Yadda ake yin "köfte" dambun nama a Turkiyya

Ɗaya daga cikin nau'o'in abincin ƙasar Turkiyya da ya zama ruwan dare game duniya shi ne “köfte” watau “meatballs” a lngilishi, zamu kuma iya kiransa dambun nama a Hausa

Yadda ake yin "köfte" dambun nama a Turkiyya

Ɗaya daga cikin nau'o'in abincin ƙasar Turkiyya da ya zama ruwan dare game duniya shi ne “köfte” watau “meatballs” a lngilishi, zamu kuma iya kiransa dambun nama a Hausa. Wannan nau'in abincin ya samu karɓuwa a gidan kowa a gidan talakawa da ma a gidajen masu hannu da shuni. Bugu da ƙari, yana ɗaya daga cikin nau'o'in abincin da zaka samu a gidaje da kuma gidajen sayar da abinci. Kamar yadda wasu ke bayyana wa za'a iya samun ire-iren wannan nau'in abincin har 300. Ana raɗa wa wannan nau'in abincin suna ne da garin da ake yinsa. A dalilin haka kusan ko wani gari ko yanki daga cikin yankunan ƙasar Turkiyya suna da nasu nau'in köfte ɗin. Alal misali, a ƙasar Turkiyya akwai İzmir köfte, Tekirdağ köfte, Sivas köfte da makamantansu. Shin ko menene wannan nau'in abincin köfte ɗin; “Köfte dai niƙeƙƙen nama ne da ake dafawa haɗe da kayan yaji” Ko wane yankin nada ire-iren kayan yajin da aka haɗa Köfte din dashi. A cikin wannan shirin namu mai suna Abincin Turkiyya, a yau zamu bayyana muku yadda ake yin Köfte na gargajiya mai saukin haɗawa a ƙasar Turkiyya.

 

Domin sarrafa Köfte na gargajiya ana bukatar waɗannan kayyayaki;

Albasa ɗaya

Bushesshen biredi yanki biyu.

Yankakkun rassa 8-10 na ganyen faski

Gram 500 na nama yankakku.

Ƙwai ɗaya

Man Zaitun Cokali ɗaya

Cokalin Cumin ɗaya.

Cokalin baƙin barkono ɗaya

Gishiri

 

Yanzu kuma sai yadda ake dafawa;

Domin yin Köfte da farko dai za'a jiƙa busassun biredin a cikin ruwa a tatse sai a mayar dashi tamkar tunkuza. Daga bisani kuma sai a yayyanke albasa a cikin wani kwano. A cikin yankakkun albasan sai a zuba naman, biredi, kwai, faski, barkono, cumin da gishiri a motse sosai. Sannan kuma sai a farfasa walnut a kuma rugurguje shi yadda girmansa ba za wuce cm ɗaya ba. Bayan an motse da sauran haɗin baki ɗaya sai a ɗan soya da mai kaɗan. A iya cinsa da zafinsa.

A more lafiya!

 

A cikin wannan shirin namu mai suna Abincin Turkiyya, a yau mun bayyana muku yadda ake yin Köfte nau'in abinci mai daraja a ƙasar Turkiyya. A shirinmu na gaba kuma zamu zo muku da wani nau'in abincin ƙasar Turkiyya mai daɗi.

Ku huta lafiya.

 Labarai masu alaka