Zaben 2018: Ci gaba da Zaman Lafiya da Tsarin Shugaban Kasa

Sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara Farfesa Kudret Bulbul.

Zaben 2018: Ci gaba da Zaman Lafiya da Tsarin Shugaban Kasa

Matsalolin Kasashen Duniya: 26

Kasashen Duniya. Turkiyya ta gudanar da Babban zabe karo na 27 kuma na farko na Shugaban Kasa mai cikakken iko. Jam’iyyar AKP ta samu kaso 52.5 a zaben Shugaban Kasa inda Shugaba Erdoğan ya yi nasara wanda hakan ya sa babu bukatar a je ga zagaye na 2. Erdoğan ya zama zababben shugaban Turkiyya na farko mai cikakken ikon zartarwa. Ya doke abokin hamayyarsa Muharrem Ince da ya samu kaso 30.6 na kuri’un da aka kada. A karon farko jam’iyyar AKP ta rasa rinjaye a Majalisar dokoki tun shekarar 2002 in banda a zaben watan Yunin 2015. 

Za a mu iya takaice yadda aka gudanar da zaben Shugaban Kasar Turkiyya na farko a tarihi cikin yanayi na gaskiya da adalci kamar haka:

Fita jefa kuri’: Kaso 85.5 na masu jefa kuri’a su kusan miliyan 60 ne suka fita zabe. Za a iya kallon wannan abu a matsayin na tarihi  a Turkiyya da ma duniya baki daya saboda yadda aka gudanar da zaben ciin adalci, gaskiya da gogayya. Wannan nuni da ir,in akrfi da demokradiyyar Turkiyya ta yi wadda ta faro tun shekarar 1876. Kamar yadda aka fadi a shafukan sada zumunta na yanar gizo A kasashen Yamma akwai akwatunan zabe, babu masu jefa kuri’a isassu kuma a kasashen Gabas babu isassun akwatuna amma a Turkiyya ana da akwatunan da kuma masu jefa kuri’a wanda ke bayar da fata nagari ga demokradiyyarmu.

Cigaban zaman lafiyar zamantakewa: Tun daga shekarar 2002 zuwa yau jam’iyyar AKP ta lashe zabe sau 5 a jere. A tarihin siyasar Turkiyya ba a taba samun nasara irin wannan ba. Samun yanayi na lashe zabe sau 5 a jere a kasashen da ake gogayya abu ne mai wahala. İdan aka yi tunani game da abubuwan da ke kawo karshen mulki, da yadda AKP ta ke sake lashe zabe, za aga alamun masu jefa kuri’a sun gamsu da yadda ake jagorantar su kuma suna son a ci gaba da dabbaka siyasa. Masu jefa kuri’a ba su saurari irin tsoratarwa da sukar da ‘yan adawa suka dinga yi ba.

An sake cewa Eh don Tsarin Shugaban Kasa: jam’iyyun adawa da hadin kan al’uma da suka taru a karkashin sa, kafin zabe sun dinga cewa, idan suka yi nasara za su dawo da tsarin amfani da Firaminista. Saboda haka ya sanya a wannan karon aka maimaita Eh din da aka ce a zaben kuri’ar raba gardama na shekarar 2017 da aka tabbatar da Tsarin Shugaban Kasa. A zaben raba gardama da kaso 51.4 aka amince da Sabon tsarin. Shugaba Erdoğan ya kara yawan magya baya inda ya samu kaso 52.5 a zaben Shugaban Kasa. Za a iya cewa, al’uma sun sake amince wa da tsarin na Shugaban Kasa.

Tafiya da dawowar jam’iyyu: Zabe na nuna yadda a tsakanin dukkan jam’iyyu ake da musaya da jeka dawo. Daga AKP zuwa MHP, daga CHP zuwa IP da HDP za a ga yadda samun kuri’u ke jan ra’ayi. A lokacin da shugaba Erdoğan ya yi jawabin nasara ya bayyana cewa, sun ga irin raguwar yawan kuri’un AKP a saboda haka za su yi abinda ya dace. Yadda Erdoğan da Ince suka samu kuri’u sama da na jam’iyyarsu a bangaren ‘yan majalisu na nuni da cewa, shugabannin sun samu kuri’u daga wasu jam’iyyun da ba nasu ba. Halaj na nuni da yadda Erdoğan ya samu kuri’u daga wani bangare na Kurdawa.

