Matsalolin Kasashen Turai a Yau

Rikicin Nahiyar Turai: Nahiyar Turai na rasa darajoji da martabobinta.

Matsalolin Kasashen Turai a Yau

Matsalolin Kasashen Duniya -08

Za mu kawo muku nazari kan sharhin Farfesa Kudret Bülbül, Shugaban Tsangayar Nazarin Kimiyyar Siyasa Ta Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara.

Ku yi tunani a lokaci guda, a ce a kasar da kuke a kashe Kiristoci 5 ko Yahudawa, a kone su tare da kashe wa me zai faru? ( A Faransa a ranar 2 ga watan Oktoban 2017 an kona Musulmai 5 da suka hada da Turkawa 3”. Ko kuma a ce a kasarku a dinga kai hare-hare kowacce shekara kan Majami’u da wuraren ibadar Yahudawa? ( A Jamus a shekarar 2015 an kai wa Masallatan Juma’a hare-hare sau 24).

Babu wata kasa da za ta yi fatan samun haka a tattare da ita. Yin wannan tambayar ma na bata wa mutum rai. Amma idan irin wadannan abubuwa suka afku a kasarku ko kuma da a ce za su faru, to za a sanar da duniya irin barazanar tsaro da rashin zaman lafiya da kasar ke fuskanta. Da sai an haki dukkan tunanin dan adam da kwakwalwarsa. Ku ma da kun kai matsayin da ba za ku iya daga kawunanku ba saboda kunya. Amma kar ku damu, wadannan abubuwa ba a kasashenku suke afkuwa, a kasashen Turai suke afkuwa. Sakamakon haka ku ba ku ankara ba, haka ma duniya ba ta ankara ba.

Turai da ke kagar darajoji

Nan da wani dan lokaci ba haka Turai ta ke ba. Musamman a lokacin yakin duniya na 2, Turai ta zama mai hadin kai, kwarewa, da taimakekekniya. Wadannan halaye masu kyau ne suka haifar da Tarayyar Turai. Tarayyar Turai ta yi kokarin assasa kare hakkin dan adam, tabbatar da doka da oda, hadin kai da taimakon juna, magance matsalar nuna wariyar da kyamar Yahudawa, dabbaka demokradiyya, ‘yancin habaka tatttalin arziki, tare da sauran sassa masu muhimmanci. Amma a yau ana tafiya ana tafiya wadannan dabi’u masu kyau suna karewa, za a wayi gari Turai ta rasa dukkansu. A wani aikin George Friedman mai suna “Rikicin Turai” A tsakanin shekarun 1945 da 1991 nasarar da Turai ta samu ba wai ta Turan ba ce, ko da Amurka da Rasha sun ce su suka samar da zaman lafiya a Turai to ni ban yarda da hakan ba. Ba za a yi musun cewa, Tura, ta dau darussa daga munan halayen da ta tsinci kanta a ciki, tare da gyara halayyarta.

Turai Kullalliya, Wadda ta mika wuya ga tsoro tare da kirkirar barazana

A yau a matakin da muke babu irin Turai da muka zayyana a sama. Ranaku na wuce wa, muna ganin yadda Turai ta zama dandalin nuna kyama ga ‘yan gudun hijira. Jam’iyyun Nazi da na Fashizanci na kara samun yawan kuri’u. Jam’iyyun masu nuna wariyar launin fata na samun nasarar hawa mulki. Shugabanni masu tunani mai kyau na ragu wa. Shugabannin masu hangen nesa da tsari mai kyau na kare wa. A yanzu hare-hare kan wuraren ibada ba ya jan hankalin kafafan yada labarai don bayar da shi a matsayin labari. Kuri’ar jin ra’ayin jama’a na nuna yadda ake kara watsi da ‘yan gudun hijira.

Jam’iyyun siyasa na samun nasara ba ta hanyar alkawarin aiyuka nagari ba, sai dai don yin alkawarin za su cusgunawa ‘yan gudun hijira. Misali shi ne Ostiriya. Jam’iyyar da ta nuna ba ta son ‘yan gudun hijira ta hau kan mulki. Idan aka duba yadda Ositiriya ke yin barazana wadda kasa ce da ba ta dauki kaso 1 na yawan ‘yan gudun hijirar da Turkiyya ta dauka ba, za a ga yadda Turai ta mika kanta ga tsantsar tsoro. (Dubu 35 ne kaso 1 cikin 100 na ‘yan gudun hijira miliyan 3.5 da Turkiyya ta dauka).

Daga lokaci zuwa lokaci kasashe na shiga irin wannan hali. A irin wannan yanayi, hukumomin kasashe da shugabbin masu tsari na samar da manufofi ingantattu don magance matsalolin rikici da fita daga cikinsa.

Amma idan aka kalli irin martanin da suke mayarwa ga ‘yan gudun hijira, Musulmai da Turkawa za a iya cewa, Turai na fama da matsalar tabun hankali. An kusa a samu Turai da ta rasa tunaninta mai kyau da kuma tsaronta na kanta. Kamar dai a ce darajar da aka samu a bangaren ilimi ta ragu sosai.

Bai kamata a dora matsalolin Turai kan ‘yan gudun hijira ba

Wannan abu tun asali matsalar Turai ce. ‘Yan gudun hijira, Musulmai da Turkawa na rayuwa tun zamani mai tsawo a Turai. Wannan adadi ba wai ya dadu ba ne a yanzu. ‘yan gudun hijira ba su sauya halayensu da al’adun rayuwarsu ba. A lokacin da Turai ta samar da manufofin hadin kai na bai daya su ma wadannan mutane sun rungumi hakan. , amma a yau ana amfani da mummunan harshe da kalamai marasa kyau wajen muzanta su, kuma idan ana haka to za a ga cewa, matsalar ta samo ne daga Turai.

Tushen wannan rikici, za a iya cewa, ya faro ne sakamakon karayar tattalin arziki, samun kudi da ba sa isa ta yadda za a binduniya yadda ta ci gaba, tare da yadda a Turai babu al’umu da yawa inda ake kin karbar baki.

Kafin yakin duniya na 2, Turai ta shiga rikici irin wannan. Turai ta kasa ganin laifinta sai ta ke ganin na Yahudawa. Da tafiya ta yi tafiya sai Turai suka dora alhakin dukkan matsalolinsu kan yaduwa tare da fara kuntata musu. Daga baya bayan an afka yakin duniya na 2 da bayansa sai Turai ta gano matsalolinta ba Yahudawa ne suka janyo su ba. Amma kuma sai da duniya ta sha wahala game da mummnan halin Turai.

Yau ci gaba da makomar Turai ana dora ta kan ‘yan gudun hijira. Ana aiwatar da tsauraran dokoki kan Musulmai da ‘yan gudun hijira. Ana rufe idanuwa game da hare-haren da ake kai wa matsugunansu da wuraren idaba da sana’o’insu. Akwai bukatar masu ikirarin wayewa da ilimi na Turai su sake karanta tarihinsu don kar su fada kuskure da zai halakar da su.

Shin Turai za ta iya fita daga wannan rikici? Domin haka da farko dole ne Turai ta fahimci cewa, matsalolin na samu wa ne daga gare ta ba wai daga Turkawa, Musulmai ko ‘yan gudun hijira ba. Ba na sa ran turai za ta iya fita daga matsalolinta. Amma wannan batu za a iya yin sa a wani sabon rubutu.

Mun kawo muku nazari kan sharhin Farfesa Kudret Bülbül, Shugaban Tsangayar Nazarin Kimiyyar Siyasa Ta Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara.Labarai masu alaka