alakanta Addinin ‘yan ta’adda da abubuwan da suke aikatawa.

Me za a yi?

Tabbas wannan hari da Tarrant ya kai da tsakar rana ya kuma yada a shafukan sada zumunta na da tasirin irin kalamai na nuna wariy, nuna tsana da kyama da kafafan yada labarai na kasashen Yamma suke yi. Wannan nuna kyama ga Musulunci ta yammacin duniya ya nuna karara yadda za a iya kai wa matakan nuna kyama ga Erdogan a Yammacin duniyar.

‘yan ta’adda irin su Tarrant, bin Laden da FETO, duk kokarin da za su yi na halarta aiyukan da suke yi, dole ne duniya ta haka kai wajen yaki da su baki daya.

Dukkan al’Umar duniya a matsayin iyali daya, dole ne mu mayar da martani ga dukkan masu aikata ta’addanci ba tare da kallon manufar da ta sanya suka kai harin ba. Duniya ta zama wani kauye guda daya. Al’Umar aAddinai, kabilu da asali daban-daban na rayuwa a waje daya a ko’ina. Kar mu bayar da iziniga masu son sace ‘yanci, zaman lafiya da kwanciyar hankalinmu tare da dilmiyar da mu a cikin duhunsu. Bari mu kammala makalarmu da wani kira. Dukkan mutanen duniya masu hankali ku hade kai waje daya. Idan ba haka ba, to guguwar da ke kadawa ta duhu za ta yi awon gaba da mu.Labarai masu alaka