Me ya sa ake samun juyin mulki a Turkiyya?

28 ga Fabrairu: Juyin Mulkin Karshe na Sakamakon Yakin Cacar Baki

Me ya sa ake samun juyin mulki a Turkiyya?

Matsalolin Kasashen Duniya -09

Za mu kawo muku sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami’ar Yildirim Beyazit Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana.

Shekaru 21 kenan wato a ranar 28 ga watan Fabrairun 1997 Turkiyya ta fuskanci juyin mulki da ya ke a cikin tarihinta.

Yunkurin juyin mulki ko kifar da gwamnati ba wani abu ba ne sabo ga Turkiyya. Za a iya ganin yadda duk bayan shekaru 10 a tarihin Turkiyya sai an samu abu irin haka. An yi yunkurin juyin mulki a Turkiyya a shekarun 1960, 1971, 1980, 1997 (28 Fabrairu), 2007 (27 Afrilu) 2016 (15 Yuli) amma za iya cewa, idan aka zo batun juyin mulkin 1997, da abubuwan da suka faru a juyin mulkin 1980 wanda shi ne na karshe za ga yadda bukatar wani juyin mulkin ta sake taso wa, amma idan aka kalli yadda mai juyin mulkin Kenan Evren ya zauna a karaga na tsawon watanni 8 kawai to za a fahimci hakan sosai.

Me ya sa duk bayan shekaru 10 Turkiyya ta ke fuskantar juyin mulki?

Kasashen duniya manya ba za su taba barin kasashe masu muhimanci da ke taka rawa ba irin Turkiyya. Sun san cewa, idan suka kyale irin wadannan kasashe to za su habaka tare da girmama sosai a duniya. Shi ya sa a koyaushe suke so su zama suna juya wadannan kasashe. Mun san haka a Jamus. Sau 2 kasar na fada wa tarkon kasashe na su sauya tsarinta, a yanzu an takaice soji ta hanyar amfan da kundin tsarin mulki.

An ga kyakkyawar makomar wannan kasashekaru bayan an yi juyin mulki tare da rataye Firaminista Adnan Amnederes. Shi ya sa a kundin tsarin mulkin 1961 aka samar da tsarin da za a dinga juya zababbu. Shi ya ake ta samun juyin mulki duk bayan shekaru 10, saboda an samar da dokokin da suka takaita karfin zababbu.

Kamar a Turkiyya, tasirin cikin gida na irin juyin mulkin da ake yi a kasashe za zai misaltu ba. A makon da ya gabata tsohon shugaban CIA James Woolsey, game da batun binciken da lauya Robert Mueller na Rasha ta tsoma hannu a zaben Amurka, ya yi ikirari da cewa, Amurkan ma na tsoma hannu a zabukan wasu kasashe. Bayan juyin mulkin 1980 a Turkiyya, Mai Bayar da Shawara kan tsaro na Amurka Paul Henze ya fada wa shugaban kasar Amurka na wannan lokacin Jimmy Carter cewa, ‘yan’ansu sun yi nasara. A shekarun 1990 Turkiyya bayan an kashe shugaba Ozal da wasu shekaru kasar ta habaka sosai wajen tattalin arziki da ‘yanci. A zamanin jam’iyyar refah karkashin Marigayi Erbakan kuma an samu ci gaba sosai. Idan lamarin ya ci gaba da tafiya a haka Turkiyya za ta zama mai tafiya kan kashin kanta ba tare da dogaro da waje ba.

A cikin wannan yanayi ne aka yi juyin mulkin 28 ga Fabrairu.

Yadda Juyin mulkin 28 ga Fabrairu ya afku

Lamarin ya fara a wannan rana bayan da tankokin yaki suka taso daga gundumar Sincan zuwa cikin garin Ankara. Wannan abu ya zo kamar bako da ba a saba gani ba. Amma tun da kuna kasa wadda tankokin yaki suka kewaye majalisar dokoki, suka kashe shugabannin da ministoci, to da kun ga jerin gwanon tankoki kun san da walakin goro a miya. Da haka abin ya girmama. A majalisar staron kasa, an dauki matakin tafiyar da gwamnati wanda sojoji suka yi. Bayan da aka gano niyyar sojojin, sai kasa ta rikice kamar da ma ana jiran hakan. Sai kawai abin ya zama kamar da ma an yi gwajin sa. Sai kawai shugabannin soji suka bayar da sanarwarsu.

