Muhimman bayanai game da tallafin karatun kasar Turkiyya

Ya zama wajibi ga  dukkan ɗaliban dake  neman tallafin karatun Turkiyya su gabatar da waɗannan takardun a lokacin da suke cike fom ɗin a yanar gizo

Muhimman bayanai game da tallafin karatun kasar Turkiyya

A ƴan makonnin da suka gabata mun muku bayani akan ayyukan Hukumar Tallafin Karatu ta ƙasar Turkiyya watau YTB. A wannan makon zamu yi bayani akan waɗanda suka cancanci miƙa takardunsu domin samun tallafin karatun na Turkiyya. Zamu kuma bayyana muku ƙa'idojin hukumar da kuma bayar da amsar akan fa'idodin da tallafin karatun Turkiyya ya ƙunsa.

 

 

TAKARDUN DA AKE BUƘATA

 

Ya zama wajibi ga  dukkan ɗaliban dake  neman tallafin karatun Turkiyya su gabatar da waɗannan takardun a lokacin da suke cike fom ɗin a yanar gizo.

 

 • Katin shaidan zama ɗan ƙasa ko makamancinsa.

 

 • Pasaport
 • Hoton ɗalibin wanda aka ɗauka bada jiwaba ba.
 • Takardun jarabawowin da ɗalibin ya yi
 • Takardar shaidar kammala karatu
 • Takardar transcript dake nuna kwasa-kwasai da ɗalibi ya yi a makaranta.
 • Shaidar takardar jarabawowin ƙasa da ƙasa (Kamar GRE da GMAT- ldan har kwas ɗin da ɗalibi ke buƙatar karantawa yana buƙatar su)
 • Jarabawar yare dangane da yaren da ake koyar da kwas ɗin da ɗalibi ke buƙata
 • Ƙasidar da ɗalibi ya taɓa rubutawa da kuma wanda yake buƙatar gudanar da bincike akai (Ga ɗaliban dake neman rukunin karatun digirgir)

KO SUWA SUKA CANCANCI SU MIƘA TAKARDUNSU ?

 

 • Ɗaliban dukkan ƙasashe banda na ƙasar Turkiyya zasu iya neman tallafin karatun Turkiyya.
 • Domin samun tallafin karatun Turkiyya, ɗalibi na bukatar samun nasarorin karatu kamar haka:
 • Waɗanda ke neman karatu a mataƙin digiri na farko ana bukatar makin jarabawar su yakai kashi 70 cikin ɗari
 • A fannin lafiya kuwa kamarsu likitanci, magani da likitan haƙora ana bukatar makin ɗalibi yakai kashi 90 cikin ɗari
 • Masu neman matakin digiri na biyu da kuma digirgir kuwa ana bukatar makinsu yakai kashi 75 cikin ɗari
 • Bugu da ƙari, ana kuma buƙatar cika waɗannan ƙa'idoji domin neman tallafin karatun Turkiyya:
 • Waɗanda ke neman karatun digiri na farko dole su kasance ƴan ƙasa da shekaru 21
 • Ɗaliban dake neman rukunin digiri na biyu dole su kasance ƴan ƙasa da shekaru 30
 • Masu neman karatun digirgir kuwa dole su kasance ƴan ƙasa da shekaru 35
 • Masana masu buƙatar gudanar da bincike a fannoni daban-daban dole su kasance ƴan ƙasa da shekaru 45

KO WASU FA'lDOJI NE TALLAFIN KARATUN TURKIYYA YA ƘUNSA ?

 

 1. Kuɗin kashi a duk wata:
  • Masu karatun digiri na farko: Turkish Lira 700 duk wata
  • Masu karatun matakin digiri na biyu: Lira 950 duk wata
  • Masu karatun digirgir: Lira 1400 duk wata
  • Masana masu gudanar da bincike a fannoni daban-daban: Lira 3000 duk wata
  • Waɗanda ke kan tsarin koyar da Turkanci a lokacin bazara: Lira 500 duk wata
  • Waɗanda ke kan tsarin koyar da Turkanci ga ma'aikata:  Lira 2000 duk wata
 2. Kuɗin makaranta
 3. Tiketin jirgi na zuwa da dawowa bayan kammala karatu
 4. Masauki
 5. Koyar da harshen Turkanci na shekara ɗaya

 

 

 Labarai masu alaka