Rana irin ta yau 25.02.2020

Muhimman abubuwanda suka faru a rana irin wannan.

1364748
Rana irin ta yau 25.02.2020

A ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 1986 mulkin kama karya na Ferdinand Marcos na shekaru 20 ya ƙare a Filifin. Marcos, wanda ya ya yi suna sakamakon mulkin kama karya da cin hanci da rashawa da ya kafa a kasar, ya tsere daga kasarsa ya sauka a Hawaii bayan shugaban 'yan adawa Corazon Aquino ya lashe zaben tare da goyon bayan Amurka. Bayanai daga baya sun nuna cewa dangin Marcos sun lalata tattalin arzikin kasar na biliyoyin daloli.

A ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 1994 kisan gillar "Masallacin Ibrahim" ya faru a yankin Yammacin Gabar Kogin Falasdinu a lokacinda wani Bayahude ya bude wuta kan Falasdinawa. Falasdinawa 29 ne suka mutu wasu 125 kuma suka jikkata. Wasu Falasdinawa 26 kuma suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ta biyo bayan lamarin.

A ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2000 shahararren mawakin duniya, Carlos Santana ya lashe lambobin yabo 8 na Grammy. Santana ya kamo Michael Jackson wajen kafa tarihi da wakarsa mai suna "Thriller".Labarai masu alaka