Rana Irin ta Yau 19.05.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a wannan rana.

Rana Irin ta Yau 19.05.2019

A ranar 19 ga watan Mayun 1881 ne aka haifi mutumin da ya kafa Jamhuriya Turkiyya Mustafa Kemal Ataturk. A ranar da Ataturk ya fita zuwa Samsun ta zo daidai da ranar haihuwarsa.

A ranar 19 ga watan Mayun 1910 ne tauraruwa mai wutsiya ta Halley ta kusanci duniya. A shekarar 1986 ne tauraruwa mai wıtsiya ta Halley ta shiga yankin rana. Lissafin da aka yi ya bayyana cewar a shekarar 2061 za a sake ganin ta.

A ranar 19 ga watan Mayun 1919 ne Mustafa Kemal Ataturk ya shiga jirgin ruwa tare da tafiya Samsun. An amince da ranar ce ranar da aka fara yak,n fatattakar kasashen yamma da suka mamaye Turkiyya. Daha daga cikin ranaku masu muhimmanci da tarihi ce a Turkiyya. Haka zalika, tun daga shekarar 1938 aka bukin wannan rana a hukumance a Turkiyya. Ataturk ya ba wa matasan Turkiyya tukwicin wannan rana. Amma kuma sau daya Ataturk ya yi bukin wannan rana ta 19 ga Mayu da ta dace da ranar haihuwarsa.

A ranar 19 ga watan Mayun 1935 ne wanda ya shirya boren Larabawa da aka fi sani da “Balarabe Lawrence”, masanin zamantakewa da tarihi na kasar Ingila, soja, dan leken asiri kuma marubuci Thomas Edward Lawrence ya mutu a hatsarin babur.

A ranar 19 ga watan Mayun 1981 ne aka sake fasalin gidan da aka haifi Ataturk a Tholenniski dake Girka tare da fara ziyartar sa.


Tag: Tarihi

Labarai masu alaka