Sakamako...

Amma tabbas abun bai tsaya a nan kawai ba, gwamnatin da ta zo ta sha fama da kafa hadaka, an kama mutane da dama, an kori wasu daga aiki, an mutu, wasu sun kashe kawunansu an cuci rayuwar wasu da dama....

An janye duk wani ‘yanci da hakkoki da mutane suke da shi. Turkiyya ta koma kasa da sojoji ke jagoranta......

Kamar yadda aka gani a shekarar 2002 kasa ce da tattalin arzikinta ya ruguje..

Cin hanci da rashawa, fashi da makami da sace-sace sun yawaita a lokacin...

Bayan haka me ya faru

Juyin mulkin 28 ga watan Fabrairu da kasashe suka yi yunkurin cukwuikwiye Turkiyya a ciki da wajenta ya zama juyin mulki na karshe da ya faru sakamakon yakin cacar baki. An ga yadda ba za a iya sake juya Turkiyya yadda ake so ba kawai saboda yakin cacar baki da ake yi a duniya a tsakanin kasashe. Sakamakon dunkulewar duniya, kafafan yada labarai na zamani da demokradiyya mummuna da mai kyau, ya sanya ba za a iya sake mallakar Turkiyya ba ta hanyar yakin cacar baki. Idan muka kalli baya zuwa yau, za mu iya cewa, 28 ga Fabrairu bai yi nasara da yakin cacar baki ba, amma kuma ya yi nasarar sake fasalin dabi’un al’uma. Saboda a yau duk wasu kungiyoyin FETO da na Addini an magance su. Idan muka kalli lamarin za mu ga ce, sakamakon 28 ga Fabrairu an tsaftace mutane da dama saboda 15 ga Yuli. An tafiyar da demokradiyya da al’uma saiaka zo aka kafa FETO.

Tare da hakan, an ga yadda Shugaban kasar Turkiyya recep tayyip Erdoğan ya ki mika wuta, kuma al’umar turkawa suka tsaya tare da shi kai da fata. Mutane 250 ne suka yi shahada inda wasu sama da dubu 2000 suka jikkata a ranar 15 ga watan Yuli. Amma kuma an tsare kasa da makomar Turkawa. Turkawa sun nuna wa duniya yadda ake karfafa demokradiyya ta hanyar hana yunkurin juyin mulki nasara.

Darussan 28 ga Fabrairu

Babban abin da ke damun Manyan kasashe Duniya shi ne tsarin da suka samar ba wai da me tsarin ya dogara ba. Saboda haka, wadannan kasashe ba su damu da ‘yanci ko makomar jama’ar wasu kasashen ba, su kawai dai bukatarsu ta biya. Babu ruwansu da Addini, maguzanci, ko kishin kasa. Suna amfani da kowanne irin tsari wajen cimma burinsu.

Masu wannan abu na mamaye kasashe na saka wa mutane kowacce irin guba a tsarinsu du su sami abin da suke so. Wannan tsari na daya daga cikin abubuwan da ke ruguza dukkan tsarukan al’uma da suka hada na shari’a, gudanarwa, ilimi da sauransu. Yana mayar da tsarukansu baya sosai.

Tsarin tsaro rufaffe kuma mara dokoki na daya daga cikin abubuwan da tsarinmanyan kasashe ke haifarwa. Sakamakon haka tsarin tsaro dole ne ya kasance karkashin kulawar demokradiyya da kula da shi domin hakan na da matkar muhimmanci.

Kwarewar da Turkiyya ta samu bayan shan wahala, ta nuna hanya ga dukkan masu son rayuwa cikin ‘yanci da walwala.

Mun kawo muku sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami’ar Yildirim Beyazit Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana.Labarai masu alaka