Wannan yanayi ne mai kyau ga demokradiyya idan aka kalli yadda masu jefa kuri’a suke kokarin sauya tarihin jam’iyyu. Hakan zai sanya jam’ityu su dinga kallo da karbar bukatun masu jefa kuri’a cikin gaggawa.

Yawan samun masu wakilci a majalisa: Sakamakon yadda ake neman kaso10 don shiga majalisa, ra’ayin wasu jama’ar Turkiyya ba wanzuwa a majalisar dokoki. Amma hadin kan da aka yi a zabukan da suka gabata ya dan rage radadin wannan abu. Jam’iyyu 8 sun shiga majalida da kansu kkuma saboda kawancen da suka kulla. Wadannan jam’iyyun su ne, AKP, CHP, MHP, HDP, IP, BBP, Saadet da DP. A zabukan da aka yi bayan 1950 a shekarar 1960 ne kawai jam’iyyu 8 suka shiga majalisar dokoki.

Tasirin hadin kan da sabon tsarin ya kawo: A shirin da muka kawo muku a makon da ya gabata mun tabo batun cewa, an wuce lokacin da jam’iyyu za su dinga neman kuri’ar mutanensu kawai. A lokacin yakin neman zabe da bayansa an ga yadda tasirin batun sai an samu kaso 50+1 sannan za a yi nasara. Cewar sai an zabi Shgaba da kuri’u kaso 50+1 na hade kan jam’iyyy, daidaita al’amura, da kuma sanya ‘yan takara da jam’iyyunsu nemöan hadin kai ba na ‘yan jam’iyyarsu kadai ba. Hakan na sanya kasa ta zama mai karfi sosaia demokradiyyance tare da ‘yantar da kanta. Wannan yanyi na kuma samar da tsaro a cikin kasa.

Kassara Girman kan kasashen Duniya: kamar ya ke a zabukan baya, wasu manyan kasashen duniya, kafafan yada labarai da kungiyoyin kasa da kasa sun yi yunkurin tsoma hannu a zaben Turkiyya. Sun nuna adawa da jam’iyyar AKP tare da zargin ta ada abubuwan marasa tushe. Kamar yadda ya kasance a zabukan baya masu jefa kuri’a ba su saurare su ba inda suka zabi abinda suke so. Haka abin ya ke a zaben da aka yi a kasashen waje. Duk da yadda wasu kasashen Yamma suka dinga yi wa Turkawa barazana da hana su ‘Yancinsu, amma sa,i da masu zaben suka sake kafa tarihi. Sun zabi abin da suke so wato jam’iyyar AKP. Masu zabe sun jefa kuri’a ne ba ta hanyar duba abin da kasashen duniya ke so, a a duba da abinda suke so. Kuma girmama abin da jama’a suka zaba na samar da kwanciyar hankali a kasashen duniya.

Kudaden da kowanne dan aksa ya ke samu a Turkiyya daga shekarar 2000 zuwa yau ya karu daga dala dubu 2 zuwa dubu 10. Turkiyya ta girmama kan ‘yanci da demokradiyya. Duk da matsalolin da ake da su a kasashemakotan Turkiyya irin su Iraki

Siriya, Jojiya, Libiya, Yukren, Girka Isra’ila da sauransu amma ta zauna kalau cikin kwanciyar hankali. An yi watsi tare da juyar da yunkurin juyin mulkin FETO da sauran kungiyoyi. Ta hanyar kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka jefa a shekarar 2016 da kuma wannan zabe da aka yi an kafa tarhihi na kusan shekaru 150 a demokradiyyar Turkiyya inda Kasar ta koma aiki da tsarin Shugaban Kasa. Kuma Turkiyya ta yi nasara kan wannan abu ne saboda bin tsari na siyasa. A zabuka da aka yi su cikin gogayya da gaskiya,, da a ce babu gwamnati mai karfi da al’uma suka ba wa karfin iko to da ba a tabbatar da saute-sauyen da ake gani ba. Wannan nasara da Turkiyya ke samu ba tata kadai ba ce, tana da muhimmanci ga yankinta da ma yammacin duniya baki daya. A loakcin da Yammacin duniya ke fargabar karbar ‘yan gudun hijira 3, Turkiyya kuma ta karbi miliyan 3.5. Ya kamata kowa ya san irin daraja, zaman lafiya, kwanciyar hankli da demokradiyya da Turkiyya ke da shi.

Sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara Farfesa Kudret Bulbul.Labarai masu alaka