Sabbin matakan yaki da ta'addanci da Turkiyya ke dauka

Bayan yunkurin juyin mulki 15 ga watan Yuni Turkiyya ta dauki sabon salo wajen yaƙi da ta'addanci, wanda ta yi ba wai a cikin ƙasarta kawai ba har ma a yankunan baki daya.

Sabbin matakan yaki da ta'addanci da Turkiyya ke dauka

A sabbin salon yaƙi da ta'addanci ne ta ƙaddamar da hare-haren Firat Kalkanı da na reshen zaitun inda ta yi nasarar kauda ƴan ta'addar DEASH daga yankin Afrin. A halin yanzu ana shirye-shiryen ƙalubalantar ƙungiyoyin ta'addar PKK-YPG a yankunan Kandil, Sincar da Munbich. An dai soma fatattakar ƴan ta'adda a yankin Kandil a ƴan watannin da suka gabata, a yankin Membich kuwa a tattauna da Amurka a yayinda a yankin Sincar tuni an shirya ɗaukar matakan soja akan ƴan ta'addar guraren.

Kan wannan batu za mu kawo kawo muku Sharhin Can ACUN jami'i a Cibiyar Nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA dake Ankara babban birnin Turkiyya.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi jawabi a jumlace inda ya bayyana cewar Turkiyya na daukar matakai ɗaya bayan ɗaya domin kauda ƴan ta'addar dake doron ƙasa. Erdoğan ya kara da cewa ko dai ƴan adawa basu so ba zamu ɗauki matakan kauda ƴan ta'adda daga Kandil kamar yadda muka yi a Afrin, Jerablus, El Babi da Azez. Erdoğan ya kara da cewa duk da akwai yan ta'adda da suka laɓe karkashin ƴan siyasa zamu dauki matakan kauda ƴan ta'adda daga ƙasarmu. Wadanda suka ƙalubalanci yaki da ta'addanci da muka yi a Afrin suna ci gaba da ƙalubalantar yunkurin yaƙi da ta'addanci a Kandil a yanzu, zamu basu kunya kamar yadda muka yi a baya.

 Erdoğan ya ƙara da cewa mun fara fatattakar ƴan ta'adda a yankunan Kandil, Sincar a ranar 11 ga watan Yuni, jiragen mu 20 sun kai hare-hare a wurare 14 sun kuma dawo, kuma zasu ci gaba, Erdoğan ya ƙara da cewa a watannin da suka gabata ne muka fara shirin kauda ƴan ta'adda a Kandil, sojojin Turkiyya sun kai hare-hare wuraren a asirce mai tsawon kilomita 24 a inda suka kafe sansanoni sa ido har 11.

Hare-haren kauda ta'addanci da Turkiyya ke yi ba wai a Kandil ne kawai ba, har ma a yankunan Siriya da lraqi. Haka kuma Turkiyya ta na daukar matakan kauda ƴan ta'adda PKK da YBŞ a yankunan. Duk da kungiyar ta'addar PKK-YBŞ da Amurka da gwamnatin lraqi sun ka baiwa damar mamayar Sincar sun ɗan kaura daga yankin har ila yau akwai wasunsu a yankunan.

 Matakan kauda ta'addanci da Turkiyya ke dauka bai tsaya ga na soja kawai ba, Turkiyya na daukar matakan diflomasi a yunkurin. Duk da dai Turkiyya ba ta dauki wasu kwararan matakai akan lamurkan gwamnatin lraqi da arewacin lraqi ba, ta yi kokari wajen aiyanar da matakan diflomasi domin samar da lumana a yankin. Haka kuma Turkiyya ta dauki matakan diflomasi wajen yaƙi da ƴan ta'addar PKK-YPG a Siriya inda ta tattauna da Amurka akan harkokin Membich da ma sauran yankunan.

 Turkiyya ta tattauna da Amurka akan lamurkan Membich domin daukar matakan kauda ƴan ta'adda daga Membich. Sun aiyanar da hakan ne domin samar da hanyar diflomasi domin kauda ƴan ta'addar PKK-YPG daga Membich. Ƙasashen Turkiyya, Faransa da Amurka na kokarin haddin gwiwa domin samar da lumana a yankin Membich.

Wannan matakin diflomasi da  Turkiyya ke dauka domin kauda ta'addanci bai tsaya ga Membich ba tana kokarin ɗaukar matakan diflomasi wajen kauda ƴan ta'adda a gabashin Firat. Kamar dai yadda aka yi a firat akwai bukatar a dauki irin wannan matakan a yankunan Rakka, Dery ez zor da Tal Abyad hakan ne zai kuɓutar da al'umma yankin daga zaluncin YPG.

Turkiyya ta yi kokari wajen ɗaukar matakan kauda ƴan ta'adda a yankunan, a yayinda a wasu yankunan kuma ta rage addabar da ƴan ta'adda ke yi wa al'umma. Matakan da Turkiya ta dauka sun rage ugubar da kungiyar ta'addar PKK-YPG suke yi wa fararen hula a yankunan.

Sharhin Can ACUN jami'i a Cibiyar Nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA dake Ankara babban birnin Turkiyya.


Tag: Daesh , PKK , Turkiyya

Labarai masu alaka