Rana Irin ta Yau 13.06.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a irin wannan rana.

Rana Irin ta Yau 13.06.2019

A ranar 13 ga watan Yuni shekarar alif dari biyar da hamsin aka kafa tubalin babban Masallacin Suleymaniye dake birnin Istanbul.

A ranar 13 ga watan Yuni shekarar alif dari takwas da casa’in da daya aka bude gidan tarihin binciken albarkatun kasa a Istanbul. Gidan tarihin na daya da cikin manyan gidajen tarihin duniya inda ya ke dauke da kayan tarihi sama da miliyan daya.

A ranar 13 ga watan Yuni shekarar alif dari tara da ashirin da takwas aka yi jarjejeniya tsakanin Daular Usmaniyya da sabuwar gwamnatin Jamhuriyar Turkiyya.

A ranar 13 ga watan Yuni shekarar alif dari tara da tamanin da uku na’ura mai suna “Pioneer 10” ta ziyarci duniyar sararin sama inda ta kasance na’urar farko da ta wuce duniyar rana.

A ranar 13 ga watan Yuni shekarar alif dari tara da tamanin da bakwai shahararren marubuci dan Turkiyya Huseyin Cemil Meriç ya rasu.Labarai masu alaka