Mene ne Matsayin Kurdawa a Musulunci?

Kan wannan batu za mu kawo muku Sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

Mene ne Matsayin Kurdawa a Musulunci?

Matsalolin Kasashen Duniya: 14

Abraham Lincoln ya bayyana cewa, “Kowa a wani lokaci, wasu kuma a kowanne lokaci, amma a koyaushe ba za ka zambaci kowa ba.” Ana iya daukar hanya har ta kai ga ana juyar da tunanin mutane. Amma kuma fita gaba kaddarar abin da ya ke zahiri ne. Kafafan yada labarai na Yammacin Duniya, na nuna ‘Yan ta’addar PKK/YPG a matsayin mayaka masu neman ‘Yanci. A wajensu wannan kngiua na wakiltar dukkan Kurdawa ne. Yakar wannan kungiya yakar Kurdawa ne. Taimaka musu kuma taimaka wa Kurdawa ne. Suna nuna cewa, hare-haren Turkiyya a Afrin ana kai wa Kurdawa ne. Abin takaici tashar Aljazeera ma na amfani da wannan harshen a wasu lokutan.

Kan wannan batu za mu kawo muku Sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

Kungiyoyin Ta’adda Kurdawa da ke karar da Al’umar kurdawa

Idan har haka ne, to ‘yan ta’addar PKK jama’ar Kurdawa suka fi cutarwa kuma suna ci gaba da cutar da su a yanzu. Mutane sama da dubu 40 da Turkiyya ta rasa sakamakon hare-haren PKK Kurdawa ne. Kungiyar PKK na amfani da tsarin Maksits ko na Leninnist wajen yin kşsan kare dangi ga Kurdawan da ba su rungumi yaki ba. Sakamakon haka ya sanya miliyoyin mutane da ke kudanci da kudu maso-gabashin Turkiyya yin hijira zuwa Yammacin kasar musamman ma Istanbul. Hakan ya sanya Istanbul ya zama garin da Kurdawa suka fi kowanne yawa a Turkiyya. Kuma mutanen da PKK da ta’addancinta suka tagayyara ba suna gudun hijira a Iraki ko Siriya ba ne, suna gudo wa Turkiyya ne.

A yau kungiyar PYD reshen PKK na yin irin wannan abu a na kisan kare dangi a Siriya. PYD tare da taimakon Amurka na son kafa matattarar ‘Yan ta’adda da za ta dangana da tekun mediterrennean. Kamar yadda PKK ta yi a baya, PYD ma na lkashe Kurdawa, larabawa da Turkmen da suka ki mara mata baya a Siriya. Sakamakon haka dubunnan daruruwan Kurdawa suka yi gudun hijira zuwa Turkiyya. Tare da wadanda suka guje wa Daesh a yau akwai miliyoyin Siriyawa a Turkiyya.

Hakika, ba za a ce a tsakanin Kurdawa babu masu taimaka wa wannan kungiya ta ta’adda ba. Kallon PKK a matsayin wakiliyar Kurdawa to kamar kallon Hitler a matsayin wailin dyukkan Jamusawa ko kuma Mussolini a matsayin wakilin jama’ar Italiya baki daya.

Wadannan tambayoyi da ake yawan tambaya a kafafan yada labarin Yammacin Duniya na samun amsa daga matasan Kurdawa. Amma kuma masu wannan tambayar ba sa yin wannan tambayar da za mu kawo. Me ya sa ba raba jihohin Amurka 50 ba wadanda suka hada da al’umu daban-daban?. Me ya sa dukkan kasashen yamma da suke taimaka wa ‘Yan aware a gabas ta Tsakiya ba sa goyon bayan ‘yan awaren kataloniya? Duk da cewa, bai taba aikata aiyukan ta’addanci amma Jamus na tsare da shugaban kataloniya Carles Puigdemont. Matsalar ba ta kowacce al’uma a yi mata kasa ba ce, siyasa ce ta raba ka juya. Kamar yadda Edmund Burke mai sukar juyin juya halin faransa ya bayyana cewa, shirn me irin wadanna tunani suke hidimtawa.

Matsalar idan za a ce ta kowacce al’uma ta samu kasarta kai ko ma kowacce jama’a da zama kasa, to ai a baya yankunanmu sun fuskanci irin wannan abu. A lokacin tafiyar Kiristoci da mamayarsu a Gabas ta Tsakiya kusan kowacce jama’a da shugabancinta. Yankin Anadolu ya kasance karkashin shugabancin mazajen Turkawa. A krshe me ya faru? Babu wani gari na Musulunci da ya ke a rarrabe da ba a samu damar an kutsa cikinsa ba tare da mamaye shi. Idan har aka fara rarraba wata al’uma to hakan zai tsaya ne a lokacin da masu rarraba sun suka so. Shekaru 100 da suka wuce Turawan Yamma sun yi amfani da irin wannan tsari wajen raba Larabawa. A yau akwai kasashen Larabwa 23. Ana tattauna yadda za a raba wasu kasashen da suka hada da Iraki da Siriya da ma masarautu. Hakan ya sanya Gabas ta Tsakiya zama a cikin hali mafi muni a tarihi.  

A lokacin da ake ji da ganin tsananin ciwon halin da aka shiga, to kamata ya yi a mayar da hankali wajen batun hade kan Gabas ta Tsakiya ba wi raba al’umarta ba.

Kurdawan da ba ruwansu da Addini mutanen kirki ne?

Kafafan yada labaran yamma na nuna kungiyar ta’adda ta PKK a matsayin kungiya da ba ruwanta da Addini wanda hakan ke sa ake kara yaba mata da ba ta taimako. Ana alakanta Musulunci da ta’addanci, tare da nuna Kurdawa kamar mara sa son addini. Ana bayyana kamar suna neman mafitar tsarinsu na Secularism a Turance. Wanna ba wani abu ba ne illa yunkurin sauya tunanin mutane. Saboda an san cewa, yakin duniya na farko da na biyu sun zama mafiya muni a tarihin dan adam wanda aka kashe miliyoyin mutane amma kuma sun faru ne tsakanin kasashe da ba ruwansu da Addini. Asali ko da batun Addini ko babu, zalunci zalunci ne, mulkin mallaka ma haka, ba wai kasahsne yamma suna taimaka wa kungiyar ta’adda ta PKK ne saboda ba ruwansu da Addini ba, a a sai don suna amfani da ita ne akwai. Haka kuma duk jama’ar da ta rasa al’adu, mutunci da darajarta to tana kokarin jingina ne da kasashen yamma, ko tana da Addn,i ko babu.

Me ya sa ake ta jirkita gaskiya?

“Idan ba a dauki izina daga tarihi ba to za a maimaita shi”. Yau tana zama madubin gobe, jiya kuma madubin yau.

Idan aka dubi tarihi, za a ga kurdawa da suke daya daga cikin masu tsaron gabas ta Tsakiya, idan suka hade da Larabawa da Tuırkawa sai sun fi samun kwanciyar hankali. A lokacin da aka raba su sai su zama cikin hawaye da wahala. Ana ta kashe tare da zaluntar su. Sai su zama wajen wasan Sharrin duniya. Hadin kan Kurdawa, Larabawa da Turkawa ne ya hana mamayar ‘yan Mishan a yankunanmu. Kwamanda kuma Bakurde ne ya jagpranci runduna wajen kubutar da Kudus daga hannun Yahudawa inda ya samar da zaman lafiya. A yanzu kasashen yamma na ci gaba da maimaita abinda suka yi ne. Suna kokarin jan wani bangare na masu kare Gabas ta tsakiya su 3 ya zama nata. Ta hakan suna kokarin yi musu mulkin mallaka ne tare da kai hare-hare. A lokacin hare-haren ‘yan mishan an yi amfani da hakan tsakanbin Kiristoci da Armeniyawa. A yanzu don hargitsa yankunan ısra’ila ana sake aiki da wannan hanya. Amma da fari ana son a fara amfani da wasu kasashen Musulmi su zama kamar masu dakon manufar ‘yan mulkin mallaka. Da wannan manufar, ana son a tafiyar da Kurdawa kan ra’ayin Marksist/Leninist. Ana zuga su da cewa, suna yaki da ‘yan ta’addar Daesh. Amma asalin manufar shi ne a samar da raguwar al’uma a cikin Musulmi da za ta sayar da yankunanta.

Duk da kokarin tafiyar da tunanin mutane wasu Kurdawa sun farga kan wannan batu. Suna kuma nuna kyamar abin da ake yi. Za a kawo lokaci da Kurdawa, Turkawa da Larabawa za su sake nasarar shekaru 1000 a wannan yankin. Yaranmu ba za su zama masu dakpon manufofin ‘yan mulkin mallaka da na ‘yan Mishan ba.

Sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

 Labarai masu alaka